Jibwis Ilesha Osun State

Jibwis Ilesha Osun State JIBWIS ILESHA OSUN STATE

Kai tsaye daga wajen shirye-shiryen gyaran filin waazin jaha a garin Ibodi dake karamar hukumar Ilesha ta juhar Osun
29/11/2025

Kai tsaye daga wajen shirye-shiryen gyaran filin waazin jaha a garin Ibodi dake karamar hukumar Ilesha ta juhar Osun

INNA LILLAHI WA INNA ILLAIHIR RAJU'UNShugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Ik**atus Sunnah Na Jihar Oyo, Kuma Sh...
27/11/2025

INNA LILLAHI WA INNA ILLAIHIR RAJU'UN

Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Ik**atus Sunnah Na Jihar Oyo, Kuma Shine Shugaban JIBWIS Southwest, Alhaji Salisu Abdullahi Umar Sabo Ibadan, a Madadin Kungiyar Na Mika Sakon Ta'aziyya Ga Yan'uwa Da Iyalai Bisa Rasuwar Dattijo Kuma Babban Malami a wannan Kasa Sheikh Dahiru Usman Bauchi🥲

Wanda Allah SWT Yayi Ma Rasuwa a Daren Yau Alhamis 06 Jumada Thani, 1447 Wanda Yayi Daidai Da 27 Nuwamba, 2025

Muna Rokon Allah SWT Ya Jikanshi, Ya Gafarta Ma Shi, Ya Haska Ka Kabarin Shi, Ya Sanya Albarka a Cikin Zuriyarsa, Allah SWT Ya Sanya Aljannar Firdausi Ta Zama Makoma a Gare Shi. Amin

JIBWIS OYO
06 Jumada Thani, 1447
27 November, 2025.

WA'AZIN JAHA ! WA'AZIN JAHA !! WA'AZIN JAHA !!!IBODI NOV. 2025ومن أحسن قولا ممن دعا إلى الله وعمل صالحا وقال إنني من الم...
26/11/2025

WA'AZIN JAHA ! WA'AZIN JAHA !! WA'AZIN JAHA !!!

IBODI NOV. 2025

ومن أحسن قولا ممن دعا إلى الله وعمل صالحا وقال إنني من المسلمين.

Kungiyar JAMAATU IZALATIL BID'AH WA IQAMATIS SUNNAH Reshen jahar Osun.

A MADADAIN:

SHUGABAN JIBWIS : Alhaji Muhammad Hashim Danmaifura

SHUGABAN MAJALISAR MALAMAI: Sheikh Bashir Hussain

DIRECTOR JIBWIS OSUN FAGN: Malllam Bashir owena.

Suna gayyatar Al'ummar musulmi zuwa wajan WA'AZIN JAHA wanda zai gudana k**ar haka:

GARI: SABO IBODI ( Dake a kan babban titin Express na Ilesha-Ife-Ibada, a karamar hukumar Atakumosa West dake gundumar Ijesha Land)

LOKACI : karfe 4:00pm na yamma zuwa 12:00am na dare.

RANA: Asabar 8th- JUMADAA ULA - 1447H. daidai da 29th - NOVEMBER- 2025 .

MALAMAI MASU WA'AZI:

- Sheikh Mas'ud Ibrahim Offa.
- Sheikh Salisu Lukman Sabo Ibadan.
- Sheikh Zakariyya Abdullahi (Osogbo).
- Sheikh Muhammad Sani Bature (Osogbo).
- Mallam Sulaiman Muhammad (Owena.)
- Mallam Auwal Idris (Ilesha).
- Mallam Uzairu Muhammad Tahir (Ibodi).
- Alhaji Sani Abubakar Police (Ibodi).
- Mallam Ahmad Muhammad Yawale (Ile-ife.)

ALARAMMOMI:

- Alaramma Adam I Adam
- Alaramma Mukhtar Said (Ile-ife).
- Alaramma Adam Muhammad.
- Alaramma Ahmad Ahmad (Osogbo).
- Alaramma Abubakar Sulaiman (Ilesha).

