Taska

Taska Dubban Hanyoyi na Dabarun saukake Fahimtar rayuwa.

20/11/2025

Anayi mata allura ni iya yin mata kukan zuci🥲 gobe kuma in tayata murna... 🫠

19/11/2025

Fati
Fatima
Zahra
Fatou
Fatumata
FatFat
🤦‍♀️

Wallahi sai da hankalina ya yi mugun tashi da na shiga ɗakin tiyatar idanu na ga yadda ake ta faman yanka ƙwayan ido ana...
19/11/2025

Wallahi sai da hankalina ya yi mugun tashi da na shiga ɗakin tiyatar idanu na ga yadda ake ta faman yanka ƙwayan ido ana ta tsira allura ana aiki.

Wannan yaro ba ya gani da ido daya amma inshallah zai sami ganinsa da idanunsa biyu.

Allah ka azurtamu da lafiya mai dorewa.

18/11/2025

Wallahi masu suna Fati /Fatima sun yi yawa aƙasar nan ya kamata mu shirya yadda za mu kakkabe wasu daga ciki. 🤭

Wannan comment din ya nemi ya tayar min da hankali. Tabbas na haura shekara 10 ba na rayuwa a Najeriya, amma ina tunanin...
18/11/2025

Wannan comment din ya nemi ya tayar min da hankali.
Tabbas na haura shekara 10 ba na rayuwa a Najeriya, amma ina tunanin akwai ƙari da ƙazafi kan wannan maganar. Sakamakon malam Bahaushe a yau ba shine na jiya ba.....

Ziyarata ta ƙarshe zuwa gidan marayu na ga wasu tagwaye da ba a san inda uyayensu suke ba. Kai tsaye zuciyata ta kamu sa...
17/11/2025

Ziyarata ta ƙarshe zuwa gidan marayu na ga wasu tagwaye da ba a san inda uyayensu suke ba.

Kai tsaye zuciyata ta kamu sa soyayyarsu.

17/11/2025

Yanzu nake samun labarin ƙanuwar abokina da mijinta ya sace mata katifa bayan iyayenta sun raba aurensu sakamakon rashin ciyarwa da son zaman banza.
Ta je kwashe kayanta sai ta tarar an babu katifa. Daga baya ta nema ya dawo mata da katifarta don ma har ta tausaya masa ta aje masa bargo, amma ya ƙi dawuwa da shi, sai ma cewa yake kawai ta yi hakuri ta yafe wannan katifa...

Wani abu ne kuka taɓa sa mishi lokaci, kuna tunanin ya yi nisa sai ga shi kamar mafarki har ya zo ya wuce muku🤔 Bari yau...
15/11/2025

Wani abu ne kuka taɓa sa mishi lokaci, kuna tunanin ya yi nisa sai ga shi kamar mafarki har ya zo ya wuce muku🤔

Bari yau mu ɗauki darasi. Have a seat 💺in the CS

15/11/2025

Wannan shine sirrin samun nasarar amfanin karatun islamiyya a Nijar fiye da Najeriya.

Da Hausa suke yin komai. A Najeriya kuma sai su ce komai sai an yi da larabci...
Yaranmu ba su san me ake faɗa ba.

14/11/2025

Misalin Hadisi da ya ci karo da Aya:

Ƙissar Sarauniyar Saba'i da ya zo a Al-ƙur'anin (Bilqis/Balƙis) ta zamanin Annabi Sulaiman.

Malamai Suna bayyanata a matsayin wacce ta kware wajen jagorancin al'umma ta yadda dukkan al'ummarta suna matukar jin maganarta kuma tana shawara da su a komai kafin ta yanke hukunci. Malamai suna bayyana cewa: haka ya sa mulkinta ya yi nasara kuma ya zama abin buga misali game da shugabanci na gari.

Sannan akwai wani Hadisi ingantacce (a sharadin inganci) da ya zo a Sahihul Buhari da yake cewa: an ruwaito annabi ya ce duk al'ummar da naɗa ƴa mace shugabancin al'amuranta ba za ta taba yin nasara ba. (لن تفلح قوم ولوا أمرهم امرأة).

Fuskar cin karo shine Allah ya kawo misalin Wannan Sarauniya da take jagorantar al'umma kuma ta yi nasara.
Sannan kuma an ce annabi ya taɓa faɗa cewa duk al'ummar da ta sanya ya mace a shugabanci sai sun yi asara.

Wanda haka ya sa wasu malamai suke daukar hukuncin hadisin wajen haramta cewa a bar mace ta zama shugaba ko alƙali, wasu ma s**a ce ko wani irin jagoranci ne bai halasta a bar mace ta yi ba.
Wasu malaman kuma s**a yi amfani da ayoyi s**a ce ba matsala bane don an ƴa mace ta zama shugaba.

Wanne ya kamata mu ɗauka a nan. Ayoyi ko Hadisi🤔

13/11/2025

Bari mu dawo fagen muhawara mu ɗan tattauna.
Shin kuna ganin ana samun cin karo tsakanin Ayoyi da Hadisai ? 🤔

13/11/2025

(You are f00l)
Reply as a gentle person
Let's go 🥰😋❤️🔐

Address

Kano
810241

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taska posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Taska:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram