Malamin Jinya

Malamin Jinya Wellbeing||Mental health

29/07/2025

Shaye bata maganin damuwa

Imrana Shuaibu Adam

22/07/2025

Mental health problems do not affect just one person they can destroy relationships, break family bonds, and even ruin love.

Just yesterday, I came across a video on Facebook where wife relatives were beating a man who was apparently their sister’s husband because he hit her or had been abusing her.

But let’s be honest: violence is never a solution. If someone finds it easy to raise their hands in anger, there’s usually something deeper going on in their mind.

The husband might be battling with stress or emotional issues, and because he doesn't know how to express or manage it, he ends up releasing that tension through violence on his wife.

When stress becomes too much, especially for men who don't know how to cope, it often turns into anger. Now, I am not saying we should excuse such behavior, not at all but when we understand the root of the problem, then we can start looking for how to fix it.

Some men are battling silent pain: pressure, frustration, disappointment. They won’t talk about it, but they act it out and sadly, their loved ones are the ones who suffer for it.

That’s why we need to start taking mental health seriously just like we take physical health seriously. If someone has a broken leg, we rush them to the hospital. But if someone is breaking down mentally, we look away or insult them. That needs to change.

Mental health is important. It is the foundation for peace, love, and understanding in homes and in society.

Imrana Shuaibu Adam


19/07/2025

Mental illness ba Nakasa bane.


17/07/2025

Your mental health Matters..

Imrana Shuaibu Adam



03/06/2025

Diabetes (Ciwon sugar)

Ciwon sugar na daga cikin ciwokan da ke wahalar da mai ita, kuma tana da ka'idojin da in anbi za'a rage yawan tashin ta, da kuma complications din ta.

Ciwon sugar yana faruwa in jiki bai amfana da Sugar dake cikin jini da kuma rashin isheshshen insulin. Insulin shi ke sa jiki ya amfana da sugar ko kuma ya storing din shi (sugar). Ciwon sugar kala biyu ne zuwa hudu.

Akwai type1, type2, prediabetes, san nan akwai na masu ciki..
Alamomin ciwon sugar sun hada da:
🛑 Yawan fitsari akai akai.
🛑 Yawan jin yunwa sosai sosai kuma akai akai.
🛑 Yawan jin kishin ruwa akai akai.
🛑 Yawan gajiya
🛑 Rashin warkewan ciwo da wuri.
🛑 Yawan rama a type 1
🛑 Gani duru duru.

Abubuwan da ke iya(risk factors) kawo ciwon sugar
👉 Overweight , musanman masu tumbi.
👉 Rashi motsa jiki
👉 masu shekaru sama da 45years
👉 Iyaye ko yan'uwa Masu ciwon sugar. Dsss

In har a ka gwada mutum sau daya sau biyu aka tabbatar yana da ciwon sugar dole ya kula da abubuwa k**an haka:
✅ Diet = Dole ya rage cin abinci mai starch da carbohydrate sosai, Ya yawai ta cin Kayan ganye, fibre rich food, protein and healthy fat dss= ya nemi shawaran Likita da Dieticians don sanin abubuwan da ya k**ata yaci..
✅ Exercise yawan motsa jiki.
✅ Bin kaidar shan magani.
✅ Gwaji akai akai.. So samu mutum ya mallaki abun gwaji nashi.
✅ Barin Shan Cigari da Giya.

In aka kula sosai mutum zai rayu cikin aminci ba tare da yawan tashin hankali ba. Bin kaidojin yana da amfani sosai.... Ciwo neh da mutum zai rayu dashi (type1) iya rayuwarshi.. Saboda haka dole ka yarda da hakan kuma ka bi kaidojin don rayuwa cikin aminci.

Dole mu karekan mu iya yin mu. Da lafiya ake komai.. Lafiyar ita ce uwar jiki.. Kar ka yarda asa maka ruwa(iv fluid) ba tare da sanin sugar level dinka ba musan man yan shekara 45yrs yayi sama, Wasu suna da ciwon amman ba su sa ni ba. Sanya ruwan da ake yi gaba gadi ba tare da sanin Sugar level din su ba, ya kashe mutane da yawa.

Nr. Imrana Shuaibu Adam 2022


18/05/2025

Akwai wani irin nauyi da yake danne zuciya fiye da dutse. Wannan nauyin shi ake kira damuwa.

Ihu ko kuka ba sune kadai alaman mutum yana cikin damuwa ba. Wani lokaci tana nu na kai ne a matsayin rashin son magana, gajiya maras dalili, ko jin cewa komai babu amfani, abun da yake ya mutum nishadi ya dai na burge shi gaba daya.

Yawanci muna kallon irin waɗannan alamomin damuwan a matsayin karancin imani, ko rauni. Amma gaskiya ya k**ata mu sani. Damuwa cuta ce, k**ar ciwon zuciya ko hawan jini.

