Lafiya uwar jiki

  • Home
  • Lafiya uwar jiki

Lafiya uwar jiki Wannan page an budesa ne kawai domin abubuwan da suka shafi lafiya

03/04/2025

Barkan mu da sallah dafatan Allah Ubangi ya karbi ibadun mu ameen

New Incentives is hiring Field OfficersIf you live in any of   or   States, here's an opportunity for you to work with N...
11/10/2024

New Incentives is hiring Field Officers

If you live in any of or States, here's an opportunity for you to work with New Incentives.

You can apply via the link below 👇
https://new-incentives.breezy.hr/?&country=Nigeria

All the best ✌️

We're looking for great people to join our growing team.

Taba kidi taba karatuBLUM.....Shi Blum da ake Mining dinsa a Telegram, kusan duk masu hasashe akan project din da ake Mi...
05/06/2024

Taba kidi taba karatu
BLUM.....

Shi Blum da ake Mining dinsa a Telegram, kusan duk masu hasashe akan project din da ake Mining sun tabbatar da cewa ba wanda ya kaishi inganci bayan Notcoin, don haka nake cewa akwai bukatar mutanenmu su dage sosai wajen mining dinsa wadanda basu fara ba suyi kokari su fara tun kafin ayi musu nisa sosai...

Yadda lamarin zai kasance shine, idan kana mining din Blum kana da ragowar gurbi a referral link dinka ka saka a cikin comments section na wannan posting din, kai da kake son farawa sai ka duba ka zabi link daya ka cike ka fara Mining....

Kuma saura kwana shida a daina mining ɗinsa.

Allah ya bamu Sa'a.
https://t.me/firecoin_app_bot/app?startapp=r_7007079292
Ga Link ɗi.

22/04/2024

Mi kuke son Sani Akan ciwon (kyanda) Measles

27/12/2023

CUTAR HAWAN JINI

Cutar Hawan jini ta yawaita matuka a cikin mutane harda al’umarmu ta jinsin bakaken fata, kuma tana jawo mana illoli masu yawa.

MENENE CUTAR HAWAN JINI?

Ana cewa mutum ya kamu da wannan cuta ne idan an auna shi da
na’urar awon karfin bugun jini (wato spygmomanometer) wadda ta nuna awon jininsa ya kai, ko ya wuce, dari da arba’in bisa casa’in
(wato >140/90mmHg) kuma awon ya dauwama a haka.

Sai dai wannan adadi da aka ambata yana sabawa saboda bambancin shekaru, jinsi (wato namiji ko mace), halin da mutum yake ciki, da sauransu.

A takaice dai, sai an je asibiti za’a iya tabbatarma mutum ko yana da cutar ko baya da ita

MENENE YAKE KAWO CUTAR?

Ta la’akari da yadda wanna cuta ke faruwa ga mutane, an raba
wannan cuta zuwa gida biyu.

_Sama da kashi casa’in (>90%) na mutane dake fama
da wannan cuta, har yanzu ba’a san takamaiman dalilin da za’ace shi ya kawo masu wannan cuta ba sai dai akwai wasu abubuwa ko al’amura da aka alakanta ga faruwar wannan cuta ga wadannan mutane na kashin farko.

1_Jinsin dan-adam (anfi samu a bakaken fata)

2_Yawaita shan gishiri fiye da kima

3_ Yawaita shan barasa (giya)

4_ Kibar jiki mai tsananin yawa

5_Rashin motsa jiki, da dai sauransu

Kashi na biyu A wannan bangare, an gano wasu cututtuka na musamman da suke kawo wannan cuta.

1_ Cututtukan dake shafar kodar mutum

1_Cututtukan dake shafar kwakwalwa

2_Wasu daga cikin magunguna na bature

3_Wasu cututtuka dake shafar jijiyoyin jini

TA YAYA AKE GANE ALAMOMIN WANNAN CUTA?

Wasu daga cikin mutanen da s**a kamu da wannan cuta basu da wasu alamomi da suke ji, wasu kuma s**an ji

1_fargabar xuciyq
2_yawan ciwon kai
3_gani dishi dishi

Wasu kuma
suna zuwa asibiti ne da alamomi na illolin da cutar ta haifar musu

(zan yi bayani nan gaba). Wasu kuwa sai sunje asibiti dalilin wata cutar, wurin bincike sai a gano cewa suna da cutar hawan jini

RE_ POST________lokacin daukar ciki____ ____Wanna shi ne lokacin da mahaifa ta bude, kuma ana iya samun ciki a wannan lo...
27/12/2023

RE_ POST

________lokacin daukar ciki____ ____

Wanna shi ne lokacin da mahaifa ta bude, kuma ana iya samun ciki a wannan lokaci cikin sauki. Lokacin kan fara daga mako 1 kafin fara al'ada. Ga hanya ma fi sauki da za ki lissa kwanakin daukar ciki.

1. Ranar da kika fara ganin jini.

2. Ki duba kwanan wata, sai ki kirga kwana 15 har da ranar farko.

3. Ki lura da ranar da kika fara kirgawa.

4. Ki yi wata alama, kwana uku kafin da kuma bayan wancan kwana 15.

5 . In kika lura za ki ga kin yi alama a kwana 7

Wannan kwana 7 su ne kwanakin da mahaifarki ta bude, saboda haka su ne kwanakin daukar ciki. Lokaci ne da idan aka sadu da mace kusan akwai tabbacin daukar ciki da kashi 98 daga cikin dari.

________________________________________

Alamomin Da Ke Nuna Kin Samu Ciki Ko ba ki je wajen likita ba, za ki san cewa a mako 2 da daukar ciki za ki fara jin wadannan alamun....

1. Ciwon kai

2. Zafin jiki

3. Kasala da jin bacci

4. Girman nononki zai karu kamar lokacin da k**e al'ada

5. Za ki kara sha'awa

6. Za ki ji kwibinki na yawan ciwo

7. Za ki dinga jin zafin ciki

8. Saurin jin wari ko dandano ko gani sosai ko cin abinci da yawa

9. Tashin zuciya / amai

https://chat.whatsapp.com/Ir64EPxolaU48h7qglOinE

Join our Whatsapp group

WhatsApp Group Invite

Kira zuwa ga 'yan uwana maza game da sanitary pad (Audugar Mata)Assalamu Alaikum Warahmatullah A yan kwanakin nan naga a...
23/11/2023

Kira zuwa ga 'yan uwana maza game da sanitary pad (Audugar Mata)

Assalamu Alaikum Warahmatullah

A yan kwanakin nan naga ana ta maganar cewa an samu ƙarin kuɗin siyan Audugar mata wato 'Sanitary pad'. To a matsayinka na saurayi, aboki, kani ko kuma yaya, shin ka taɓa bawa 'yar uwarka, yan unguwarku ko budurwarka kudi ka ce taje ta siya ko kuma ka siyo mata da kanka da kudinka?

Shin ka taɓa tunanin inda mata suke samun kuɗin siya ko kuma yadda suke tambayar kudin a wajen mutane duk da cewa akwai kunya?

Shin ka taba tunanin menene amfanin wannan abun ga lafiyarsu da kuma yanayin da zasu shiga idan babu ita?

Ya kamata ka sani cewa yanzu wannan rayuwar ta sauya gaba daya, sannan zuciyoyi sun lalace kuma abubuwa sunyi tsada. Kuma yanzu ana yanayin da abinci yayi wahala ba'a magana akan sanitary pad.

Tabbas mace tana ɓukatar taimako da kulawa a kowanne irin lokaci. Sannan duk macen da ta kai shekara 12 dole tana buƙatar a jata a jiki a bata kulawa ana mata maganin damuwarta, ba maganar cewa kai babbane kace wai baka son raini, duk rashin kunyar yarinya ba ta isa ta raina mai yi mata abun alkhairi ba.

Ka sani fa dole mace ta yi iya yinta wajen ganin ta samu kuɗin da za ta siyi audugar amfani duk wani ƙarshen wata domin tsaftar jikinta da kare lafiyarta. Wata zata yi roƙo ne don ta samu ta siya, idan ta yi roƙo a wajen lalatattun mutane mai ka ke tunanin zai faru da ita a wannan gurbataccen zamanin da muke ciki?

