26/10/2025
CIGABA A JIHAR BAUCHI Tarihi Ya Canza: An Rushe Kofar Wunti Domin Cigaba da Aikin Flyover a Bauchi
26 ga Oktoba, 2025
Tarihi ya sake rubutu yau a garin Bauchi, yayin da aka rushe tsohuwar Kofar Wunti, ɗaya daga cikin muhimman wuraren tarihi da s**a daɗe suna wakiltar asalin tsohon birnin Bauchi. Wannan mataki ya biyo bayan cigaban aikin gine-ginen Flyover da Gwamnatin Jihar Bauchi ke aiwatarwa domin inganta zirga-zirga da bunƙasa tsarin birane.
Kofar Wunti ta kasance ɗaya daga cikin fitattun ƙofofin tsohon Bauchi tun zamanin Sarkin Bauchi Malam Yakubu, . A wancan lokaci, ta kasance babbar hanya ta shiga cikin Birnin Bauchi, inda ake kula da tsaron gari da kuma masu shiga da fita. Haka kuma ta zama alamar tarihi da girmamawa ga al’ummar Bauchi
Sai dai duk da rushewar ƙofar don ci gaban zamani, akwai yiwuwar sake ginawa sabuwar Kofar Wunti domin ci gaba da wanzar da tarihi da kuma tabbatar da cewa wannan alama ta tarihi ba ta shuɗe ba.
Akwai Tabbacin sake inganta sabuwar wannan Tarihi.
Masu lura da harkokin tarihi da al’adu sun yaba da wannan mataki, suna cewa sake gina sabuwar ƙofar zai zama hanyar haɗa tarihi da cigaban zamani, da kuma tunawa da gagarumar gudunmawar da tsohuwar Kofar Wunti ta bayar wajen kafa da kare garin Bauchi tun fil azal.
A halin yanzu, aikin Flyover na ci gaba da tafiya cikin sauri — wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin jihar domin sauƙaƙa zirga-zirga, inganta gine-gine, da kyautata rayuwar jama’a. Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad kauran Bauchi ne ke aiwatarwa.
Me zaku ce kan hakan...?