04/11/2021
Amfanin kukan miya ajikin dan Adam, kuka na taka muhimmiyar rawa wajen kiwon lafiya da warkar da cututtuka, baya ga inganta lafiya da take matukar mutum ya na amfani da ita akai-akai.
Yanzu dai ba tare da bata lokaci ba, ga amfanin kuka ga lafiyar dan-adam:
1. Kuka ta na maganin gudawa; Ba shakka wannan mujarrabi ne. Idan mutum ya na fama da gudawa, sai ya sami sassaken kuka ya wanke sannan ya jika ya ke sha, da sannu gudawar za ta tsaya.
2. Kuka na maganin guba; Idan mutum ya sha guba bisa tsautsayi, sai ya samu garin kuka ya hada da zuma ya sha babban cokali daya to zai hana gubar da aka sha tasiri a jikinsa.
3. Kuka ta na gina jikin dan-adam; wani bincike da masana kiwon lafiya su ka gudanar ya nuna cewa, ganye kuka na sahun gaba a nau'ikan ganyaye da ke kunshe da sanadarai ma su gina jiki cikin sauri. Saboda haka yawan amfani da kuka na taimakawa wajen gina jiki.
4. Ganyen kuka na maganin tari da kuma yawan taruwar majina a kirjin mutum.
5. Bincike ya gano cewa, ganyen kuka na rage yawan zufa/gumi kwatankwacin yadda wasu turarukan zamani ke yi.
6. Ana amfani da ganyen kuka domin maganin gajiya.
7. Ana amfani da ganyen kuka wajen maganin tsutsar ciki.
8. Matan aure za su iya amfani da garin kuka don karin ni'ima, duk uwar-gida ko amaryar da ke son samun karin ni'ima sai ki daka kuka ta yi laushi sosai sannan ki tankade daga nan sai ki samu madara peak milk ta ruwa ki hada ki dama ki ke sha.
Fadakarwa: Idan ana son a samu tasirin ganyen kuka sosai, ya na da kyau a shanya ganyen a inuwa har ya bushe, don kuwa masana kiwon lafiya sun yi gargadin cewa, shanya ganyen kuka a rana kamar yadda mutane su ka saba, na rage ma sa sanadarai ma su yawa, har wasu na ganin shanya ganyen kukar a rana na iya haddasa yin hasarar akalla kashi 50 cikin dari na sandaran da ya ke kunshe da su.