21/09/2024
Shin me Al-Qur'ani Ya Ce akan istimna’i ?
Alqur'ani ya nuna cewa istimna’i haramun ne a cikin aya ta 5-7 na suratul al-Mu'minun. Ayoyin sun yi magana kan siffofin muminai. Allah yana cewa muminai suna da siffofi k**ar haka:
وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ ﴿٥﴾ إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ ﴿٦﴾ فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ ﴿٧﴾
Kuma waɗanda suke tsare farjojinsu. (5) (Sai dai daga mãtan aurensu da kuyanginsu, to, bã zã su zama abin zargi ba.
Don haka aya ta bakwai tana bayani ne akan duk wanda suke biyawa kansu buqata ba ta hanyar aure ba to lallai sun aikata zunubi. Wannan ya haɗa da fasikanci, zina, luwadi, madigo, da istimna’i
Me Hadisi yace akan istimna’i ?
Ruwayoyi da dama daga Manzon Allah (s) da Imamai (a) sun yi magana kan haramcin istimna’i a Musulunci. An yi amfani da lafuzza daban-daban wajen istimna’i a hadisi, k**ar shafar al'aura (daki), auren kai, da auren hanu. Imam Ja’afar Sadik (a) ya ce istimna’i k**ar zina take. Manzon Allah (s) yace;
نَاکِحُ الْکَفِّ مَلْعُونٌ
Tsinuwa ta tabbata ga wanda suke auren hannu (zinar hannu). awarin ba zai sake yin ta ba.
Idan mutum ya aikata istimna’i yaya zai yi?
Idan mutum, Allah ya kiyaye, ya aikata istimna’i , dole ne ya dauki wasu matakai. Da farko dai wajibi ne ya tuba daga wannan babban zunubi. Idan mutum ya yi istimna’i kuma ya fitar da maniyyi dole sai yayi wankan janaba, ma'ana najasa ce wadda dole ne a cire ta hanyar wankan janaba. Don haka idan mutum zai yi sallah wajibi ne sai yayi wankan janaba. Abin lura anan shi ne duk wani nau'i na janaba, walau ta hanyar halal ko haram, to lallai sai an kawar da ita ta hanyar janabah.
Idan mutum yayi wankan janaba ba lallai sai yayi alwala ba idan yana son yin sallah, sai dai idan alwalar tashi ta baci.