A matsayinka na mutum mai hankali, ya kamata kayi tunanin goben ƙanwarka ko kuma sauran yan uwanmu mata da muke tare da su.

Daga karshe ina kira ga masu hannu da shuni da masu halin taimakawa dasu taimakawa yan uwanmu mata da tallafin wannan sanitary pad din domin kare lafiyarsu, domin tabbas wannan yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da kyakkyawar makoma a garesu, tsaftarsu, lafiyarsu da rayuwarsu.

Zaka iya fara wannan aikin daga cikin gidanku ko unguwarku.

Nagode!

21/11/2023

Matasa a duqufa medical check up, duk mutuwa tana da sababi, inkaji ance wane ya yanke jiki ya faɗi ya dace ka fara tunanin meke haddasa irin haka? Mutuwar fuju'a ba'a bar so bace,
Saide sau tari rashin sani kesa ai mata kallon fuju'a amma a zahiri jiki ya jima cikin jinya ƙin basa hakkinsa ake. Ina qara jan hankali don fa kana jinka lafiya hakan bai nuna lafiya kake har sai likita ya tabbatar ma.

Wanda ko yasan yana da wata larura da yake sake da sha mata magani... Ya daure ya dena, ya rungumi magani tamkar abinci, sakaci da karamar cuta kesa ta girma tafi ƙarfin jiki tare da tattalin arziki...har sai an kai ga neman taimako.

Har ga Allah mu bakaken fata Bama baiwa kula da lafiya wani muhimmanci, ina amfanin ka qare kuruciya neman kudi karshe ka karar da kudin wajen neman lafiya kuma bata samu ba antafi lahira a wahalce. Check up dinnan sau daya a shekara inkayi ya wadatar, inkana da wadata kuma kai sau biyu a shekara wato duk bayan wata shida.

Yusuf y Ibrahim

Join our whatsapp group
16/11/2023

Join our whatsapp group

WhatsApp Group Invite

▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓Yawan shafawa ko tattaɓa nono, ko kuma ya zamto me gida na yawan wasa dasu ko sanyasu a baki.Ko ...
16/11/2023

▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓

Yawan shafawa ko tattaɓa nono, ko kuma ya zamto me gida na yawan wasa dasu ko sanyasu a baki.

Ko kuwa sanya rigar nono mai santsi da zai zamto ita da kanta tamkar tana yiwa mace waiwayi,

Ko shan magungunan ulcer da ƙwarnafi musamman wanda ake kira da CIMETIDINE,

Ko Macen da aka dorata akan maganin hawan jini me suna methyldopa ko ALDOMET, Da wacce ke shan magungunan damuwa wato depression ko rangwamen hankali antipsychotics,

Da wacce ke haɗiyar ƙwayoyi ko shan garin hulba, ko shafa manta din jikin nono, ko riqa yin massage da ruwanta wato fanugreek,

Ko Macen dake amfani da maganin bada tazarar haihuwa na sha ta baki wato oral pills, ko wacce ta hadu da larurar data shafi lakar gadon baya spinal cord,, Ko Macen da aka taɓa yiwa aiki a nono, ko me larurar ƙoda,

Ko Macen da haila ke rikece mata tare da fuskantar canzawar gani zuwa dususu lokaci-lokaci gami da ciwon kai, ko harma da rashin samun juna biyu in me aure ce....wanda kan faru a sakamakon wani qaramin ƙari da ya fito a wani sashi na cikin kwakwalwarta da ake kira firolaktinoma da batasan dashi ba........

