05/03/2025
Idan kana so ka kiyaye mutuncinka da kimarka, ka yi mu’amala mai kyau da mutane, ka girmama su, ka mutunta su, kuma ka tabbatar da cewa halayenka, dabi’unka, da tarbiyyarka sun dace da mu’amalarka a aikace.
Akwai wasu mutane, musamman mata, da suke tunanin cewa idan mutum ba mijinsu ba ne, to babu buƙatar su girmama shi ko yi masa biyayya. Suna ganin kamar ana ba su umarni ne, wanda hakan yana nuna cewa ba sa son a gaya musu gaskiya don su gyara halayensu. Sai dai maganar gaskiya ita ce, biyayya ga miji wajibin aure ne, amma idan mace tana da irin wannan tunanin na kin karɓar gyara da gaskiya, to ko da mijinta ne, ba lallai ba ne ta yi masa biyayya yadda ya kamata. Domin tunanin da ke hana mutum yarda da gyara yana da alaka da girman kai da rashin son gaskiya.
Addininmu na Musulunci yana koyar da kyautata mu’amala da mutane, girmama manya, da yin adalci a cikin dukkan hulɗa da mutane.
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ba wanda zai girmama wani domin yana da matsayi sai Allah zai ɗaga matsayinsa.”
(Tirmidhi)
Haka nan, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ba ya cikinmu wanda ba ya girmama manya, bai tausaya wa ƙanana, bai kuma girmama malamai ba.”
(Ahmad)
Akwai bambanci tsakanin biyayya ga miji da kuma girmama mutane da s**a girme mu a shekaru ko masu gaya mana gaskiya. Don haka, dole ne mu girmama su idan muna son gaya mana gaskiya da kuma yi mana gyara a inda tunaninmu bai kai ba. Kyakkyawar mu’amala da girmamawa alama ce ta tarbiyya mai kyau, kuma yana daga cikin kyawawan halayen da Musulunci ya koyar.
elhussain Graphic da'awah ✍️