Lokaci NE

Lokaci NE Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Lokaci NE, Pharmacy / Drugstore, Keffi.

06/06/2025
05/11/2022

Ya Ubangiji Ka Taimakeni Akan Ambatonka, Da Godemaka, Da Kyautata Ibadarka.🤲

An Kar6o Daga Abu-Hurairah R.A Yace :"Wani Mutum Ya Zo Wajan Ma'aiki S.A.W Sai Yace :" Ya Ma'aikin Allah, Na Hadu Da Wata Kunama Wadda Ta Harbeni A Jiya, Sai Ma'aiki S.A.W Yace Masa :"Ina Ma Za Ka Ringa Fadin Wannan Idan Ka Yammata : A'UZU BI KALIMATILLAHITTAAMMAAT MIN SHARRI MA KHALAQA, da Baza Ta Cutar Da Kai Ba."

05/11/2022

ƳAN'UWANA SAMARI !!!

IDAN KUN TASHI YIN AURE YA KAMATA KU TUNA CEWA MATA SUN KASU ZUWA RUKUNI HUƊU NE:

1- Akwai macen da tana da SIFFA mai kyau, amma ba ta da ƊABI'AH mai kyau, kuma ba ta da addini (ma'ana ba ta da riƙo da addini).

2- Akwai macen da tana da SIFFA mai kyau, sannan tana da ƊABI'AH mai kyau, kuma tana da addini.

3- Akwai macen da ba ta da SIFFA mai kyau, amma tana da ƊABI'AH mai kyau, sannan tana da addini.

4- Akwai macen da ba ta da SIFFA mai kyau, kuma ba ta da ƊABI'AH mai kyau, kuma ba ta da addini.

ABIN LURA...
Duk wanda ka ga ya yi aure, to, dole ɗaya daga cikin mata guda huɗun nan, ya aura, ko shakka babu a kan haka.

Mu roƙi Allah ya sa mu dace da (auren rukuni na biyu da rukuni na uku).
Mu roƙi Allah ya kange mu ya kuma kare mu daga (auren rukuni na ɗaya da rukuni na huɗu).

Allahumma Ameen. Yaa Allah !

NASIHA CE...!!!

(Hafizahullah)

05/11/2022

Aduar" datakemin dadi' take matuqar faranta raina itache...ALLAH YABARMU DA ANNABI
[S_A_W]🤍

05/11/2022

Manzon Allah (SAAW) yace: Murmushi Sadaqa ne.
(Tirmizhiy:1956).

Allah Ya sa mu wanye lafiya.

05/11/2022

GA WATA ADDU'A !

"Allahumma ya Farijal hammi, wa ya kashifal gammi, farrij hammiy, wa yassir amriy, warham da'afiy, waqillata hilatiy, warzuqni min haithu la ahtasib ya rabbal alameen

Manzon Allah (sawa) ya ce: Duk wanda ya labarta wa mutane saba'in wannan addu'ar, to Allah zai yi masa budi kan damuwarsa, ya saukake masa al'amarinsa, ya yi rahama ga rauninsa.

Manzon Allah ya yi gaskiya.

(Hafizahullah)

05/11/2022

Ya Allah fulfill my dreams.
Ya Allah give me success.
Ya Allah give me a bright future.
Ya Allah bless my parents.

05/11/2022

*SAMUN GAFARAR ZUNUBAI NA KWANA GOMA A RANAR JUMA'A*
-
Daga Salmanal Farisy ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻨْﻪُ yace Manzon Allah SAW yace;
*(Babu wani mutum da zaiyi wanka ranar juma'a kuma ya tsarkaka gwargwadon iko na tsarkinsa,kuma ya shafa mai daga mansa,kuma ya sanya turare,sannan ya fita zuwa masallaci, bai qetara tsakanin mutum biyu ba,sannan ya sallaci abinda aka wajabta masa,sannan yayi shiru a lokacin da Liman yake Huduba,face an gafarta masa tsakanin wannan juma'ar zuwa wata juma'ar)*
@ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ - ﺭﻗﻢ : ‏( 883 ).
A wata riwar acikin Saheehu Musulim;
*(Da karin kwana ukku)*
@ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ
ﺍﺑﻦ ﺣﺠﺮ ﺭَﺣِﻤَﻪُ ﺍﻟﻠﻪُ ﺗَﻌَﺎﻟَﻰ :-
Yana cewa;
"Kankare zunubai daga juma'a zuwa wata juma'ar baya samuwa sai ya ciki Sharuddan da aka ambata acikin hadisi,sharuddan sune kamar haka;
*Yin wankan Juma'a*
*Yin tsafta da gyaran jiki da tufafi*
*Sanya turare mai dadin kamshi da shafa mai*
*Sanya tufafi mai kyau*
*Tafiya masallaci cikin nutsuwa*
*Kada ka qetara tsakanin mutum biyu*
*Kamewa daga chutar da wani*
*Kuma kayi nafilar gaisuwar masallaci*
*kuma kayi shiru ka saurari huduba*
*Kuma ka baryin Lagwu lokacin huduba*
*Ka fuskanci Liman lokacin da yake Huduba*
@ ﻓﺘﺢ ﺍﻟﺒﺎﺭﻱ : ‏( 372/2 )
Allah ne mafi sani