Duk wadancan ababen dana lissafa a sama na iya HADDASAWA Mace ganin RUWA clear ko RUWAN NONO na zuba daga nonuwanta walau guda ɗaya ko duk biyun... alhalin BUDURWACE ita ko matar auren da bata shayarwa kuma tasan bata da ciki.
_______________________________________

Don haka inkina daga cikin masu fuskantar wannan al'amrin saiki tsaya ki nazari kiga cikin abubuwan dana lissafa inaa kika faɗo? wanne abu k**e tunanin shine ke kawo miki wannan matsalar, ko da kuwa wasa da kai ake wajen rage sha'awa saboda takura... hakan na iya kawowa musamman idan anashafa kirjin. Kuma wannan al'amarin shi ake kira GALAKTORIYA a likitance! wato zubar ruwan nono walau fari fat ko kalar ruwa-ruwa daga nonon Macen da bata shayarwa, bata da ciki ko bama ta da aure.
_______________________________________

Hakazalik akwai wanda basu da ko guda ko basa aikata ko guda cikin wadancan abubuwa amma kuma suna fuskantar matsalar, irin wannan sune masu IDIYOFATIK GALAKTORIYA, Ma'ana Allah ne ya barwa kansa sanin dalilin matsalarsu.

Don haka wannan bawani abin damuwa bane yakan tafi da kansa, ko kuwa idan aka dena yawan stimulating na nonon. Kar kurum don mace na fuskantar haka ace za'a fassarata.

Ba abin damuwa bane, amma idan ya zamto yana fita da yawa, kuma hakan na sanya mace takura gaki da damuwa toh tana iya zuwa taga likita a binkita domin gano tushen matsalar a maganceta.
Musamman a Mace me auren da samun ciki yai wahala ga yawan ciwon kai lokaco lokaci, da canzawar gani, da rashin ganin haila akowanne wata kamar sauran Mata toh koda bata ganin komi na fita daga nononta wannan na bukatar ganin likita kwai bukatar ai Brain scan domin gano matsalar idan firolaktinoma ne abata maganin matsalar, ba'a aiki domin maganceta, maganin sha yana wadatarwa.
_______________________________________

Sannan wannan Matsala ce da har a Maza tana iya faruwa mutum yaga inya matsa nononsa ruwa na fita, hakan kan faru ga masu karancin sinadaran jima'i, sau tari ma irin wannan dama basu da sha'awa

Hakanan ana iya ganin haka ko a jariri musamman idan sinadarin istirojin na uwa ya ratsa ta mahaifa ya shiga jikin jariri ko jaririya kafin haihuwa.

✍🏻
Dr. Ibrahim Y. Yusuf

ALAMOMI '11' NA LARURAR CIWON SUGAR°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°Muna cikin kwanakin da aka ware domin ...
15/11/2023

ALAMOMI '11' NA LARURAR CIWON SUGAR
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Muna cikin kwanakin da aka ware domin wayar da kai tare da gargadi don gane da ciwon sugar a faɗin duniya.

------------------------------------------------------------------
1. YAWAN FITSARI

Bisa dabi'ar mutum kan zagaya fitsari akalla sau 4 zuwa 5 a tsawon yini, sannan yakan farka sau 1 zuwa 2 da daddare domin fitsari.

Amma a lokacin da kika ko ka sami kanka kana zarya a bandaki sama da sau 6 a tsawon yini, musamman yawan farkowa da daddare kana ta tsilla fitsari toh ka iya zama alama dake nuna ƙodojinka na aiki tuquru fiye da ƙima wajen ganin sun fitar da sikari daga cikin jininka.

Saide yawan shan ruwa musamman da yamma ka iya zamowa dalilin yawan fitsarin wani lokaci. Don haka kai kokarin kada ka qara shan ruwa daga karfe 7pm na yamma, hakanan karka sha kowanne irin lemo ko drinks.... Idan bayan qin shan kaga duk da haka kana yawan tashi ko zarya zuwa fitsari toh kwai alama me karfi na cewa akwai ciwon sugar tattare da mutum, gwaji ne xai tabbatar. Yawan fitsari batare da ana yawan shan ruwa ba alama ce babba ta ciwon sugar.

------------------------------------------------------------------
2. YAWAN KISHIRWA

Idan kana shan sama da liter 4 na ruwa, wato kimanin sama da ledar pure water 8 arana, kuma duk da haka shan ruwan baya kashe maka kishirwa yadda ya kamata to alama ce babba ta akwai matsala. Musamman jin ƙishi bayan gama shan ruwa ba jimawa.

