Al-Ihsan Isamic Medicine Research Centre.

Al-Ihsan Isamic Medicine Research Centre. Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Al-Ihsan Isamic Medicine Research Centre., Medical and health, SDP Anguwan dodo Tifa garage Gwagwalada Abuja, Abuja.

AMFANIN SHAIHA ( Tazargade) GA AL'AURAR MACE************************************************Tazargade yanada tasiri sosa...
12/11/2023

AMFANIN SHAIHA ( Tazargade) GA AL'AURAR MACE
************************************************
Tazargade yanada tasiri sosai wajen gyara al'aurar mace musamman ma wajen kara matsi ma macenta tahaifu, kokuma gabanta yabude sosai, sannan yana taimakawa wajen kashe kwayoyin infection Wanda yake janyo abubuwa kamar haka:
- Karancin ni'ima.
- Rashin jindadin saduwa da maigida.
- Bushewar gaba.
- Jinzafi lokacin saduwa.
- Fitar farin ruwa kamar kindirmu.
- Kaikayi. Dasauranu.

YADDA AKE AMFANI DASHI
Za'a debi cikin babban cokali daya azubashi acikin tafasasshen ruwa kamar litre biyu daga bisani sai abarshi yadan huce kadan, sai ashiga ciki azauna kamar minti goma. Anaso amaimaita haka kullum sau daya natsawon sati daya insha Allahu zakiga abin mamaki.

AL-IHSAN ISLAMIC MEDICINE & RESEARCH CENTRE, GWAGWALADA

12/11/2023

MAGANIN I'INA KO NAWIN BAKI
**********************************
Idan aka samu yaro Wanda yayi nawin baki yayi shekara biyu zuwa sama baya magana har kannen bayansa ma suna magana
kokuma yara masu magana da kyar suna i'ina sai amusu wannan hadin domin sufara magana yadda sauran mutane sukeyi.
1- 10grm na man habba.
2- 10grm na man Zaitu lawz huluwu.
3- 10grm na man Na'ana
4- 10grm na man Zi'itir
5- 10grm na man Bardaquish.
Za'a hadasu awaje daya kuma yawansu yazama daidai agarwaya sosai, sai kullum abashi karamin cokali dasafe bayan anci abincin breakfast da minti talatin 30 minutes.
AL-IHSAN ISLAMIC MEDICINE CENTRE, GWAGWALADA
09030538005

12/11/2023

SHAN RUWAN DUMI DASAFE
******************************
Lalle shan ruwan dumi dasafe yanada matukan tasiri wajen magance cututtuka dadama ajikin mutum kamar irinsu:
- Hawan jini
- Ciwon kai
- Ciwon zuciya
- Rage kitse
- Farfadiya
- paralyse
- Ciwon gabobi
- Matsalolin ido
- Matsalolin kunne
- Matsalolin Wuya.
- Rashin daidaituwan jinin al'ada.
Anaso asha ruwan dumi kada yayi zafi kaman shayi amfison wanda mutum zai iya shanyewa gabadaya inyadaura abakinsa amma yazama da dumi, sannan yazam kafin break fast sannan asamu ratan minti arba'in kafin aci ko asha wani abu bayan bayan shan ruwan.

AL-IHSAN ISLAMIC MEDICINE & RESEARCH CENTRE, GWAGWALADA 09030538005

12/11/2023

AMFANIN BAWON KWAI
*************************
Dayawa daga cikin mutane basusan dacewa bawon kwai yana kunsheda sinadarin CALCIUM har kashi 90% cikin dari ba, wanda shiyakeda alhakin karfafa kashi da hakora ajikin mutum, Kamar yadda bawon kwai yana kunsheda wasu sinadarai daban kamar irinsu Iron, Manganese, Phosphorus, Zinc, Fluorine, Copper, Chromium, Molybdenum.
Sinadarin Calcium dake cikin bawon kwai yana iya zama magani ga matsalolin Calcium damutane suke fama dashi ayanzu, masamman ma mata masu juna biyu da masu shayarwa.
Domin samun dukkanin fa'idojin karin lafiya da bawon kwai yake kunshe dashi, ana iya sarrafashi kamar haka:
Za'a samu bawon kwai kwara biyar sai adakata tayi laushi sosai sannan azubata acikin ruwa litre uku sai asanyata acikin fridge akyaleshi tsawon sati guda har bawon yajike sosai, sannan za'a iya zuba mata lemon tsami kadan aciki, sai asha kofi daddaya kullum har yakare.

