16/07/2025
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Jagoranci Gwamnonin Arewa Wajen Jana'izar Marigayi Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa (NSGF) kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, a jiya, ya jagoranci takwarorinsa domin halartar jana’izar marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda aka yi jana’izarsa a gidansa da ke Daura, jihar Katsina.
Gwamna Inuwa Yahaya ya samu tarbar Gwamna Dikko Umar Radda da wasu manyan jami’an gwamnati da manyan baki a lokacin da ya isa Katsina.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci dubun al'ummar kasar wajen yi wa marigayi jagoran Najeriya gaisuwar ta'aziyya.
Daga cikin manyan bakin da s**a halarci taron akwai shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno, shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embaló, da firaminista Ali Mahamane Lamine Zeine na Jamhuriyar Nijar.
Haka kuma akwai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, da masu rike da mukamai da kuma tsofaffin gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisa, da sauran manyan jami’ai da manyan baki daga ciki da wajen kasar nan.
An gudanar da Sallar jana'izar ne a unguwar helipad dake garin Daura, wanda babban limamin Daura, Sheikh Salisu Rabiu ya jagoranta.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi yabi marigayin tare da yi wa tsohon shugaban kasar addu’ar Allah ya jikansa da rahama, yana mai addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.
Da yake zantawa da manema labarai, Gwamna Inuwa Yahaya, ya bayyana marigayi shugaba Buhari a matsayin mai gaskiya, kishin kasa da kuma shugaban Da bai Da son kai.
Ya yi nuni da cewa tsohon shugaban kasa Buhari ya rayu kuma yayi jagoranci bisa ka’ida, tare da sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Nijeriya hidima da daukaka al’ummarta, musamman talakawa.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce "A yau al'ummar kasar nan na bankwana da dan jiha na gaskiya, abin da ya gada shine Rayuwa Mai sauki, da'a da kishin kasa, shugaba Buhari zai ci gaba da kasancewa cikin tarihin kasarmu har abada."