16/01/2026
Saƙon Sanarwa ga Mambobin Ƙungiya
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh,
Muna gaishe ku da fatan alkhairi tare da fatan kuna cikin koshin lafiya.
Muna sanar da dukkan mambobin wannan ƙungiya mai albarka cewa, an sauya sunan ƙungiyarmu daga:
“Nigeria Union of Medical Herbal Practitioners (NUMHP)”
zuwa
“Nigeria Traditional Herbal Medicine Workers Union (NTHMWU)”.
Wannan sauyi ya biyo bayan sababbin tsare-tsare da ci gaban da aka samu wajen daidaita harkokin ƙungiyarmu da tsarin Nigerian Labour Congress (NLC), inda yanzu ƙungiyarmu ta samu cikakken rajista da sahalewa a matsayin ƙungiya ta ƙwararru a matakin ƙasa.
Alhamdulillahi, wannan babbar nasara ce ga dukkan mambobin ƙungiyarmu, domin hakan zai ƙara tabbatar da martabar masu aikin magungunan gargajiya, kare haƙƙin ma’aikata, da kuma inganta tsari, horo, da haɗin kai a tsakaninmu.
Muna fatan wannan sabon ci gaba zai ƙara kawo cigaba, haɗin kai, da albarka ga ƙungiyarmu da kuma al’ummar ƙasa baki ɗaya.
Allah Ya sanya wannan sauyi ya zamo alheri ga kowa.
Na gode da kulawa da haɗin kai.
✍️Imrana Mansur