Idan kana fama da irin wannan nauyin a zuciyarka, ka sani ba kai kadai bane. Kuma hakan ba yana nufin kai mai rauni bane yana nufin kana buƙatar kulawa. Kar kayi saurin illanta kanka don kana jin duniyar ba dadi, ka ne mi shawaran masana.

Allah ya kara mana lafiya. Amin

Imrana Shuaibu Adam


22/04/2025

A halin yanzu, saboda zafin rana da ake fama da shi, mutane da dama sun daina motsa jiki k**ar yadda s**a saba daman tafiya ce kawai motsa jikin da sukeyi. Amma wannan halin zama babu dan motsa jiki ko kadan yana iya jawo kullewar ciki da taurin bayan gida har mutum ya shiga toilet, ya ta nishi, sai ka ce zai haihu!

Ko da kana shan ruwa sosai, yana da amfani ka ɗan motsa jiki kadan ko da a ɗaki ne, ka zazzaga kadan. Haka kuma, ka tabbatar da cin abinci mai ganye, don samun isasshen fiber wanda ke taimakawa wajen sauƙin bayan gida.

Allah ya ƙara mana lafiya, ya sauƙaƙa zafin rana da wahalhalun da ke tattare da shi. Amin.

Malamin Jinya



A ana shan ruwa kadan-kadan, sau da yawa a rana. Kada ka bar jiki ya bushe, kuma kada ka wuce gona da iri wurin shan ruw...
18/04/2025

A ana shan ruwa kadan-kadan, sau da yawa a rana. Kada ka bar jiki ya bushe, kuma kada ka wuce gona da iri wurin shan ruwan. Ruwa yana da amfani, amma yawan shan sa, na iya kawo matsala a jiki. A kalla dai ka sha ruwa da baiyi kasa da kofi takwas a rana, musanman in ana zafi sosai.

Ka saurari jikinka. kana fara jin kishi ka sha ruwa.
fitsari yayi kala sosai, ka sha ruwa.
Bakin ka ya bushe, ka sha ruwa.
Ana rana kana ta zufa, to ka sha ruwa, kuma ka ci abinci.
Allah ya kara mana Lafiya. Amin.

Malamin Jinya.

26/03/2025

Akwai mutane da Allah Ya yi wa ni’ima ta kiba, amma suna so dole sai sun rame, su dawo slim ko ta halin kaka. Ana samun irin su a cikin mata da maza, amma sun fi yawa a cikin mata. A wani bangaren kuma, akwai waɗanda ba su da halittar kiba, amma sai su dage cewa dole sai sun yi kiba, ko da kuwa hakan zai iya cutar da lafiyarsu.

Tabbas, akwai kiba da take iya zama illa ga mai ita, haka kuma akwai ramewa da take iya zama matsala. Sai dai babbar matsalar ita ce mutum ya yanke shawarar rage kiba ko ƙara kiba cikin gaggawa, ba tare da bin hanyoyin da s**a dace ba.

Da yawa daga cikin waɗanda ke son canza jikin su cikin gaggawa suna faɗa shan magunguna da za su iya haddasa illa mai tsanani ga lafiyarsu. Wasu daga cikin waɗannan magunguna:

Suna karya garkuwar jiki, suna sa mutum ya fi kamuwa da cututtuka.

Suna iya haddasa lalacewar gabobin jiki, k**ar hanta da koda.

Wasu daga cikinsu na iya haddasa cututtuka masu tsanani k**ar kansa (cancer).

Wasu suna kawo matsaloli ga tsarin hormones na jiki, wanda zai iya haddasa ƙarin damuwa da matsaloli masu yawa.

Kafin kayi wani yunkuri na rage ko ƙara kiba, yana da kyau ka nemi shawarar likita ko kwararren mai ba da shawara kan lafiyar jiki ko Nutritionist.

Ka Tuna! Lafiyarka ita ce babban jarinka, kar ka cutar da ita domin cimma burin da za ka iya samu ta hanyoyin da s**a fi dacewa!

Imrana Shuaibu Adam


23/03/2025

Idan har ciwon Ulsa ɗinka bai lafa ba yayin azumi, to akwai abubuwa biyu da za ka duba:

Ko dai asali chronic ne ko ya zama severe kuma yana buƙatar kulawa ta musamman.

Ko matsalar daga abinci ne – Idan ba chronic bane, to wataƙila abincin da kake ci a sahur da buda-baki ne ke ƙara dagula lamarin.

Yadda Za Ka Rage Matsalar Yayin Azumi:
🔹 A lokacin Sahur Ka ci abinci mai ɗaukar lokaci kafin narkewa k**ar oatmeal, dabino, da dan vegetable a abinci. A Guji kayan yaji da acidic foods.