MASU MASUAKIN BAKI:

Alhaji Sani Abubakar Police.
Mallam Uzairu Muhammad.

UBAN TARO: Alhaji Abubakar Sahabi (Sarkin Hausawan Ibodi)

A karkashin jagorancin: SHEIKH BASHIR HUSSAIN.(Shugaban Majalisar Malamai ta jahar Osun).

SANARWA : Idris M Rismawy Abu Nu'aym (Jibwis Osun P.R.O).

ALLAH YABADA IKON ZUWA LAFIYA. AMEEN YA RABB.

NISA'US SUNNAH JIBWIS ILLELA L/G SOKOTO STATE 🫡🫡🫡
18/11/2025

NISA'US SUNNAH JIBWIS ILLELA L/G
SOKOTO STATE 🫡🫡🫡

Hotuna: JIBWIS MODEL SCHOOL, OYO ta karrama Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau da Lambar yabo ta girmamawa a wata ziyara ...
28/09/2025

Hotuna: JIBWIS MODEL SCHOOL, OYO ta karrama Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau da Lambar yabo ta girmamawa a wata ziyara da Shugaban ya Kai makarantar bayan kammala taron FASON na kwana uku a Garin Ibadan.

ZIYARA:kai tsaye daga masarautar Olubadan a garin ibadan Oyo State, sak**akon ziyarar da JIBWIS NIGERIA takai wa Sarkin ...
28/09/2025

ZIYARA:
kai tsaye daga masarautar Olubadan a garin ibadan Oyo State, sak**akon ziyarar da JIBWIS NIGERIA takai wa Sarkin garin Ibadan "OLUBADAN"

Allah ya bada ladar ziyarar ya kuma maida su gida lafiya, Ameen thumma ameen

JIBWIS ILESHA OSUN STATE

Hotuna: Gagarumin taro (Conference) Wanda aka shirya a karkashin Kungiyoyin Ahlus Sunnah (FASON) wanda shugaban JIBWIS S...
27/09/2025

Hotuna: Gagarumin taro (Conference) Wanda aka shirya a karkashin Kungiyoyin Ahlus Sunnah (FASON) wanda shugaban JIBWIS Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau da tawagarsa s**a halarta a Garin Ibadan.

Jibwis Nigeria

MADADIN KWAMITIN JIBWIS SOCIAL MEDIA RESHEN JAHAR OSUN.Muna farin cikin gayyatar al'ummar Musulmi zuwa wajan shedar daur...
27/09/2025

MADADIN KWAMITIN JIBWIS SOCIAL MEDIA RESHEN JAHAR OSUN.

Muna farin cikin gayyatar al'ummar Musulmi zuwa wajan shedar daurin auren daya daga cikin yan kwamitin Zakariyya Yusuf dake garin GAREJIN OLODE , wanda za a yi shi a garin Sabo Ondo da ke jahar Ondo k**ar yadda yake a cikin katin gayyata.

Allah yabada ikon zuwa, wadanda basu samu damar zuwa ba muna buƙatar Addu'a ga ango da kuma amaryarsa.da sauran jama'ar musulmai Allah yasnaya musu Alkhairi da albarka kuma ybasu zaman lafiya

SHEIKH ABDULLAHI BALA LAU ZAI JAGORANCI TARON KUNGIYOYIN AHLUS SUNNAH NA NAJERIYA A YANKIN KUDU MASO YAMMADaga Sani Umar...
25/09/2025

SHEIKH ABDULLAHI BALA LAU ZAI JAGORANCI TARON KUNGIYOYIN AHLUS SUNNAH NA NAJERIYA A YANKIN KUDU MASO YAMMA

Daga Sani Umar Maiyara

Shugaban JIBWIS na kudu maso Yamma (Southwest Zone) a tarayyar Najeriya Alh Salisu Abdullahi Umar na Farin cikin gayyatar Al’umar Musulmin Nigeria Musamman mazauna Kudancin kasar gagarumin taro (Conference) Wanda aka shirya a karkashin Kungiyoyin Ahlus Sunnah (FASON) a Garin Ibadan.

Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau Zai Jagoranci taron Kuma daya daga cikin masu gabatar da Kasidu a taron tareda wasu mashahuran Malamai daga Yankin na Yarbawa.

MALAMAI MASU GABATARDA TAKARDU

*Sheikh (Dr.) Abdullahi Bala Lau
*Shk. (Dr.) Abdul Mojeed Imran Eleha
*Prof. Ishaq Lakin Akintola
*Dr. Idris Sekoni
*Dr. Musharaf Aderogba
*Shk. Isa Akindele Solahudeen
*Prof. AbfulGaniy Raji
*Shk. Masud Ibrahim (Offa)
*Shk. Dr Dhikrullah Shafli
*Dr. Tawadhul Adeoye
*Shk. Mukadam Hussein
*Shk. AbdulFatah Thani
*Dr. Abdul Haadi Thiamiyy

MAI MASAUKIN BAKI:
Sheikh Tajudeen Abdul Kareem Al Adabiyy (Baba Lagbeni)

Allah ya bada ikon halarta, Amin

Jibwis Nigeria

First Aid Group of Jibwis Nigeria   Lalle Aikin Agaji ba na mai girman kai bane, Hon. Zannah Bunbudu É—an Majalisa ne na ...
19/09/2025

First Aid Group of Jibwis Nigeria

Lalle Aikin Agaji ba na mai girman kai bane, Hon. Zannah Bunbudu É—an Majalisa ne na tarayya ( Representative) daga jihar Zamfara jihar Muslunci.

Hon. Zannah ɗan Agaji ne kuma mai muƙami na ƙasa ƙarƙashin majalisar Agajin ƙungiyar Izalah
Wato National Senior Special Assistance to the National Director General
Engr. Mustapha Imam Sitti

Hon. A tsaye yake har yanzu wajen bada gudunmawa wa Addinin Musulunci a dukkan lokacin da hakan ya taso.

Hon. An bashi Duty kuma ya tsaya akan Dutin da aka bashi ba tare da girma kai ba, to kai É—an Agaji wanda idan an baka Duty kake nokewa ka dai ga yadda manya suke aikin a tsaye babu k**a hannun yaro.

Allah ya ƙarawa wannan Aiki namu Albarka, Allah ya ƙara Ɗaukaka wannan Aiki namu na Agaji, wallahi wannan uniform ɗin ana ganin kimar sa a ko'ina a faɗin duniya.

Agaji babu k**a hannun yaro

First Aid Group of Jibwis Nigeria.

First Aid Group of JIBWIS,National Directorate  INNAA LILLAAHI WA INNAA ILAAIHI RAJI'UN !!!Daraktan Agaji na Kasa JIBWIS...
17/09/2025

First Aid Group of JIBWIS,
National Directorate
INNAA LILLAAHI WA INNAA ILAAIHI RAJI'UN !!!

Daraktan Agaji na Kasa JIBWIS Nig. Engr. Mustapha Imam Sitti na sanar da 'yan Agaji tare da sauran Al'umar Musulmi rasuwar ALH. ABDULLAHI I. N. BAKORI (Katsina State, Director.) wadda ya rasu yau Talata 16/9/2025 .
Za ayi jana'izarsa gobe Laraba 17/9/2025 da 11:00 A.m (na safe) a Garin BAKORI, Jihar Katsina.

Ana bukatar addu'o'inku 'yan uwa masu albarka.
Allah (SWT) yaji Kansa ya kuma saka masa.
Allah ya gafarta masa.
(Dep. Nat. Pub. Sec.)

Address

Ereguru Street, Ilesha
Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Ilesha Osun State posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram