04/10/2024
FANNONIN LIKITANCI
A wannan bidiyon da mukayi a harshen turanci mu kawo wasu fannonin likitanci guda 10, ma'anoninsu da kuma wasu abubuwa da suke yi.
Wadannan fannonin sun haɗa da:
1. Cardiology: fannin likitanci da yake lura da zuciya da jijiyoyin jini, likitoci wannan fannin s**an lura da masu cututtuka k**ar hawan jini, ciwon zuciya, mutuwar zuciya dss, suna kuma yin amfani da ababe k**ar ECH, Echocardiogram domin tantance wace irin cutace ke damun mutum, ta haka kuma su bayar da shawarwari, magunguna da ma wasu ayyukan da s**a shafi zuciya da hanyoyin jini.
2. Nephrology: Fannin likitanci da yake lura da Ƙoda, abar da take aiki dare da rana wurin yace ƙazantar da ke cikin jini domin a fitar dashi a matsayin fitsari. Likitocin wannan fannin suna kula da cututtuka da s**a haɗa tunda daga sanyin mafitsara da ƙoda har zuciya mutuwar ƙoda. Sukan bayar da magunguna, sune kuma suke da ƙwarewa a fannin wankin ƙoda (dialysis), kuma tare da su ake yin dashen ƙoda kuma su suke kula da masu wannna lalura.
3. Dermatology: Shi kuma wannan fannin yana kura da fata da abubuwan da suke fitowa daga fata k**ar ƙumba da gashi, suna bayarda shawarwari da ma magance cututtuka da s**a haɗa ƙurarrajin fata, ƙyasfi, kansar fata dss. Ko baya ga wannan suna da ƙwarewa sosai wurin ƙawatarda fata dama duk abinda ya shafeta.
4. Orthopedics: Waɗannan likitocin fiɗa ne (surgeon) da suke lura da ƙasusuwa, gaɓoɓi da ma sauran sassan jiki da suke aiki wurin motsi k**ar tsoka, jijiyoyi dss. Su suke kula da masu kariya, targaɗe, sanyin ƙashi, sanyin gaɓoɓi, ciwon baya dss. Sune kuma ke da ƙwarewa a fannin sport medicine.
5.Otorhinolaryngology: Shi kuma wani fannin ne likitocin tiyata da suke lura abin da ya shafi kunne, hanci da maƙoshi; an fi kiran wannan fannin da ENT (Ear, Nose and Throat), likitocin ENT suna lura da cututtukan da s**a shafi waɗannan sassan 3, kuma suna da ƙwarewa a fannin cututtukan da s**a shafi wuya k**ar cututtukan maƙoƙo (thyroid disorders) da ma kansar wuya.
6. Radiology: Wannan fannin likitancine mai ban ƙaye da ake amfani hasken radiation domin gano cututtuka da kuma illolin da suke cikin jikin ɗan Adam, su kuma bayar da shawarwari akan hanyoyin magani. Su suke bayarda bayanin abubuwan da aka gani a hotuna Ultrasound scan, X-ray, MRI, CT scan dss. Haka kuma sunada ƙwarewa a wasu ayyukanda ba'a buƙatar feɗe jiki (minimal invasive surgery) da kuma interventional radiology.
7. Ophthalmology: Likitancin Idanu kenan, duk da Idanu k**ar basu da wani girma, amma fa aikinsu ba ƙarami bane, shi yasa likitoci a wannan fannin suke da ƙwarewa akan cututtukan da s**a shafi Idanu tun daga rashin gani da kyau da ake kira refractive error, harga cututtukan idanu da s**a haɗa da Glaucoma, catarat dss. Ophthalmologists Kan bayarda shawarwarin kuka da Idanu, magunguna cututtuka mabanbanta, gama suyi aiki (tiyata) a cikin ƙwayar ido.
8. Paediatrics: Likitancin yara kenan, masu kula da lafiya da jin daɗin yara tun da haihuwarsu har zuwa balaga, suke kula da duk wata cuta d take shafar yara ta jiki, matakan rayuwa na yara dama mu'amalarsu, sun ƙware a fannin bayarda shawarwari ga uwayen yara akan hanyiyin kula rayuwar yara, alluran riga-kafi dss.
9. Gynecology: Likitanci mata, ƙwararrin wannan fannin suna lura duk cututtukan da suke da alaƙa da gaɓoɓin haihuwa na mata (female reproductive system), gynecologist ne dai sukeda ƙwarewa akan lalurorin mata da s**a haɗa da na jinin al'ada, ciki, haihuwa, cututtukan k**ar su fibroid, sanyin mahaifa da mara (STI, PID), endometriosis, kansar bakin mahaifa dss.
10. Oncology: Ɗaya daga cikin fannonin likitanci masu wuyar sha'ani da suke tu'ammali da masu lalurorin ciwon daji (kansa), s**an bayarda taimako ta hanyoyi mabanbanta da s**a haɗa da Alluran chemotherapy, gashin radiotherapy da ma ayyukan hiɗa.
Ku faɗa mana wani fanni na likitanci da kuke son sanin wani abu akan su a comment section.