22/10/2025
SIRRIN KORAR ALJANU
,
,
,
Daga cikin muhimman bayanai dana samo akan hanyar da akebi a magance matsalolin jinnu musamman mata wanda suke mafarkai kodai namijin dare ko jarirai wanda ya tabbata akwai matsalar aljanu,
Rashin samun namiji tsayayye da zai auri mace duk yanda takeda farin jinin samari amma babu wanda zaiyi magar sure, hakan yanada alaka da aljanu ko kuma su hana mace ji a ranta tana bukatar namiji saidai ta rinka samun nishadi da namiji a mafarki, da dai sauran alamu dayake nuna akwai aljanu,
Atalaice akwai hayaki kala uku
Akwai turare kala uku
Sai mayuka suma kala uku
ƘARIN BAYANI akan hayaƙi shine anayinsa ne kafin a kwanta a ɗaki zaki iya saka hayakin saiki rufe bayan ɗan lokaci saiki bude ki shiga ki kwana kullum ake hakan,
ƘARIN BAYANI akan turare kuwa shafawa ake lokacin da akayi kwalliya ko kuma a fesa ajikin kaya musamman ƙayan bacci,
KARIN BAYANI akan mayi kuwa ana shafawa lokacin da za'a kwanta bacci mayi dayakeda wari ana iya haɗawa da wani turare me ƙamshi,
HAYAKI
kwanson tumfariya ana dakashi sama sama a hada da garin habbatussauda,
Baƙar ƙaya itama anayin garin sama sama,
Ganyen magarya da ganyen zurman ayi garinsu kada suyi laushi,
TURARE
Oud
Sandalwood
Binta sudan
MAYUKAN
man gelo
Man habbatussauda
Man albanunaj,