25/01/2024
Yadda za ka gane alamun shanyewar ɓarin jiki da abin da ya kamata ka yi.
Shanyewar ɓarin jiki, wato "brain stroke" a turance, larura ce da ke shafar ƙwaƙwalwa a yayin da wata daga cikin hanyoyin jinin da ke kai wa ƙwaƙwalwa jini ta toshe ko ta fashe. Toshewa ko fashewar jijiyoyin jinin ƙwaƙwalwa na nufin katsewar gulukos da oksijin ga ƙwaƙwalwa, hakan kuma zai haddasa suma ko mutuwar ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa cikin 'yan mintuna.
Duk da cewa 'yan shekara 65 zuwa sama sune s**a fi haɗarin samun shanyewar ɓarin jiki, sai dai, shanyewar ɓarin jiki na iya samun kowa, a ko ina, a kowane lokaci.
Kaso ɗaya na masu shanyewar ɓarin jiki suna mutuwa ne nan take, kaso na biyu su warke sumul, kaso na uku su samu waraka a wasu sassa amma su ƙare rayuwarsu da wani ɓangare na nakasa a wasu sassan.
Alamomin shanyewar ɓarin jiki su kan zo kwatsam ne.
Alamomin sun haɗa da:
1] Karkacewar baki ko fuska. Wani lokacin tare da zubar da yawu.
2] Rauni ko shanyewar hannu ko ƙafa. Ana iya gane hakan idan aka umarci mutum ya ɗaya hannu ko ƙafa na kowane ɓangare, hagu da dama.
3] Karyewar harshe, sarƙewar magana, nauyi ko ɗaukewar magana gaba ɗaya. Ana iya gane akwai matsalar magana idan mutum ya yi yunƙurin magana ko kuma idan aka tambaye shi, "me ya faru"?
4] Da zarar an lura da waɗannan alamu, abin yi na gaba shi ne garzawa da mara lafiya zuwa asibiti kai tsaye domin samun taimakon gaggawa. Kada a ba wa mutum wani magani; na ƙwaya ko na ruwa ko kuma ruwan rubutu.
"Ƙwaƙwalwa lokaci ce, kuma lokaci ƙwaƙwalwa ne". Ma'ana: yawan lokacin da aka ɓata kafin kai mai alamun shanyewar ɓarin jiki asibiti; to yawan miliyoyin ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwar da za su suma ko su mutu kenan.
Awa ukun farko shi ne mafi kyawun lokacin da ya kamata a ce mai alamun shanyewar ɓarin jiki ya isa asibiti domin fara samun taimakon gaggawa.
Taimakon gaggawar da mutum ya samu na nuni ga kyawun makomar da zai samu yayin warkewa.
Tura wannan saƙo ga 'yan uwa, abokai da sauran al'umma domin su iya taimaka wa