31/07/2025
SANARWAR DAURIN AURE DA WA'AZIN WALIMA
A madadin Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah) muna farin cikin gayyatar yan'uwa da abokan arziki zuwa wajen daurin aure da wa'azin walimar auren 'ya'yan shi
Salwa Yakubu Musa da Ummu Sulaim Mujtaba Yakubu
Daurin Aure:
Rana: Juma'a 01 August, 2025
Lokaci: Bayan Sallar Juma'a
Wuri: Masallacin Juma'a na G.R.A Katsina
Wa'azin Walima da aka shirya za'a gabatar kamar haka:
WA'AZIN MAZA
RANA: 01 August, 2025
LOKACI: Bayan Sallar Isha'i
WURI: Masallacin Zaid Bin Thabit da ke Gidan Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Kofar Kaura Lay-out, Katsina
WA'AZIN MATA
RANA: 02 August, 2025
LOKACI: Karfe 9:00 na safe
WURI: Masallacin Zaid Bin Thabit da ke Gidan Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Kofar Kaura Lay-out, Katsina
Malamai Ma Su Wa'azi:
Shugaban JIBWIS na Kasa - Sheikh (Dr.) Abdullahi Bala Lau
Sakataren JIBWIS na Kasa - Sheikh (Dr.) Muhammad Kabir Haruna Gombe
Alarammoni:
Alaramma Abubakar Adam Katsina
Alaramma Ahmad Sulaiman Kano
Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
Da Sauran Manyan Malamai Da Alarammomi
Allah ya bada ikon halarta. Amin!
JIBWIS Katsina
06 Safar, 1447
31 July, 2025