28/06/2025
CIWON QODA DA BAYANI A KAN CIWON KODA.
_Manufar Mu A Kullum Itace Wayar DA Kan Al'umma, da bada taimako akan konwace irin matsla ta raywua Bisa koyarwa ta addinin musulunci ✆ WhatsApp_ _☏+2348068203568.
✍🏽✍🏽✍🏽
*ادم علي عبد الله*
_Adam Aliyu Abdallah Gwani (likita)_
```Kira Ko WhatsApp```
🤳 08068203568 🤳
Allah Madaukakin Sarki ya halicci dan-adam da Qoda guda biyu✌🏻 a jikin kowane mutum, ta hagu da ta dama, wadanda ke da mazauni a kwibi ko gefen ciki karkashin hakarkari ta baya (retroperitoneals).
Daga jikinsu akwai wata magudanar fitsari da ake kira (ureter) da ta sauko ta hadu da tantanin tara fitsari dake mara wato (bladder) a turance k**ar yadda kuke gani a daya daga cikin hotunan da na sa akasa. Toh ta wannan magudanar fitsari kan gangaro daga koda ya taru a mara kafin mutum yayi fitsari ta mafitsara (urethra).
Qoda ita ke tace komi a jika daga ciki hadda fitsari, kuma ita ke sashi toh daga kan wannan magudanar fitsarin zuwa mafitsara, duk ciwon daya faru a wannan waje kan iya hawa ya taba koda.😭
koda na aiki a matsayin matatar jinin da ya kwaso kayan abinci🍝🍛 da ruwa🥃 ko na magani💊🍵, ya bi ta cikinta don a tace a samar da fitsari.
Fitsari kenan yana dauke da ruwa da wasu sinadarai da jiki baya bukata wanda yawancinsu masu guba ne k**ar gubar ammonia. Idan Qoda bata da lafiya, ruwan da ya k**ata a fitar mai dauke da wannan guba kan taru a jiki wanda akan gani a matsayin kumburin jiki (fuska da kafa da hannuwa da fari kafin daga bisani ya bi duk jiki gaba daya). 🙅🏻♂️🙅🏻♀️
Kumburin yana da dan bambanci da kumburin ciwon zuciya💓 dana ciwon hanta.
Bayan tace jini, koda tana sarrafa sinadaran bitaman na rukunin D da erythropoietin maisa jiki ya kera jajayen ‘ya’yan halittu na jini.
Idan koda na da ciwo mai tsanani ba ta iya samar da wadannan sinadari wanda hakan kan sa jini ya yi karanci a jikin mai ciwon koda, ko karancin sinadarin bitamin D.
A lokuta da dama koda za ta iya samun ciwo kuma ta farfado ba tare da anga alamu ba. Idan har aka fara ganin alamu na kumburin jiki da rashin jini a jiki to sai an yi da gaske kafin a shawo kan ciwon, wanda da yawa kuma maganin shi ne dashen wata kodar ta daban ko wanke jini da na’ura mai aiki k**ar kodar da ake kira dialysis machine (A Ilimi Na Likitancin Zamani fa Kenan)👨🏻⚕️👩🏻⚕️
Wannan cigaba na dashen koda ko wanke jini da na’ura, a yanzu ana iya yinsa a wannan kasar, sai dai dan karen tsada. Shi yasa yake da kyau a san abubuwan da ke kawo ciwon koda ko a dauki matakan kariya.
Wani batu mai kwantar da hankali game da koda shi ne aikin da koda biyu suke yi, guda daya ma za ta iya yi ba tare da wata matsala ba🤷🏻♂️🤷🏻♀️ Don haka ne ma ake ganin wadanda aka ciri daya daga cikin kodarsu aka dasa wa wani kan yi rayuwarsu k**ar kowa.🤷🏻♂️🤷🏻♀️
ABUBUWAN DA KE HADDASA CIWON QODA
Abubuwan da suke kawo ciwon koda suna da yawa, kuma hawan jini da ciwon suga wadanda aka sha bayani a kansu sune kan gaba wajen sanadi. Sai shan magunguna ba bisa kaida ba musamman ga mata👩🏻 da ke shan magungunan ciwon mara kala kala💊💊💊 yayin period, Shan barasa🍾🥃, karancin shan ruwa, yawan cin nama🍗🍖, yawan shan gishiri, yawan cin abubuwa masu kitse da Sauransu.
SAURAN SUNE :
Toshewar mafitsara da kwayoyin cuta.
Ciwon koda wanda toshewar mafitsara kan jawo Akwai cututtukan da kan toshe wasu daga cikin sassa na mafitsara (tun daga bakin kodar har zuwa wurin fitar fitsarin).
Idan hakan ta faru, maimakon fitsari ya zirare, sai ya taru ya kumbura wurin da abin ya faru, kaana yayi sama ya taru a kodar, ita ma ta kumbura, yadda idan ba a dauki mataki ba,
takan mutu gaba daya cikin kankanin lokaci. 😭
Amma da zarar an kawar da abin da ya toshe mafitsarar cikin sauri, sai kodar ta dawo aiki k**ar ba abin da ya taba ta.
