30/09/2025
KAIMA KANA CEWA A DAURA MAKA DRIPS IDAN BAKA DA LAFIYA?
📍Mutane s**an zuwa s**e a daura musu ruwa saboda basu da lafiya. Wanda Drip kuma ba magani bane kai tsaye.
📍Akwai ruwan da idan ka sakawa mutum matsala zai bashi,MISALI Mai hypertension ka saka masa Normal saline.ko Mai Diabetes Ka saka masa Dextrose.
Ko wanne ruwa akwai dalilan saka shi
👇🏽👇🏽
DALILAN DA AKE SA WA MUTUM DRIP
1. Rashin ruwa a jiki (Dehydration) – idan mutum ya rasa ruwa saboda zazzabi, gudawa, amai, ko rashin shan ruwa.
2. Magani – a wasu lokuta magani yana fi tasiri idan aka saka ta jijiya (misali antibiotics, painkillers).
3. Abinci (nutrients) – idan mutum ba zai iya ci ko sha ta baki ba, ana iya bashi abinci ta hanyar drip (TPN – Total Parenteral Nutrition).
4. Gudanar da jini ko ruwa da gaggawa – misali a lokacin zubar jini ko accident.
NAU’O’IN RUWA (DRIP)
1. Normal Saline (0.9% NaCl) – domin kara ruwa da gishiri a jiki.
2. Dextrose solution – ruwa mai sikari domin kara kuzari.
3. Ringer’s lactate – don Kara electrolytes a jiki.
"Ka nemi shawarar likita kafin kaje a daura maka ruwa"🙏
RPHT Naseer Mouser