21/01/2026
YADDA YIN SHIRU NA WANI LOKACI YAKE TAIMAKON KWAKWALWA 🧠✨
Yin shiru (silence) na lokaci na iya taimakawa wajen girman sabbin kwayoyin halittar (neurons) kwakwalwa abinda ake kira (neurogenesis), musamman a sashen (hippocampus), wato inda ƙwaƙwalwa take adana bayanai da koyon sabbin abubuwa.
Lokacin da muka yi shiru, kwakwalwa tana samun hutu daga hayaniya da cunkoson sauti.
Wannan na ba ta damar:
Gyara kanta:
- Adana abubuwan da muka koya
- Da kuma karfafa hanyoyin sadarwa da jiki
- Da ƙarfafa haɗin ƙwayoyin halittar kwakwalwa
A takaice, shiru na ba kwakwalwa sarari ta gyara da gina kanta, maimakon ta ci gaba da fama da amo da hayaniya.
🤔 Amma ta yaya shiru ke yin wannan aiki a zahiri?
👇 Zan bayyana muhimman dalilai a comments don mu tattauna tare.
🧠🌱 Ƙananan canje-canje kamar yin shiru na takaitaccen lokaci na iya kawo babban sauyi ga lafiyar kwakwalwa.
❓ Tambaya:
Yaushe ne karo na ƙarshe da ka ba kanka lokaci kaɗan cikin shiru?