AL-IHSAN ISLAMIC MEDICINE & RESEARCH CENTRE, GWAGWALADA

12/11/2023

AMFANIN TSAMIYA A JIKIN DAN ADAM.
*****************************************
Kamar yadda ya kasance sanannen abu
gurin mu Musulmi, ba wani icen da Allah (swt)
Ya halitta face da irin ta sa fa'idar, sai dai ya kasance an gano wannan fa'idar ko kuma ba'a gano ta ba. Duk da tsamiya aba ce me tsami amma tana da abubuwa da yawa na Karin lafiya , sannan tana kunshe da sinadaran kara lafiya da kuzari da sauransu.
A cikin dukkan kayan marmari tsamiya tana da ingantattun sinadaran iron, magnesium, niacin, phosphrous, protein, da potassium amma me ciwon siga zai yi kokarin Kada ya sha saboda tana kunshe da sikari.
Har ila yau tsamiya tana da mahimmanci ga me al'ada saboda ingancin abubuwan
gina jiki data kuntsa.
Ciwon Mara lokacin Al'ada;
Ana hada tsamiya da man zaitun dan asha don maganin ciwon mara na lokacin al'ada dama wanda bana al'ada ba. Ana shan tsamiya saboda kumburin ciki ko rashin bayan gida, ciwon hanta da mafitsara da ciwon ciki.
Ana maganin sanyi da zazzabi, akan baiwa yara saboda tsutsar ciki. A kan sarrafa yayan tsamiya don maganin karaya. Ruwan yayan tsamiya na maganin bushewar ido akan disa shi a ido.
Wasu daga cikin amfanin tsamiya dai sun kunshi:
- Yaki don hana kamuwa da cutar 'cancer'
- Kariya daga karancin sinadarin 'vitamin c.
- Saukaka ciwon zazzabi
- Kariya daga kamuwa da mura
- Taimakon jiki wajen narkar da abinci
- Saukaka cushewar ciki
- Ragewa jiki yawan kitsen 'cholesterol'
- Taimako wajen inganta lafiyar zuciya
- Kurkura ruwanta na saukaka kaikayin makogwaro na mura
- Dafaffen ganyenta na maganin ciwon
'ulcer' da taimakawa wajen kashe tsutsar ciki ga yara
- Ta na maganin basir
- Taimako wajen tace jini.
Kazalika ana iya amfani da ita don magance cututtuka da dama, kadan daga ciki su ne:
•Maruru
•Gudawa
•Amai
•Cututtukan hanta
•Kuturta
•Cututtukan fata
•Ciwon ido
•Guba.

AL-IHSAN ISLAMIC MEDICINE CENTRE, GWAGWALADA

12/11/2023

AMFANIN BAWON TAFARNUWA
*********************************
Kada kajefarda bawon tafarnuwa, domin kusan amfaninsu dayane da tafarnuwan, wato ita bawon tafarnuwa ana ganin kamar batada amfani... Ashe itama tanada nata amfani kamar yadda ita tafarnuwan kanta takeda amfani, tana daukeda sinadarai masu yawa waenda suke kare mutum daga cututtuka dadama, daga cikin:
- Bawon tafarnuwa kariyace babba daga kamuwa da cutar daji wato (Cancer ) ko wace iri ajikin Dan Adam, idan aka tafasa anashan ruwanta.
- Bawon tafarnuwa tana taimako wajen kara tsayin gashin mata tareda kashe amosanin kai Wanda shi yake cinyewa mata gashi, idan aka tafasa sai azuba man zaitun aciki kafin asauke akan wutan sannan daga bisani sai abarta tahuce sai awanke gashin da'ita, sai anemi sabulu mai kamshi ko shamfo awanke gashin saboda rabuwa da warin tafarnuwan.
- Yana taimakawa wajen kariya daga kamuwa da hawan jini sannan tana rage yawan cholesterol dake cikin jini.
- Yana daidaita insulin dake jikin mutum Wanda zai dedeta sugar dake jikin mutum.
- Yana magance matsalar Farfadiya da ikon Allah idan ana tafasawa ana baiwa mai wannan matsalan, sai kaga mutum yawarke daga wannan matsalan har abada.
- Yana karfafa garkuwan jikin mutum Wanda zasuyi fada da duk wani cuta mai cutarwa acikin jiki.

