08/02/2025
ZUBEWAR CIKI TARE DA YAWAN MUTUWAR JARIRAI ACIKI
Akwai matukar ciwo asami rabo na juna biyu akarshe azamto anrasa shi. Wanda bisa kididdiga adukkan mata 4 masu ciki akalla 1 na rasa nata yayin da 3 kadai kekai labari.
Da farko akwai bambanci tsakanin 6ari wato miscarriage da kuma mutuwar yaro aciki wato stillbirth.
In ciki ya zube kasa sati 23 na goyonsa wato watanni 5 shine ake cewa 6ari. Amma duk cikin da ya zube bayan sati 23 aduniya ko sati 28 a Nigeria wannan shine mutuwar jariri wato still birth.
Abubuwa ne da sun yawaita ayanzu toh amma dangane da 6ari wato miscarriage abubuwan dake haddasa sune;
■ Rashin lafiyar cikin mahaifar mace wato kila akwai wata nakasa ta halitta a mahaifar,
■ Sai kuma yawan zirga-zirga ace ana da yaron ciki amma arika daukar mace ko ita akaran kanta ta rika tafiye-tafiye a mota ko akasa ta sama da awa 2 da rabi, ko tafiyar babur ta kimanin minti 15 zuwa 20,
■Koh yawan aikin karfi ba hutu,
■ Sai kuma raunin ko rashin kwarin bakin mahaifa wato cervix insufficiency a wadanda keda karancin sinadarin protein din dake ba cervix din kwari wato collagen adalilin gado,
■ Sai kwayoyin cuta irinsu PID da infections din nan dake descending ya shige,
■ Sai cutukan koda (kidney disease),
■ Ciwon suga da kuma
■ Ture-turen sassake-sassake ko tsarki da abubuwa iri-iri a farji da mata s**a cusa kansu ciki ayanzu.... wanda wani ruwan maganin yana sa bakin mahaifar mace ya bude ne wato Dilatation
■ Sai kuma abu na karshe shan magunguna daka kuma barkatai walau na hausa ko na asibiti batare da tuntubar masana ba; kuma abunda baku sani ba cikin magungunan hadda kuwa irinsu; Ibuprofen (motrin), Cataflam, Aspirin da kukafi rainawa.... Ballantana kuma Tetracycline wanda kuka fi sani da 'Ja da yellow💊 wanda wannan maganin yana da mugun hatsari koda ciki ya zauna ana iya haifo yaro me naqasa, Sauran sune su;
Chloramphenicol, Ciprofloxacin, levofloxacin, septrin, Codeine, misoprostol da masu ulcer kesha da sauransu suna nan birjik.
🌺🌺🌺
Don haka magance wannan matsalar ta 6ari ya ratayane ga magance ko kiyaye tushen da matsalar ke somowa... adena dogayen tafiye tafiye ga masu juna biyu, inkuma kunqi shikenan domin cimarmu ayau baki daya bata da kyau sai kafan daga ciki, abinci gargajiya da aka guda shine daidai da jikin mu amma da yawa sun watsar shiyasa dole jikinmu bazai lfy ba,
Sannan masu sugar su tsaya sui control sosai, madu shan magunguna barkatai su kiyaye sai bisa umarnin likita. Paracetamol shine kadai sanannen maganin ciwon jiki ko kai da aka yarda me juna biyu ta iya sha tundaga farkon ciki zuwa haihuwa
SAI KUMA YAN STILL BIRTH
Wato mutuwar jariri aciki musamman a karkara abun nan ya yawaita... toh saide kowacce akwai abunda ka iya jawo mata haka daban... don haka dalilan na iya canzawa tsakanin wata da wata saide domin asan dalilin macen ko mai gidanta ne ya kamata a sanda hakan ta faru su nemi likita dayai musu binkice ko gwaje-gwaje domin agano muku abunda ake tunanin shine tushen mutuwar jaririn da kaucewa hakan.
Toh saide bisa sanina na fahimci abubuwa da dama na kaiwa ga haddasa haka kamarsu:
■- Matsalar cikin mahaifa wato inta zamto dama ba daidai take ba tun a halittar mace domin wasu akan samesu da mahaifa biyu, ko mahaifa 1 me baki biyu, ko wacce take kankanuwa....