05/11/2022

NASIHA TARA (9) GA WANDA YAKE CIKIN DAMUWA/JARABAWA

★ Ka tsaya ka binkica kanka ka duba tsakanin da Allah, da'ar ka ga Allah, ya ya take? Ka duba kaga shin baka aikata wasu ababen da Allah ko baya so? Idan ka san akwai matsala ka gyara.

★ Sannan alaqar ka ga iyaye ka duba kaga kana kyautata musu yanda ya kamata?sannan babu wani mutum da ka ke zalunta??

★ Idan wani abune kake tsoron faruwan sa ko yake baka tsoro Karka manta da fadin (Hasbunallahu wani'imal wakeel) "ita Annabi Ibrahim ya fad'a lokacin da aka jefashi wuta, sai wutar ta koma Sanyi mai aminci"

★ Manzon Allah ﷺ ya ce: idan Allah ya yi nufin bawan sa da alkhairi se ya jarabce shi da musiba".
To, kada ka damu, ta yiwu wata hanya ce da Allah yake so ya daukaka darajanka, ko ka gane wasu kusakuran naka ka kuma kara kusanci gareshi Allah (S W T)

★ Kada ka nemi biyan buk'atarka gurin wani mutum, kada kuma ka rika fadan yasassun maganganu akan damuwanka, ka kyautata ma Allah zato ka kame, sannan ka kame gabban ka daga Sabon Allah

★ Maida lamari ga Allah da neman taimakon sa, ka dauka, cewa duk wata damuwarka shi ne zai maka magani, dole dama rayuwa akwai jarabawa, bazaka taba jin yadda kake so ba ko yaushe, kuma duk lokacin da tsanani ya yi yawa akwai sauki yana tafe.

★ Yawan Sadaka da abinda da Allah ya h**e maka mai kyau, kayi tawassili Allah ya yaye duk wata damuwa.da yawan Sallan dare (daya bisa uku na karshe) lokaci ne na Amsa addu'a

★ Yawan zikiri ambaton Allah, da s**a tabbata a sunnah (duba Hisnul Muslim).
Sannan koda kana aiki ne, bakin ka ya yawaita zikiri, da Salatin Annabi da Istigfari, da addu'ar (La'ila ha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin)..

★ Idan sauki ya zo, (lokacin da kake cikin jin dadi) kada kuma ka manta da Allah, da yawan ci gaba da Addu'a da kuma godiya gare shi a ko wani hali da kiyaye dokokin sa.

Ya Ubangijin mu! Duk wani Wanda yake cikin kunci da jarabawa ta rayuwa Allah ka bashi ikon cinyewa ka kawo masa sauki da mafita (Amin)

Sheikh Albani

Al Qur'anil Kareem Yana da surori 114Ayoyi 6666 Kalmomi 77437Harufa 33215Wasula 314183Digo 197934Hizuf 60Juzu'i 30Rubu'i...
05/11/2022

Al Qur'anil Kareem
Yana da surori 114
Ayoyi 6666
Kalmomi 77437
Harufa 33215
Wasula 314183
Digo 197934
Hizuf 60
Juzu'i 30
Rubu'i 240
Ushiri 480
an saukar da surori 85 a Makkah
Ansaukar da surori 29 a madinah
Surorin da s**a fara da alhdllh 5
Surorin da s**a fara da tasbishi 6
Surorin da s**a fara da harufa 19
Guraran da sujjada a alqur'ani 15

Address

Keffi

Telephone

+2348139709783

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lokaci NE posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share