02/11/2025
Episiotomy (Yankan Haihuwa)
Episiotomy yana nufin yankan da likita ko ungozoma ke yi a wajen farji ( tsakanin farji da dubura ) domin fadada hanyar haihuwa lokacin da mace ke haihuwa.
π©Ί Dalilan da ake yin Episiotomy
Ana yin sa ne idan:
Ana so a hana tsagewar perineum (wajen tsakanin farji da dubura).
Haihuwa ta yi tsanani kuma ana son a taimaka wa jariri ya fito da sauri.
Ana amfani da kayan taimako kamar forceps ko vacuum.
Jariri yana da girma sosai ko kuma wajen haihuwar ya yi Ζunci (musamman a farkon haihuwa).