AL-IHSAN ISLAMIC MEDICINE AND RESEARCH CENTER GWAGWALADA
09030538005

12/11/2023

KARIN NI'IMA GA MATA.
**************************
Tabbas mace komai kyawunta idan bata da ni,imar jiki to bata iya gamsar da mijinta, dole mijinta yashiga damuwa, to amman ni'imar mace ya dan ganta da irin nau'in abincin datake ci. Amman matsalar itace basa tuntubar masana dan basu haske, saidai kawai suyi ta sayan magungunan yan kasuwa wanda basa dadewa a jikinsu wasuma basa aiki. Ga duk macen dakeson samun ni'ima a jikinta tota liqewa wannan sinadarin. Kuma ana hadin ne da dare idan sun jiku da safe akesha.
1. Asamu kankana (water milon)meyashi sai a fafe samansa da wuka ayi mata kofa.
2. Asamu kanumfari (Clove) a dakashi a zuba acikin kankanar.
3. Asamu dabino a nikashi a zuba a cikin kankanar.
4. Kwakwa (coconut) kwallo daya a fasa ta a zuba ruwan cikin
kan kanar sannan kwakwar ma a nika ta a zuba cikin kankanar. Sai a rufe kankana saida safe sun jiku sai uwar gida tashanye ruwan tas sannan ta cinye kankanar. Zaki bawa kawarki labari. Anaso mace ta yawaita wannan abun zatai kima da martaba ga mai gidanta.
Kila ma megida ya baki kyautar motarsa saida safe ayita rigima. Wallahi Insha Allahu duk wacce tayi amfani da wannan sinsadarin zata yaba kuma zata kara yiwa Allah godiya.

AL-IHSAN ISLAMIC MEDICINE AND RESEARCH CENTER, GWAGWALADA
09030538005

12/11/2023

JINNUL ASHIQ
Assalamu alaikum warahmatullah Al-Ihsan Isamic Medicine And Research Centre,
sunyi kokarin bayyana maku wani sharrin aljanin JINNUL ASHIQ waton aljanin soyayya kokuma JINNUL ASHIQA aljanar soyayya. Kamar yanda muka sani shine munada nau’ikan aljanu sinfi kusan 10 wanda kowane daga cikinsu yanada hatsari sannan kuma yanada kalar cutarwar da yake yiwa dan Adam idan har ya shiga jikinsa kokuma ya shafe shi.
Akwai JINNUL ASHIQA
JINNUL ADHFAL
JINNUL DHAYYAR
JINNUL MAKABIR
KIDIMUL HAMMAMI
JINNUL JALABI
JINNUL GAWWAS
ÃMIRUL BAITI
JINNUT TABADDIL
JINNUL LAMSI WAL MASSI
Amma zamuyi bayani ne dangane da Jinnul ashiq/ashiqa sakamakon shine mafi hatsarin cikinsu ga lafiyar dan Adam.
Shidai Jinnul ashiq wani nau’in aljanine wanda yake shiga jikin dan Adam yana cutar da lafiyarsa tun daga kan mu’amalarsa ta yau da kullum harzuwa ga lamarinsa na auratayya ko kuma soyayya. Shidai jinnu ASHIQ yana shiga ajikin dan Adam ne da nufin soyayya sannan kuma shi jinnul ashiq ya kasance shine mafiya hatsabibancin aljanu domin kuwa shine aljani wanda yake ZINA da bil adama. Hakika bincike ya nuna cewa lallai aljani yanada sha’awa ninki fiyeda dan Adam adon haka abu kadan ne wanda zai bayyanar masa daga dan adam na tsiraici kokuma mai dada sha’wa yaji yakamu da sha’awar wannan bil adaman.
Dalilai da suke sanyawa Jinnul ashiq ya shiga jikin bil’adama
a. Bayyanar da al’aura acikin gida(ga mace ko namiji) musamman mata masu sanya kaya masu bayyanar da surar jikinsu dakuma bayyanar da asalin halittar jikinsu.
b. Barin gashin kai a bude(mata).
c. Shiga bandaki(toilet)ba tareda ambaton Allah ba.
d. Yawan zama cikin kazanta/ko son kazantar.
e. Yin shiga irin ta al’ada
f. Dalilin sihiri.
a. Bayyanar da al’aura acikin gida(ga mace ko namiji) musamman mata masu sanya kaya masu bayyanar da surar jikinsu dakuma bayyanar da asalin halittar jikinsu.
b. Mata masu barin gashinsu JINNUL ASHIQ

Address

SDP Anguwan Dodo Tifa Garage Gwagwalada Abuja
Abuja

Telephone

+2349030538005

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-Ihsan Isamic Medicine Research Centre. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram