16/03/2023
ILIMIN LIKITANCI DANA ADDINI
Ilimidai shine tushen habakar bani'adam a rayuwarsa ta duniya data barzak, babu shakka addu'ar nan ta rabbi zidni ilman ba tana tsayawane a duniya kadaiba, harda kiyama bani'adam yana buqatar cigaban da samun ilimi daga Allah ( S W T), k**ar yadda yafaru a manzilar saukowa duniya wacce ake kira QAUSUN NUZUL zuwa wannan duniya to haka yake kuma ga mai komawa wato QAUSUS SU'UD zuwaga Allah, marhaloline da dan'adam ke matiqar buqatar ilimi daga Allah zuwaga bawa, a takaicedai Dan'adam mai buqatuwane ga ilimi a kowacce marhala ta rayuwa.
Sai dai abin tambaya shine wanne ilimine yake kan gaba wajen Dan'adm? Wannan itace tambayarda zamu amsa a cikin wannan rubutun, da wannan amsace zamugane abinda yadace muhimmatu wajen nemansa a wannan zamani domin samun ingantacciyar rayuwa a duniya da makoma mai nishadi nan ga Allah madaukakin sarki.
ILIMI KASHI BIYUNE
Yazo a wata riwayar sayyidina Ali (A) cewa ilimi kala biyune madaukaka, ilimin jikkuna da ilimin addini, wannan riwayar tana baiyana cewa samun lafiyar dan'adam shine gaba ga komi a rayuwarsa ta duniya, domin idan ba lafiya komi tsayawa yakeyi, tinda hakane, wannan riwayar tana gaya mana muhimmancin neman ilimin lafiyar jiki a rayuwar bil'adam, yazama wajibi wasu daga jama'a sudauki lokaci domin karanta fannonin ilimin lafiya domin sanya Al'umma kan shawarwari da magunguna masu dacewa da larurar da ke damunsu.
A daidaikummu yak**ata muyi dukkan mai yiwuwa domin sanin lafiyar jikinmu ako wanne hali, ba dalilin kasancewa cikin lafiya bane idan bamuji rashin lafiya ajikinmuba, lallai yak**ata muje gun likita donin samun shawarwari da magunguna, likitoci abokammune a kowanne hali, kenan yak**ata k**ar yadda muke da lauyoyi suma likitoci mu kusancesu domin sanin halinda lafiyarmu take ciki, wannan yanada maiqar muhimmanci.
Daga nan sai mu himmatu wajen neman ilimin addini don keutata alaqarmu da mahalicci, daganan sauran fannonin ilimi subiyo.
Ardo galadima
08032546244