■- Hakama cuttuakan farji wanda s**a shiga ciki s**a ta6a mayanin mahaifar mace da tubes dinta kamar (PID)
■- Sai Hawan jini wanda inya zamto mace tai wasarairai dashi ba ashan magani ko ba'a kiyaye ci da shan abubuwan da aka hana mai hawan jinin yaci... Ko
kuma kila mace ma batasan tana dashi ba saboda ba'ajin wata alama ko canji ajika duk da galibi akan ganosa wajen Awo amma wasu basa daukar hawan jini da mahimmanci wanda illarsa ba karama bace zai iya kashe mutum farat daya... don haka yana iya jawo mutuwar jariri. Sannan hatta jijjiga yayin haihuwa shike jawota... don haka wannan shine babban dalili ayau babba da yaro yau hawan jini ya yawaita kuma da yawa basusan suna dashi ba.
■- Sai sanannen ciwon sugar a mace ko gestational diabetes wanda akan samesu dashi lokacin goyon ciki wanda bayan sun haihuwa sugar kan tafi... toh amma duk da haka bayan shekaru 10 zuwa 15 ainishin ciwon sugar kan bayyana ajikinsu na dindin din wannan ma abune da ayau ya yawaita, yana kuma daga abunda ke kashe jarirai aciki.
■- Sai karancin ruwan amniotic fluid da jariri kan rayu aciki a mahaifa,
■- Ko rashin cikar wani sashi na halitta ajaririn kamar huhu, ko uwar hanji Wanda tangardar halittun gado kan jawo
■- Sai shaye shayen magunguna daka batare da umarnin likita ba shima... ya zamto kurum mutum saide ya aika asayo masa magani a chemist hakan ka iya haddasa matsaloli kamar yadda nai bayani wajen miscarriage.
■- Sai kin zuwa awo tare da kin shan jajayen maganin folic acid da wasu matan kanyi saboda kurum basason warinsa wanda shikesa wasu har aga jaririn da tabo... ko fafukakken gadon baya... spina bifida
■- Sai karancin jini game juna biyu wanda shima kan faru ne adalilin kin zuwa awo ko haduwa da malaria a yayin goyon ciki.
■- Sai kuma yagewar wani sashi na mahaifa ya zamto mace ta rika ganin zubar jini alokacin goyon ciki kwanaki kadan kafin faruwar hakan (P. Abruption)
■- Sai kuma inya zamto igiyar cibiyar yaro wato umbilical cord dinsa nada tsayin da ta nan'naďe wuyansa ta shaqesa ya mutu musamman a masu ruwan Amniotic da yawa fite da kima saboda yawan bundun-bundun din da jariran keyi...
■- Sai kuma ikon Allah wanda saide kallo; ana iya nazarin aga duk babu ko daya cikin wadancan... kalau mace take
Don haka kunga likitocin da s**a karfi haihuwarku sune ke iya Assessing su fahimci tushen matsalar data sa yaron ya mutu...
Amma musamman masu ciwon sugar da hawan jini wajibi amaida kai wajen shan magani kullum kullum babu daga kafa, tare da gujewa cin gishiri da maggi sosai.
Masu hawan jini a tabbatar Bp bai haura 140mmhg, Masu sugar diabetes hade da Bp ku tabbatar baya haura 130.... dole kui wani abu ku tsaya ku lura da kanku tun wuri... domin hawan jini ba wasa bane kamar yadda kuke daukarsa, haka ma sugar
Sannan wajibi ne zuwa awo ga dukkan masu juna biyu, anwuce lokacin zaunawa ace za'a haihu agida, cimarmu da komi namu ya canza dole complications su yawaita.
Shyasa har matan ma rasasu ake arika ta haihu lfy agida amma ta mutu, wani bun ga jariri yaxo da rai amma ai kuskure ya sha ruwan haihuwa ya hadu da Neonatal Respiratory Distress syndrome aga yana grunting saboda babu iska ya rika canza kala yai Blue ya zamo cyanotic karshe ya mutu saboda baya iya shakar iska... wanda in a asibiti ne za'a iya cetar rayuwarsa asashi a Oxygen azuqe abunda ya kur6a....
Fatan Al'umma zaku kiyaye. Ban yadda a kwafi rubutun nan acanzashi ba ta kowanne fuska. A kiyaye!!!