Idan toshewar saman tantanin fitsari ce, akan ga bangaren koda guda ne ke kamuwa kuma mutum zai iya kamuwa har koda ta tabu bai sani ba🤷🏻♂️🤷🏻♀️. Amma idan daga kan tantanin zuwa
kasa aka samu toshewar, kusan duka koda biyun za su iya harbuwa.🙅🏻♂️🙅🏻♀️
Irin cututtukan da kan toshe mafitsara Matsaloli irinsu tsakuwa da kari ko tsuro na tantanin fitsari, da kari na bakin mahaifa da kumburin prostate (a wasu maza👨🏻👨🏻🦱🧔🏻
wadanda s**a zarta shekaru hamsin)👴🏻 da sauran irin wadannan cututtuka masu alamu, duk kusan iri daya, kan kawo cikas ga kwaranyewar fitsari yadda ya k**ata, wanda hakan kan taba lafiyar koda.
ALAMOMIN CIWON KODAR
Idan saman tantanin mara na fitsari ciwon yake; akan samu Ciwon kwi6in ciki, daga lokaci zuwa lokaci, Wani zubin harda yunkurin amai, ko ma aman🗣️. Irin wannan tsakuwa ce ta fi kawo shi kuma ciwon kwi6in yafi tsanani, don har kwantar da mutum zai iya yi, mutum ya kasa katabus. Idan kuma daga mara ne zuwa kasa ciwon yake, za a ji ciwon mara maimakon na kwi6in ciki, ko a rika fitsarin jini da jin zafi da wahalar fitar fitsari, ko a ga fitsari na rabuwa biyu (a maza).🧔🏻👨🏻🦱👨🏻
- HANYOYIN KARE KAI💪🏻
1- Duk wanda aka taba samun a danginsa an cire wa wani tsakuwa a kodarsa ko a matsarmama (kidney stones), to shi ma yana cikin hadarin samun tsakuwa a koda, domin abin akwai gado. Akwai abinci kuma irin su alayyahu🌿 da jan nama🥩, wadanda s**an jawo saurin samun tsakuwa a koda, don haka wadannan mutane ya k**ata su nisance su amma da hujjar zasu maye gurbin abincin da wani irinsa, k**ar latas🥬🥦 da kifi. 🐠🐟🐬🐋
Akwai kuma yanayi na zafi da kan iya sa taruwar ita wannan tsakuwa, duka dai a irin wadannan mutane da kan iya samu. Don haka yawan shan ruwa lokutan zafi yakan kiyaye taruwar dattin da za su hadu su ba da tsakuwa.
2- Ga masu noman rani na fadama, ko na damina a gonar da ruwa kan taru, ba tare da sun sa takalmin ruwa ba, da masu wanka a ruwa🏊🏻♀️ maras tsabta k**ar kududdufi duk ya k**ata su san cewa akwai kwayayen ciwon tsargiya da kan iya shiga jikinsu su kawo kari a tantanin fitsari.
Saka takalman roba⛸️⛸️🧦 (takalmin ruwa) ga manoma don kariya daga kwayayen schistosoma zai iya kiyaye su. Su kuma masu wankan rafi ko kududdufi🏊🏻♀️🏊🏻♀️ sai dai su guji hakan, don kuwa su ma suna cikin hadarin kamuwa da wannan tsuro.
3- Duk wanda ya taba noman fadama inda ruwa kan kwanta, ba tare da takalmin ruwa 🧦ba, ko kuma ya taba yin wankan rafi, musamman idan mutum ya taba yin tsargiya ko fitsarin jini amma bai sha magani ba, to yana da kyau yaje asibiti🏥🚶🏻♂️ mafi kusa a gwada👨🏻⚕️👩🏻⚕️ fitsarinsa a kuma ba shi maganin kashe wadannan tsutsotsi masu kawo tsuro a mafitsara.
4- Duk namjin da ya taba yin ciwon sanyi, mai alamu na ganin farin ruwa k**ar kamu a karshen fitsari, bai je an ba shi magungunan da s**a dace ba, shi ma yana cikin hadarin kamuwa da toshewar mafitsara a nan gaba, don haka da zarar an ga irin wannan alamun ciwon sanyin ake daukar mataki kafin abin ya zama matsala.
5- Yana da kyau duk matar da ta kai shekaru arba’in🧕🏻 kuma ta rika zuwa asibiti akalla sau daya a shekara ana gwada ruwan bakin mahaifa wato pap smear don kiyaye kamuwa daga ciwon daji na bakin mahaifa.
6- Duk namijin da ya manyanta👴🏻, ya ba hamsin baya, kuma yake da wahalar fitar fitsari, ko jinkiri wajen fitsari, shi ma ya samawa kansa lafiya, ya ga likita.👨🏻⚕️👩🏻⚕️
7- Duk mai ciwon kwibin ciki, na bangare daya ko duk biyun kuma ciwon yaki-ci-ya-ki-cinyewa, to yaje yaga likita👨🏻⚕️👩🏻⚕️ ayi masa hotunan koda na d-ray wadanda kan iya nuna duk wata matsala a kodar k**ar tsakuwa sannan asan me ya k**ata aimasa.
Cibiyarmu ta tana dar muku da ingantattun Maganin ciwon koda wanda ake warkewa gaba daya da izinin allah cikin Wata Daya (1) Month
Ga masu bukata zaku iya tuntubarmu kai Tsaye ta WhatsApp ko Kira ta Lambarmu
👇👇
☎️08068203568☎️
_Manufar Mu A Kullum Itace Wayar DA Kan Al'umma, da bada taimako akan konwace irin matsla ta raywua Bisa koyarwa ta addinin musulunci ✆ WhatsApp_ _☏+2348068203568.
✍🏽✍🏽✍🏽
*ادم علي عبد الله*
_Adam Aliyu Abdallah Gwani (likita)_
```Kira Ko WhatsApp```
🤳 08068203568 🤳