Ask Doctor - Tambayi likita

Ask Doctor - Tambayi likita Muna amsa tambayoyi kan abunda ya shafi lafiyar jikin mu. A turo mana sakon tambayoyi ta inbox.

MENENE CUTAR TYPHOID (taifod).Taifod cuta ce da take k**a ƙaramin hanji. Illar ta yana farawa daga ƙaramin hanji sannan ...
28/07/2023

MENENE CUTAR TYPHOID (taifod).
Taifod cuta ce da take k**a ƙaramin hanji. Illar ta yana farawa daga ƙaramin hanji sannan ya bazu zuwa sassa daban na jikin mutum idan ba'a magance ta akan lokaci ba.

MENENE YAKE KAWO CUTAR TAIFOD: kwayar cutar bacteria mai suna salmonella typhi ita ke haddasa cutar taifod a mafi akasarin lokaci, sai kwayar cutar salmonella paratyphi wacce itama tana kawo cutar ta taifod.

TA WACCE HANYA AKE KAMUWA DA CUTAR TAIFOD: Taifod cuta ce da take yaɗuwa ta hanyar cin gurɓataccen abincin da yake dauke da kwayar cutar ko shan ruwa mara tsafta wanda yake dauke da kwayar cutar.

ALAMOMIN CUTAR TAIFOD: Zazzaɓi mai zafi wanda baya sauka, Ciwon kai, Ciwon ciki, Ciwon jiki/gaɓoɓo, Kasala, Amai gudawa suna daga cikin alamomin cutar taifod.

GWAJIN DA AKEYI WAJEN TABBATAR DA CUTAR TAIFOD: Daga cikin gwaje-gwajen da akeyi dan tabbatar da cutar akwai gwajin jini wanda ake daukan jinin mutumin da yake da alamomin cutar taifod a duba da na'ura a nemi kwayar cutar salmonella typhi ko paratyphi. Akwai gwajin bahaya da ake yi wanda shima ana duba kwayar cutar ne a cikin bahaya. Sauran gwaje-gwaje sun hada da gwarin ɓargo da gwajin fitsari.

MATSALOLIN DA CUTAR TAIFOD KAN IYA HADDASAWA IDAN TA DAUKI LOKACI A JIKIN MUTUM BA'A MAGANCE TA BA: Gane cutar da magance ta akan lokaci yana da matuƙar muhimmanci saboda rashin ganewa ko magance ta a kan lokaci yana iya jawo matsaloli masu haɗarin gaske a jikin mutum wanda har ana iya rasa rai a ɗan karamin lokaci, misali hujewar hanji, kwararar jini daga jikin hanci, tana iya taɓa hanta ta jawo cutar hanta, tana iya taɓa zuciya tasa zuciyar ta kumbura, ana iya mutuwa sanadiyar zubewar jini ko ƙarewan ruwan jiki.

MATAKAN DA ZA'A BI DON KIYAYE KAI DAGA KAMUWA DA CUTAR TAIFOD: Hanyoyin da ake bi wajen kare kai daga kamuwa daga cutar taifod hanyoyi ne masu sauki, kasancewar cutar tana yaɗuwa ne ta hanyar cin abincin ko shan ruwan da yake dauke da kwayar cutar. Tsaftar abinci da abun sha shine matakin farko wajen kare kai daga cutar. Samun hanyoyin samun ruwa mai tsafta, tsaftace abinci sosai kafin a ci musamman abubuwan da ake cin su ɗanye irin su ganyayyaki da kayan marmari, Wanke hannu da sabulu kafin a ci abinci da bayan an shiga banɗaki.
Allah yasa mu dace.

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ask Doctor - Tambayi likita posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Ask Doctor - Tambayi likita:

Share

Category