------------------------------------------------------------------
3. SAURIN JIN YUNWA

Wani lokacin ba jimawa da gama cin abinci sai jin yunwa, mutumin ya sami kansa cikin karuwar cin abinci bakatatan, inma bai ci ba kila yaji hhar kyarma jikinsa ke yi. Wannan ma babbar alama ce. Sikarin da yaiwa yawa ya danqare ne acikin jini ke gugar wani sashi na kwakwalwar mutum yake sashi jin yunwa.

------------------------------------------------------------------
4. YAWAN KASALA

Yayin da sugar tai yawa a cikin jini batare da sauran sassan jiki su tsoka, laka, zuciya, hanta da sauransu sun tsotseta ba domin su sami kuzari....hakan zaisa ƙoda ta rika aiki ba kakkautawa don ganin ta rage adadin wannan sugar din dake cikin jini, Gajiyar da kodar ke kwasa ce ke sanyawa mutum jin kasala shima.

------------------------------------------------------------------
5. RIƘA JIN TSIKARI AJIKA KO CIWO

Sugar fiye da kima acikin jini kan lalata jijiyoyin kai sakonni, wannan tasa lokacin da kaa fara jin naman jikinka na rawa, ko ka rika jin kamar an tsikareka da allura wani lokacin, ko inka farko kaji kafafunka sun dau zafi rum ta ciki, kamar siminti ya dau rana ka takashi... Ko yawan ciwon baya, kafaɗa ko cinya da kalfatar ƙafa, aji ciwo cikin tsoka har sai an riqa dogare ƙafa jikin bango wasu lokutan in an kwanta.

Toh wannan ma na daga cikin alamomin ciwon sugar har sai abinda binkice ya nuna.

------------------------------------------------------------------
6. CANZAWAR GANI HAZO-HAZO

Sugar intai yawa tunda jiki babu sinadarin da zai narkar da ita hakan nasa murfin kaifin gani na idanu yya kumbura wato "lens swelling" wanda inya kumbura hakan bazai ba idanun damar saita ganinsu ba, saide mutum ya fara ganin dususu kamar wanda ya bude idanu a cikin ruwa, ko kamar anzuba masa mai a ido, kananun alamomi na symbol dake kan t**i baya oya ganinsu da kyau ya karanta. Wannan ma ka iya zama alama ta mutum na dauke da ciwon sugar.

------------------------------------------------------------------
7. KAIKAYIN JIKI

Saboda sugar intai yawa ajini tana kara masa kauri ya tikke, wanda hakan kesa kidneys mikewa tsaye wajen aikin cireta ta hanyar sanya mutum yawaita fitsari...toh shi kuma yawan fitsari na qara rage yawan ruwa cikin jinin wanda hakan ke sanya fata fara bushewa wanda alamar hakan itace yawan jin kaikayi. Idan har kana fuskantar wannan musamman bayan gama wanka toh kaje a duba sugar dinka, a kuma duba kodarka.

------------------------------------------------------------------
8. RASHIN SAURIN WARKEWAR CIWO

Sugar na lalata kananun jijiyoyin jini, hakan yasa in aka ji rauni baya saurin warkewa sugar din dake cikin jinin kuma kan jawo kwayoyin cuta su sami gun zama don suna son zaqi. Idan kaga kai rauni walau babba ko karami amma yaqi warkewa akan kari, ko kuwa sai yai kamar ya dauko warkewa sai ya jagule toh kaje a duba sugar jikinka.

------------------------------------------------------------------
9. SAURIN TUNZIRI

Mutum ya sami kansa ko aga ya canza ya rikide kurum ya zamo mafaɗaci, ko ya akai masa abu ba hakuri, tare da yawan son kwanciya, baison ma a rabesa, bai sha'awar yin komi kamar me cutar damuwa, toh hakan ma ka iya zama alamu na kamuwa da cutar sugar. Saboda yawaitar sugar a jika kansa mutum ya zamo mara hakuri da faɗan tsiya.

------------------------------------------------------------------
10. KWAYOYIN CUTA A MAFITSARA

Sugar din da ƙoda ke aiki tuquru wajen Flushing dinta ta cikin fitsari hakan na ba kwayoyin cuta samun damar zama a fitsara wanda karshe kan haddasawa mutum fuskantar zafin fitsari, radaɗi, warin fitsari, ko ganin farin ruwa bayan gama fitsari, ko pyelonephritis me naci yaki jin magani.

