28/06/2014
SAKON RAMADAN DAGA: ASH-SHEIKH IMAM
ABDULLAHI BALA LAU (Shugaban Kungiyar
na Kasa).
Da sunan Allah mai Rahama mai Jinqai. Dukkan
godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, muna
gode masa, kuma muna neman taimakon Sa, da
gafarar sa. Muna neman tsarin sa daga dukkan
sharri.
Ina so inyi amfani da wannan lokaci mai albarka
domin in gabatar da gaisuwa, tunatarwa da addu'a
ga dukkan mutanen wannan kasa mai albarka
(musamman musulmai), kuma a wannan wata na
Ramadan mai tarin albarka da falala.
Allah madaukakin sarki yana cewa: "Watan Ramadan
wanda a cikinsa aka saukar da Al-Qur'ani, shiriya ga
mutane, kuma bayyanannar shaida ta shiriya
da...." [Qur'an:185].
Wannan wata na Ramadan wata ne mai daraja, falala
da muhimmanchi a Musulunchi. Shine watan Al-
Qur'ani, watan azumi, watan albarka, alfarma,
gafara, falala da fa'idodi masu yawan gaske. A
takaice, shine watan da yafi ko wane wata
muhimmanchi da fa'idodi cikin watanni goma sha
biyu na shekara.
A cikin wannan wata ne Allah ya saukar da Al-
Qur'ani, kuma a cikinsa ne daren "Lailatul Qadri"
yake fadowa, wanda ya fi watanni dubu falala.
Kuma watan Ramadan wata ne da musulmai ke zage
damtse wurin tausayi, kyautatawa, kame kai daga
barin alfahsha, haquri, sadaqa da 'yan uwantaka.
Cikin wannan wata ne ake samun dukkan alkhairi.
Wannan wata babban bako ne da duk musulmi na
kwarai ke kosawa da marhaba da zuwansa. A wurin
bayin Allah na gari kuwa, watannan dama ne na
'kara kusantar Allah. Kuma ga masu son shiriya,
wannan wata dama ne na barin alfahsha, al-kaba'ir,
da munanan ayyuka domin komawa ga Allah. Don a
wannan watan duka shai'danu an 'daure su kuma an
kulle su.
Saboda haka, ina so in tunatar da shugabanni da
wadanda ake shugabanta na wannan kasa da suyi
amfani da wannan wata mai albarka don kara
tausayi, gaskiya, amana, adalchi da tuhuman
kawunanmu kan ayyukanmu.
Sannan kuma har yanzu ina amfani da wannan dama
domin jawo hankalinmu da mu guji ta'addanchi,
ha'inchi, chin zali, rashin 'da'a, chin amana, fasadi,
alfahsha, fadace-fadace, tada hamkula, izgili, qazafi,
sharri da chin hanchi da rashawa!
Ina mai horon dukkan musulmi ba tare da la'akari da
matsayi, kudi, kabila, gari, ko jinsi ba, da mu dauki
wannan watan na Ramadan a matsayin bako da ke
zuwa sau daya a shekara. Wata ne na 'yanchi, gafara,
rahama, tuba da zage damtse wurin bautan Allah.
Ina kira a garemu da mu tuba, tuba na gaskiya ga
Allah, kuma mu inganta dangantakarmu da Allah ta
hanyar yin azumi, sallolin nafila, karatun Qur'ani,
sadaka, kyauta, 'da'a, da yawaita addu'o'i. Saboda an
bamu wannan wata ne domin mu inganta imaninmu
da kara tsoron Allah. Allah yana cewa a cikin Suratul
Bakara, aya ta 183:"Ya ku wadan da kuka yi imani,
an wajabta (sanya) muku azumi kamar yadda aka
wajabta wa wadanda s**a gabaceku domin ko zaku
samu tausayi da tsoron Allah."
daga 'karshe, a cikin wannan wata mai albarka,
kasarmu Nigeria tana bukatar addu'o'inmu managrta
daga dukkan bakunanmu. Domin Allah ya zaunar
damu lafiya, kuma ya karemu daga dukkan sharrin
masu sharri!
Ina addu'a Allah ya zaunar damu lafiya, ya yafe mana
zunubanmu, ya kyautata zamantakewarmu, kuma ya
karemu daga fitintinun da kasarmu ke ciki wadanda
s**a hada da rashin tsaro, rashin adalchi, rashin
amana, kashe rayukan da basu ji ba basu gani ba,
chin hanchi da rashawa da sauransu!
Allah ya taimake mu, ya kare mu, ya sada mu da
dukkan alkhairan wannan wata mai albarka, ya bamu
lafiya da zama lafiya.
Ameen Summa Ameen!!!
Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau
(Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'ah Wa
Iqamatis Sunnah Nigeria).
jibwisnigerian@yahoo.com