🔹 Bayan Shan Ruwa a Buda-baki – Kada ka fara da abubuwa masu nauyi ko mai yawa, ka sha ruwa kadan sannan ka fara da abinci mai saukin narkewa k**ar dabino da shayi.

🔹 Guji shan ruwan sanyi sosai – Domin yana iya sa ciki ya kumbura kuma ya tada ciwo.

🔹 Rage shan shayi da caffeine – Domin na iya ƙara yawan acid a cikin ciki.

Allah ya kara mana lafiya. Amin

Gaskiyar Abin Da Ya Kamata Ka Sani Akan Dangantakar Azumi da UlcerAna yawan jin maganar cewa azumi yana haddasa ulcer, a...
04/03/2025

Gaskiyar Abin Da Ya Kamata Ka Sani Akan Dangantakar Azumi da Ulcer

Ana yawan jin maganar cewa azumi yana haddasa ulcer, amma shin ka san cewa yana iya taimakawa wajen warkar da ita ma?

Yawancin mutane da ke fama da ulcer suna jin tsoron yin azumi saboda suna tunanin rashin cin abinci na tsawon lokaci zai kara dagula matsalar. Amma bincike ya nuna cewa azumi na iya rage alamomin ulcer, har ma ya taimaka wajen gyaran bangon ciki.

A cikin kwanakin azumi, ciki yana samun damar hutawa daga ci gaba da aiki don narkar da abinci, wanda hakan yana taimakawa wajen rage yawan acid a ciki. Idan mutum yana ci akai-akai, jiki yana fitar da acid don narkar da abinci, amma idan an dan dakata da ci, acid din yana raguwa, yana hana shi fama gyanbon bangon ciki.

Bincike ma ya nuna cewa azumi yana kara yawan mucin, wani abu mai k**a da gel da ke kare ciki daga acid mai yawa.

Idan kana fama da ulcer kuma kana azumi, akwai abubuwa da za ka yi don gujewa matsala. Kada ka fara cin abinci mai nauyi ko mai yaji a Sahur da Iftar, ka fara buda baki da dabino da ruwa k**ar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar.

Hakanan, guji shan shayi ko coffee mai caffein da zarar ka tashi daga barci, saboda yana iya kara yawan acid. Abu mafi muhimmanci shi ne ka sha ruwa mai yawa daga Iftar zuwa Sahur domin rage hadarin bushewar jiki da yawan acid a ciki.

Idan ulcer dinka yana da tsanani sosai, yana da kyau ka tuntuɓi likita kafin ka fara azumi. Amma idan yana matsakaici, zaka iya yin azumi ba tare da wahala ba idan ka bi ka’idojin cin abinci mai kyau.

Kana da ulcer kuma kana yin azumi? Ta yaya kake shawo kan matsalar? Ka fada mana ra’ayinka domin wasu su amfana

Imrana Shuaibu Adam





photo: Hermina Hospital.

02/03/2025

Barci ba kawai hutawa ba ne, idan ana bin sunnah, yana da fa’idodi masu yawa ga lafiyar jiki da tunani. Yin barci da wuri da tashi da asuba yana daidaita hormones, yana rage damuwa, kuma yana kara kuzari da tsare-tsaren rana.

Annabi (SAW) ya koyar da kwanciya da hannun dama, wanda kimiyya ta tabbatar yana inganta numfashi da narkewar abinci. Wannan matsayi na kwanciya yana rage ciwon ciki da heartburn, yana ba jiki damar hutawa cikin nutsuwa.

Yin addu’a kafin barci yana rage damuwa da kara lafiyar kwakwalwa, yana taimakawa wajen samun barci mai kyau. Mutanen da ke yin addu’a suna da ƙarancin stress da bacin rai fiye da waɗanda ba sa yin hakan. Hakanan, cin abinci mai nauyi kafin barci na iya hana kwakwalwa samun isasshen hutu, yana haddasa gajiya da rashin kuzari da safe.

Qailulah (barci na rana) yana da muhimmanci k**ar yadda Annabi (SAW) ya karfafa yin sa kafin Azahar. Yin bacci na mintuna 20-30 yana rage gajiya da karfafa kwakwalwa. Mutanen da ke yin irin wannan barci suna da kyakkyawar kwakwalwa fiye da waɗanda ba sa yi.

Shin ka saba bin wadannan sunnonin barci? Wanne zaka fara gwadawa yanzu?

Allah ya kara mana Lafiya. Ya Karbi Ibadunmu. Amin.

Imrana Shuaibu Adam




Address

Bauchi

Opening Hours

Monday 15:00 - 20:00
Tuesday 15:00 - 20:00
Wednesday 15:00 - 20:00
Thursday 15:00 - 20:00
Friday 15:00 - 20:00
Saturday 07:00 - 21:00
Sunday 07:00 - 21:00

Telephone

+2348135396823

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Malamin Jinya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Malamin Jinya:

Share