23/02/2025
DAN ALLAH TSAYA KA KARANTA.
Daga: Dr. Abdurrahman Dambazau
Ranar Litinin 17/2/25, Mun shiga ɗakin da ake kwantar da marasa lafiya na ɓangaren tiyata (Surgery). tare da likitan da ke hannun dama na a wannan hoto.
Wannan likita sunan sa doctor bashir Aliyu, likita ne na tiyata a babban asibitin koyarwa da ke azare(FMC AZARE), asibitin da nake koyan aiki a matsayi na, na ɗan ƙaramin likita.
Bayan mun shiga sai ya ga wata yarinya ƙarama wacce ita ma tana buƙatar tiyata(surgery) amma kuma bata cikin list na wannan rana. Abun da muke nufi da list shine: duk ranar da za ai tiyata ana ware iya mutanen da za ayi ma a wannan rana.
Ma'ana yarinyan bata cikin waɗan aka tsara zai ma tiyata a wannan rana.
Bayan ya ganta sai ya kira ni, yace dambazau ka shirya mun yarinyar nan anjima bayan na gama tiyato ci biyu da nake dasu zaka tayani na mata. sai nace mai to, Naje nai duk shirye shiryen da ake ma mara lafiya idan za amai tiyata.
9:30 na safe dr bashir ya shiga ɗakin tiyata ya fara ayyukan sa, wajen karfe 12 na rana, ya gama tiyatan farko, zuwa 3 na rana, ya gama tiyata na biyu, wanda alokaci ko a ido ka kalle shi kasan ya gaji, amma duk da haka wajen uku da rabi yace dambazau a ɗakko yarinyar nan, a kawo ta ɗakin tiyata. Sai naje Nama nurses magana aka kawo ta.
Akwai kayayyaki da akace iyayen yarinyar su siyo, za ai amfani da su a lokacin da ake tiyatan, wanda sakamakon yana yi na rayuwa basu da halin da zasu iya siyo wa. dr bashir ya ciro kuɗi a aljihun shi yace dambazau gashi ka basu suje su siyo, na basu s**a je s**a siyo, bayan sun siyo muka fara tiyata, wanda bamu gama ba sai wajen shida na yamma.
Tambayar anan shine;
Shin da gaske ne likitoci basu da kirki??
Ko wani ɓangare na rayuwa ba ka rasa ɓatagari ko mara sa kirki, amma musani ɓangaren likitanci ɓata garin ƙalilan ne in ka haɗa su da sauran ɓangaren rayuwa irin su shari'a, ƴan sanda, banki, jarida da sauran su.
A kwana kin nan akwai matar da tai iƙirarin likitoci a asibitin malam aminu kano sun cire mata mahaifa, wanda duk wanda ya shiga ɓangaren comment zai ga yadda mutane ke faɗar abubuwa mara sa daɗi akan likitoci. muƙaddara labarin gaskiya ne, atunani na hakan bazai sa likito ci su zama ɓata gari ko masa kirki ba.
Akwai likitoci da yawa wanda suke sadaukar da lokacin su, dukiyar su, da kuma jindaɗin su, don suga sun taimaka ma mara lafiyan su(Patient). hasali ma har da waɗan da s**a rasa rayuwar akan hanyar taimakon mara lafiya irin su Dr muhd musa habeeb, (consultant anaesthesia AKTH) Allah ya jiƙan sa da gafara.
Aikin likitanci aiki ne da ke tattare abubuwa da dama wanda idan mutum ba acikin sa yake ba bazai taɓa gane su ba.
Dan Allah adunga ma likitoci uzuru.
Nagode
Dr Abdurrahman Dambazau
Daga shafin Dr. Dambazau TV