
16/01/2025
Technology yayi nisa baya jin kira, shin ko kunsan cewa za'a iya yin tiyata (Surgery) ba tare da surgeon din yana tare da patient din ba.. ?
--Ma'ana likitan tiyata da yake zaune a kasar America zai iya yiwa majinyacin da yake zaune a Nigeria tiyata ta hanyar amfani da technology ba tareda sai anje America ba.
--Ana kiran wannan aikin da "Remote Surgeries" ko kuma kace "Telesurgery" ko kuma dai kace "Remote Robotic Surgery" duk abu daya ne, wannan tiyata tana faruwa ne kamar yadda kake buga video games ta amfani da pads da kake latsawa.
--Yadda abin yake, idan aka shirya majinyacin da za'a yiwa tiyata anan Nigeria, Surgical Team din zasu shirya komai za'a saka majinyancin a cikin dakin tiyata mai dauke da kayan tiyata na fasaha wato (Mechanical Arms), Nurses da Anesthesiologists zasu kasance tare da majinyancin a wurin saboda taimakawa likitan da zaiyi tiyatar da yake a cen America.
--Bayan an shirya majinyaci sai a tabbatar Robotic System din an shirya su da kyau a dakin tiyatar, system din yana dauke da camera mai matikar haske da kyau wacce likitan da zaiyi aiki a America zai kalli majinyacin tamkar yana tare dashi, haka zalika akwai na'urorin da ake kira da "Mechanical Arms" wadanda sune zasu dinga motsi ko gabatar da aikin tiyatar a duk sanda likitan yayi motsi da kafarsa ko hannunsa akan Robotics Instruments din dake a dakin da yake.
--Surgeon wato likitan da zaiyi tiyatar da yake zaune a America, zai shiga wani wuri da ake kira da "Special Console" wani daki ne mai dauke da duka na'urorin da zaiyi amfani dasu wurin yin tiyatar, (Robotics Instruments) da na'urorin da zaiyi amfani dasu wurin yin motsi da hannunsa ta yadda Mechanical Arms din robotic system dake a asibitin nigeria zasu motsa domin gabatar da aikin tiyatar.
--A takaice: Likitan dake America zaiyi tiyata ga marar lafiya a Nigeria, kamar yadda ake buga game a waya ko ake buga Video Game. Na'ura zatayi aikin tiyatar ta hanyar mimic ko bin umarnin motsi na likitan.
--Fasahar Remote Surgery Technology an fara amfani da ita a duniya tuntuni, wanda fasahar 5G technology ta taimaka sosai a wurin tabbatuwar wannan fasaha, saboda dole ana bukatar network da connections mai kyau kuma mai karfin gaske.
Shin zaka iya yarda ayi maka ko dan'uwanka Remote surgery?
Allah yasa mu dace..