26/08/2025
Shin Kun Taɓa Tambayan Kanku? Mene dalilin dayasa Masu Cin Latas Suke da Cika ken Lafiya??
Amsa!
Latas Wata Ganye ce da ake yawan amfani da ita a matsayin kayan miya ko a cikin salad. Ba wai dadi kawai take da shi ba,
tana ɗauke da gagarumin amfani ga lafiyar mu:
1. Ƙarfafa gani: Latas tana da sinadarai masu kare ido, musamman Vitamin A, wanda ke taimakawa wajen kyakkyawan gani.
2. Taimako ga hanta da jini: Yawan sinadarin iron da folate da ke cikin latas na taimaka wa jini ya gudana yadda ya kamata, kuma yana taimaka wajen hana cutar anemia.
3. Sauƙaƙa narkewar abinci: Saboda yawan fiber da ke cikinta, tana taimaka wa hanji wajen narkewa da hana matsalolin kumburin ciki da basir.
5. Kula da nauyi: Latas tana da ƙarancin calories, don haka tana taimakawa masu son rage kiba.
6. Karfafa garkuwar jiki: Latas tana dauke da Vitamin C da sauran antioxidants da ke taimaka wa jiki wajen yakar cututtuka.
7. Kwantar da hankali: An san latas tana da wasu sinadarai masu sa nutsuwa da kwantar da damuwa.
Don haka, yin amfani da latas a abinci yau da kullum ba wai kawai ado bane, babban kariya ne ga lafiyar mu.
Imam Isah S Mai Yasin Zaria.