------------------------------------------------------------------
11. Canzawa guiwoyi ko wuyan mutum aga yayi shacin baƙi kamar guru, ko guiwoyin hannu da knuckles, da kuma ganin skin tags wato wasu tsirori kanana masu kamar danya.
------------------------------------------------------------------
Wannan sune manyan alamomin daka iya nuna kwai larurar sugar ajika har sai in gwaji ya nuna babu. Don haka duk me fuskantar guda ko uku daga ciki toh ya daure yaje yai gwaji, inba haka ba ya zauna toh sanne alamu zasu bayyana ya fa makaro. Kwai sama da mutum milyan 8 masu ciwon sugar batare da sunsan suna da ciwon ba

Allah shi yaye mana wahala.

✍🏻
Ibrahim Y. Yusuf

13/11/2023

ZUBAR JININ HAILA SOSAI FIYE DA ƘIMA wato "RUSHING" [HEAVY BLEEDING]
▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓

Kamar yadda in aka dafa dankali yake laushi tuɓus ta yadda ko yatsa kasa ka dirza ɓawonsa zaka ga ya saluɓe nan da nan, ko kuma saboda ma tsabar shan wuta zaka ga ya sassaluɓe ya fashe.....

Toh kwatan-kwacin abinda ke faruwa kenan a cikin mahaifar ƴaƴa Mata wato (uterus) a yayin haila. Haka mayanin bangon mahaifarsu ke ɓamɓarowa tare da saluɓowa ya zubo kamar yadda maciji ke saɓa... wanda hakan ke haifar da fitar wannan jinin wanda ake kira jinin haila bayan salubowarsa.

Sannan hakan zai sa ku fahimci yadda period keda tsananin zafi, zogi da ciwo, domin in dankali yasha wuta ka daukesa a hannu kaima kasan me ka taɓa wajen azabar zafi, Toh amma haka su Mata jikinsu ke karɓar wannan zogin, shiyasa ba banza ba wasu ke murqususu, wadu ma basa iya mikewa sosai sak sui tafiya saboda azaba yadda kowa agidan sai yasan lokacin hailar wance yayi, domin kowa da yanayin irin yadda jikinsa ke isar masa da saƙon zogi ko zafi.

____________________________________________________________________________

Zanyi ƙarin haske ne akan zubar jini sosai fiye da ƙima dakan faru da wasu matan yayin haila.

A ƙa'idance bai kamata ace yayin haila Mace ta fitar da jinin da yafi cikin sirinjin allura me lambar biyar (5ml syringe💉) ƙwaya 3 zuwa 4 ba a kullum. wato 15mls zuwa 20mls. Wannan normal ne.

Toh amma daga lokacin da jini ya zamto yana kwaranyowa wato rushing, wani lokacin harda duddunqulallan jini wato clots toh da akwai damuwa.

▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓

ALAMOMIN HEAVY BLEEDING YAYIN HAILA

Ga alamomin dake nuna Mace na zubar da jini fiye da Ƙima kuma akwai bukatar ɗaukar mataki domin babu lafiya:

1. Inya zamto duk bayan awa guda sai Mace ta canza pad saboda jikewa da jini tsawon awoyin yini a jere.

2. Ko Pad daya kurum baiwa Mace har sai ta haɗe pads biyu gu ɗaya sannan zata saka saboda yadda jinin ke kwaranyowa.

3. Ya zamto har da daddare sai kin tashi kin canza pads saboda jiqa.

4. Jinin ya cigaba da zuba har fiye da sati guda.

5. Fitar da jini a duddunqule manyan gudaji me yawa.

6. Jinin yasa bakya iya sakewa ki ayyukan yau da kullum saboda yadda yake fita.

7. Ko yawan kasala, nauyin munfashi kiji kamar iskar shaqa na miki kaɗan saboda zubar jini.

Duk macen dake fuskantar alamomi bakwai ɗoin can yayin haila to alamace dake nuna tana da HEAVY MENSTRUAL FLOW wanda ke bukatar aduba ai wani abu.

▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓

WASU DAGA CIKIN DALILAN DAKE JAWO ZUBAR JININ FIYE DA ƘIMA SUNE:

Akwai lokacin da yakan zamto abu me wahala a iya gano dalilin da yasa Mace ke zubar da jini sosai, toh amma akwai tarin ababen da binkice ya tabbatar suna jawo hakan.

1. Rashin daidaiton sinadaran jima'i, girman nono, sha'awa, haila da goyon ciki wato 'Istirojin da furojestaron". Wanda a lafiyayyar Haila ya dace ace wadannan sinadaran sunyi dede da dede wato 50/50 wanda hakan ne kesa a sami lafiyayyen mayanin mahaifa wato lining na uterus da kan kwaɓo yayin haila. Amma inya zamto babu dedeto musamman ace "Furojestaron" ya ɗara "Istirojin" wato ansami 70/30 ko 60/40 maimakon 50/50 toh hakan zaisa mayanin shimfidar cikin mahaifar a wannan wata tai kauri sosai, wanda kaurin nata shikesa saita dahu sosai kafin ta kwaɓo tabi jini ta fito, wanda hakan ke jawo aga jinin na fita fiye da ƙima domin da kyar jikin ya ɓamɓarota.... Hakan kan faru

Daga cikin abinda ke haddasa rashin wancan dedeton shine: Mace inta kasance me jiki ko ƙiba, Mace me ganin nononta na samar da ruwa duk da bata shayarwa koma kila budurwa ce, Mace me 'PCOS' wato yawan marurai jikin ƙwayayen haihuwa, Ciwon maƙoƙo, Ciwon sugar, ko kuma idan ya zamto tana haila amma bata ovulation musamman ga Matan dakan yi haila batare da wani ciwon mara ko wata damuwa sosai ba. Wanda rashin ovulation kansa wani lokacin kwatsam Mace sai taga jini a tsakiyar wata alhalin tasan ba lokacin haila bane.

Magance yawan zubar jinin a wannan Macen ya rataya ga magance matsalar macen bayan angano, walau ƙiba, pcos, ds.

______________________________________

2. Tsiron cikin Mahaifa na fayiburod (Fibroid); wanda kan fito jikin mahaifar Mace wanda suke a tsakanin shekarun haihuwa wato shekaru 15 zuwa 50. Musamman a Matan da s**a sami jinkirin haihuwa ko na aure, ko rashin daukar ciki akai-akai. Fibroid kansa zubar jini sosai ko jini yake zuwa a tsakiyar wata ya zamto lokacin da Mace bata tsammanin haila kwatsam sai taga jini, ko ya rika daukewa yana dawowa, ko haila ta wuce kwanakinta.

Yin scanning agano matsalar tare da magancesa ko aiki aciresa na jawo zubar jinin ya daidaita ya dena.
______________________________________

3. Tsiron cikin Mahaifa na Folif (polyp) shima tsirone dakan yi kamar fibroid saide shi bai cika qara girma ba, kuma yafi a Matan da s**a manyanta suke gab da dena haila. Wannan kansa ko bayan dena haila mata suke ganin jini na diga musu lokaci lokaci wato spotting. shima magancesa ta hanyar ciresa kansa a rabu da matsalar.

______________________________________

4. Sai tsiron ƙurarraji a wajen mahaifa wato "Adenomayosis" sakamakon glands din tsokokin mahaifar dakan kumbura su zamo sunyi kurji. Wannan na haddasa zubar jini sosai sosai kaga Mace na zubar da jinin haila kamar anyanka wata dabbar, sosai, tare da matsanancin ciwon mara, tare da birgima,

Zuwa ga likitocin Mata (Gynecologist) Bayan gano matsalar tare da dorata akan magani shine mafita.
______________________________________

5. Macen da aka sakamata IUD cikin mahaifa na tazarar iyali. wasu daga side effect din da s**an fuskanta shine zubar jini sosai yayin haila koma jinin ya riqa musu wasa musammman matan da aka sanyawa copper IUD me ƙunshe da estrogen da progesterone.

