
11/05/2025
Lokacin da Annabi Sulaiman (A.S) ya nemi shawara daga jemage. sai wasu halittu huɗu daga halittun Allah s**a zo wajensa suna da buƙata da koke-koke:
Na farko: Rana ta ce:
“Ya Annabin Allah, ka roƙi Allah Ya zaunar da ni a wuri guda kamar yadda Ya zaunar da sauran halittu, kada in ci gaba da yawo daga gabas zuwa yamma kullum."
Na biyu: Macijiya ta ce:
“Ya Sulaiman, ka roƙi Allah Ya ba ni hannu da ƙafafu kamar sauran dabbobi. Na gaji da yawo da ciki na kullum."
Na uku: Iska ta ce:
“Ya Annabin Allah, har yaushe zan ci gaba da yawo kamar wacce ta rikice? Ka roƙi Allah Ya zaunar da ni a wuri guda, in samu hutawa."
Na huɗu: Ruwa ya ce:
“Ya Annabin Allah, har yaushe zan ci gaba da yawo a kasa da sararin sama, babu wurin zama, babu natsuwa? Ka roƙi Allah Ya zaunar da ni a wuri, duk wanda ke buƙata sai ya zo ya neme ni."
Allah ya koya wa annabi Sulaiman harsunan tsuntsaye, sai ya tara su domin shawara. Daga cikinsu akwai jemagu (ƙudan dare), wanda shi ne mafi rauni a cikinsu. Sulaiman ya so ya nuna musu cewa ko rauni yana da daraja, sai ya ba jemagu labarin waɗancan koke-koke na rana, macijiya, iska da ruwa...
Sai ya tambaye shi: “Ya jemage, me kake gani game da wannan? Me za ka ce?”
Jemage ya girgiza fuka-fukansa, ya matso kusa cikin ladabi da tawali’u, sannan ya ce:
"Ya Annabin Allah, suna neman zama da hutu, amma a cikin motsinsu akwai hikima da baiwa da ba kowa ke ganinta ba sai wanda Allah ya ba basira.
Idan rana ta tsaya, duniya za ta yi duhu, amfanin gona da dabbobi za su hallaka, kuma dare da rana za su bace.
Idan macijiya ta samu ƙafafu, za ta rasa tsoronta, mutane za su fi jin tsoronta, kuma sirrinta da Allah ya boye zai ɓace.
Idan iska ta tsaya, iska za ta lalace, jiragen ruwa za su tsaya, ruwa ba zai sauka ba, noma zai lalace.
Idan ruwa ya tsaya, zai lalace, ya ƙazantu, babu mai amfana da shi, ya zauna a wasu wurare, wasu kuma su rasa shi.”
Sai jemagu ya ce da wata murya mai nutsuwa da hikima:
"Ya Annabin Allah, komai na motsi ne, kuma hutunsu na cikin motsinsu ne. Idan suna neman wurin zama, to su sani cewa matsayinsu na gaskiya yana inda Allah Ya dora su. Kuma Allah bai halicci komai a banza ba. Kowanne da hikima da albarka a cikin abin da yake kuka da shi.”
Sai Annabi Sulaiman ya yi murmushi, ya kalli tsuntsaye da dabbobin, ya ce:
"Gaskiya jemagy ya faɗa. Duk da raunin sa, shi ne mafi fahimta. Kuma duk da ƙarancinsa, shi ne mafi hankali. Ku gode wa Allah da halin da kuke ciki, domin kowannenku akwai hikima da ni’ima a cikin halittarsa da ba kowa ke ganinta ba, sai wanda Allah Ya ba fahimta."
Sai rana ta yi shiru, macijiya ta nutsu, iska ta tsaya kuka, ruwa ya natsu, kuma kowannensu ya koma ga aikinsa da natsuwa da yardar cewa Allah ne mafi sani mafi hikima.
Idan ka gama karantawa, ka yi salati ga mafi daraja daga cikin annabawa da manzanni, Muhammad (S.A.W), bawan Allah kuma manzonsa.
Sannan inci alfarmar sa kayi following dina