28/12/2025
Let Go! Amma kafin Let Go din, shin ka san waɗannan abubuwan?
Kafin ka danna Apply ko ka jira gayyata daga Facebook, ka tsaya ka bawa kanka amsa ga waɗannan tambayoyi guda 10:
1. Shin kana amfani da Facebook Lite kawai?
Facebook Lite ba ya nuna dukkan warnings, monetization status, da alerts. A shawarce ka yi download din normal Facebook.
2. Shin account ko page ɗinka na da Community Standards ko Partner Monetization Violations ko babu?
3. Shin Page Recommendations ɗinka active ne, ko Facebook sun yi maka flag har s**a sanya ka Unrecommended?
4. Wane irin content kake niyyar dora wa page ɗinka?
I. Rubutu da hoto (Text & Photo)
II. Reels
III. Live
IV. Dogon bidiyo (Long video)
5. Shin ka fahimci dokokin Facebook gaba ɗaya?
a. Community Standards
b. Partner Monetization Policies
c. Shin ka san ma’anar:
d. Re-used content
e. Repetitious content
f. Copyrighted content?
6. Shin ka san banbanci tsakanin:
I. Legal Name (sunan da ke a katin shaida/bank)
II. Profile Name (sunan Facebook ɗinka)?
7. Idan page ne da kai, shin kowanne admin clean ne?
I. Tsoffin admins da s**a yi violations na iya kawo maka cikas
II. Facebook yana kallon duk abin da aka taɓa haɗawa da page, ba yau kawai ba
8. Shin page ɗinka ya kai lokacin balaga (age & trust)?
Kana posting akai-akai ko ya zama dormant? A kalla ana so account/page ya kai wata uku active kafin su gayyace ka.
9. Shin kana yawan canja settings na page ɗinka?
Yawan canja admin, payout, ko unlinking/linking Instagram. Yawan irin wannan canje-canje akai-akai na iya sa Facebook kin amincewa dakai.
10. Shin ka san cewa Facebook Monetization har yanzu yana cikin Beta (gwaji)?
Wannan na nufin ba kowane account ko page Facebook suke gayyata ba, ko da ya cika sharudda.
Amma tsaftataccen account, bin dokoki, da hakuri suna ƙara yawan damar samun gayyata.
Tunda ka karanta har na goma fada mana Abubuwan daka sani cikin wadannan da Abubuwan da kake neman karin bayani akai. A karshe nima nace Let Go!
Karatuttukan Malaman Musulunci
Suleiman Nura Sa'idu ✍️