Don haka magance wannan matsalar shine a canzawa Mace IUD zuwa ga me progesterone kadai zalla banda estrogen, ko kuma a canza mata wata hanyar planning din zuwa implanon, allura, maganin sha ta baki ko wata hanyar daban, ana haka jinin zai dedeta.

______________________________________

6. Samun juna biyu a ɓangaren Mahaifar da bai saba aje ɗa ba, wato maimakon can cikin uterus inda yake da zurfi da faɗi, amma sai ya zamto cikin gashi acikin mahaifa amma daga farko-farkon bakin mahaifar ana wuce cervix "fulasanta firebiya" wannan kanja Mace taga jini na zuba, shine ma wasu kanyi zargin ga Mace nada ciki amma tana haila...abinda ba haka ya kamata ya faru ba.

Wannan saide a zuba idanu ai hattara, a hana mace aikin karfi sosai domin cikin na iya samun matsala akoda yaushe ko ya jawo aikin gaggawa na CS domin acire cikin.

______________________________________

7. Cutar kansar bakin mahaifa ko cikin mahaifa (cervical cancer) Zubar jini sosai sosai musamman bayan duk anyi magunguna amma abu ya cigaba hakan ka iya zama alamun dake nuna tsokokin bakin mahaifar mace sun fara rikiɗa zuwa kammanin kwayoyin kansa, Musamman ganin jini ba tsammani ko yake fita sosai, Shiyasa gashinan ake gwajin kyauta don haka zuwa aiwa Mace gwajin musamman me auren data haura shekara 30, ko wacce ke gab ko ta dena haila, wacce de aka riga aka saba saduwa da ita, Ko wacce take da zargi me karfi akan mijinta manemin Mata ne, banda ƴan Mata matukar Mace bata taɓa sanin Namiji ba, domin kwai masu amsa sunan yan Mata amma ko mai aure ba lallai takaisu sanin daɗin Namiji ba irin wannan sune kan gaba cikin wanda ya dace suje ai musu cervical cancer screening da za'a buɗe asa spatula a dangwalo majinar bakin mahaifarsu a tantance.
______________________________________

8. Hakazalik Matsalar ka iya zamowa adalilin larurar zubar jini ta gado sakamakon sun gaji karancin sinadaran dake sanya jini tikkewa da sauran tsaida zubarsa, kamar su hemofiliya ko Bonwilbiran. Irin wannan larura ce ta gado baka iya rabasu da ita complete saide ana iya basu magani da zai takaita fitarsa don ganin ba ashiga wahala ba.
______________________________________

9. Hakazalik yana iya kasancewa a dalilin wani magani da Mace kan amfani dashi wanda shine ke sanya period na mata rushing. kamar Maganin tazarar haihuwa nasha wato OCP, ko maganin katsa jini ga masu larurar kumburi ko ciwon zuciya da akan basu, ko shan magani irinsu Aspirin. Irin wadannan dakatar dasu ko canza musu kalar magani shine mafita.

______________________________________

10. Matan dake da ciwon koda, ko ciwon hanta ko makoko wato "thyroid disease" suma s**an fuskanci wannan matsalar. Don haka maida hankali wajen maganin matsalar shi zai taimaka su rabi da heavy bleeding din.

▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓▓

Kuyi haƙuri rubutun yai tsayi duk da ahakan ma na takaicesa sosai. Don haka kowacce Matsala kunji abinda na faɗa matsayin hanyar magance ta, don haka zuwa ga kwararun likitoci medical doctors da kuma Gynecologist likitocin Mata shine zai taimaka agano tushen matsalar da kuma hanyar da za'a bi a magance. Karki ce ai naje asibiti amma har yau... A'a ta yiwu ba babban asibiti kikaje kikaga Gyne doctor ba. inma shi kika gani in babu canji ba laifi bane kije wani asibitin ki qara ganin wani gynea ko medical doctor din, ta yiwu a sami bambancin kwarewar aiki.

____________________________________________________________________________

✍🏼
Dr. Ibrahim Y. Yusuf
30th Sept, 2023

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lafiya uwar jiki posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your practice to be the top-listed Clinic?

Share