17/01/2025
KAI'KAYIN NONO (BREAST ITCHING)!!!
--------___________@
REVISION
Kaikayi walau a budurwa ko amai aure, ko waccen data ta6a haihuwa ko kuwa sabanin hakan abune dake faruwa.
Nono de bangare ne na jiki da ya kunshi mashimman kwayoyin halittu daban daban gami da kitse da lallausar tsoka mai ragaraga tattare cikinsa da kuma acan kansa (ni**le) wadanda duk ke taimaka masa ya zamo yanajin ta6i da samar da wadataccen ruwan nono don jin dadin shayar wa idan lokacin bukatar hakan tataso.
Kaikayin nono yakan zamo abu mara dadi gami da takura ga mace musamman budurwa, sannan hakan awani bangaren ka iya kasancewa alama dake nuna samuwar wata matsala amma de yawanci abunda ke jawo hakan sun hada da:-
1- Shigar ko hawan kwayoyin cuta (infection) kan fatar nono wannan kan jawo kaikayi awasu lokutan susar ta jawo kuraje inda gurin ka iya dadewa.
2- Sai inya kasance ana wanke rigar nono da wani sinadarin omo ko sabulu da fatar macen bataso hakan ka iyasa idan mace tai zufa irritant din ya nuso bra din tafara jin kaikayin.
3- ko Kuma sabulun wankan mace ya kasance allergies ga jikinta. Ko kuma Shanya irin Wannan kaya arana bayan wankesu ciki harda pant. -Anfi so ake shanyasu adaki.
4- Sannan ka iya kasancewa alama dake nuna akwai wani nau'i da ka iya haddasa sankarar nono (breast cancer) ajikin nonon wato bayyanar Kari ko ince lump acikin breast.
5- Akwai Kuma yanayin reaction na tafiyar sinadaran hormones na glands din cikin nono irinsu prolactin hakan ma nasa wasu suke jin kaikayi musamman amata masu karfin sha'awa..
6- Zufa a mata masu kiba da yawan zufa akai akai wannan ma nasa ingumin ya ratsa fata suji duk sun takura inda inba canza wata bra din s**ai ba ko s**a cire kaya s**a sha iska wannan na jawo kaikayin.
SHAWARA
Akan yi kokari agano a inda matsalar take a magance walau shawarwari ko magungunan rage radadi.
Sannan asan irin sabulu ko Omo da za'a ke wanke irin wadannan inner wear din.
In an wanke su ake shanysu inda hali a inuwa Koma cikin daki Sab