01/08/2025
Yawan Shan Vitamin C na iya illata mu.
Vitamin C muhimmin sinadari ne da ke taimakawa wajen kula da lafiyar jikinmu. Amma shan shi fiye da kima na iya haifar da illa, musamman ga ƙoda.
Yau zamu yi bayani akan yadda Vitamin C ke tasiri ga ƙoda da kuma abubuwan da ya kamata mu kiyaye.
Idan muka sha Vitamin C da yawa, jikinmu yana mai da shi wani abu da ake kira oxalate, wani datti ne da ake fitarwa ta fitsari.
Matsalar ita ce, oxalate idan tayi yawa a jiki zai iya haɗuwa da calcium a fitsari, inda za su koma duwatsun ƙoda (kidney stones).
Wadannan duwatsu za su iya makalewa a ƙoda ko hanyoyin fitsari, sai su dinga jawo ciwo mai tsanani, da kuma amai, da ciwon ciki.
Ka yi tunanin hanyoyin fitsari kamar bututun ruwa. Idan waɗannan duwatsu s**a makale a cikin bututun, za su hana fitar fitsari yadda ya kamata. Wannan na iya kawo matsanancin ciwo har a bukaci aje asibiti.
To, Shawarar da masana s**a bayar ita ce kada a wuce shan 2000mg a rana. Shan fiye da haka na iya ƙara haɗarin samun duwatsun ƙoda. Wasu mutane kuma su fi kowa saurin kamuwa da wannan matsala, don haka yana da muhimmanci a tattauna da likita kafin a fara shan kari (supplements).
Abin farin ciki shine zaka iya ci gaba da cin abinci masu wadatar Vitamin C a jiki kamar lemu, strawberries, da tattasai ba tare da wata matsala ba. Wadannan abinci na da kyau kuma suna daga cikin abinci masu gina jiki.
Sai dai a rage shan supplement Idan ba likita ne ya rubuta mana ba, kuma a nemi shawarar likita idan ana da wata damuwa.
A ƙarshe, duk da cewa Vitamin C yana da amfani ga jikin dan adam, shan sa fiye da kima na iya ƙara haɗarin duwatsun ƙoda.
Lafiya fa aka ce jari ne.
Allah ya sa mu dace. Ameen