Makarantar kula al'amuran yanmata da zaurawa

Makarantar  kula al'amuran yanmata da zaurawa Muna koyar da zaman take war aure
Muna hada Aure

ABUBUWA DA YAKE KAWO ZAWARCI.1. Mutuwar miji: Idan miji ya rasu, matar na iya zama bazawara.2. Rabuwa (saki): Matsalolin...
23/12/2024

ABUBUWA DA YAKE KAWO ZAWARCI.

1. Mutuwar miji: Idan miji ya rasu, matar na iya zama bazawara.

2. Rabuwa (saki): Matsalolin da ke haifar da rabuwa tsakanin ma’aurata, kamar rashin jituwa, cin amana, ko matsalolin zamantakewa, na iya kai wa ga zawarci.

3. Rashin fahimta da shige-shige: Matsaloli da ke tattare da rashin fahimtar juna ko shiga hurumin juna na iya haifar da rikici wanda zai kai ga saki.

4. Matsalolin tattalin arziki: Rashin kudi ko matsalolin da s**a shafi arziki na iya zama babban dalilin rabuwa a aure.

5. Matsalolin dangi: Idan akwai tsangwama daga iyaye ko dangin ma’aurata, wannan na iya dagula zaman aure, musamman idan ba a warware matsalolin cikin lumana.

6. Rashin biyayya ko cin amana: Idan daya daga cikin ma’auratan ya kasance mara biyayya ga daya ko yana cin amana, wannan na iya kawo karshen aure.

7. Rashin hakuri da juriya: Idan ba a iya jure matsalolin rayuwa ko rashin fahimtar juna, aure na iya fuskantar kalubale wanda zai kai ga zawarci.

8. Matsalolin lafiya: Wasu matsalolin lafiya na iya sa aure ya samu matsala, musamman idan daya daga cikin ma’auratan ba ya iya jurewa.

9. Saurin yin aure ba tare da shirye-shirye ba: Wasu matasa kan yi aure ba tare da cikakken fahimta da shiri ba, wanda hakan na iya jawo matsaloli.

10. Sauyin halaye da sha’awa: Idan halaye ko burin daya daga cikin ma’auratan s**a canza sosai bayan aure, wannan na iya haifar da rashin fahimtar juna.

Mahimmanci ne a lura cewa zawarci ba yana nufin gazawa ba ne. A wasu lokuta, yana zama hanya mafi kyau domin samun kwanciyar hankali da rayuwa mai kyau.

Dan Daudun Najeriya Bobrisky ya magatu akan jinin Haida.
08/12/2024

Dan Daudun Najeriya Bobrisky ya magatu akan jinin Haida.

20/09/2024
Da za mu fahimci wannan, 👇👇Da mun sama wa zukatanmu hutu da nutsuwa.Don kana son mutum, ba sharaɗi ba ne, ko tilas sai (...
11/07/2024

Da za mu fahimci wannan, 👇👇
Da mun sama wa zukatanmu hutu da nutsuwa.

Don kana son mutum, ba sharaɗi ba ne, ko tilas sai (shi ma) ya so ka ba, ya dawo maka da irin soyayyar da kake yi masa (kwabo da kwabo).

BA SHARAƊI BA NE! Don ka yi duk wata dagewa da nuna bajinta don wani ya so ka, shi kuma ya juya maka baya, daidai ne da kai ma wani ya so ka ka juya masa baya saboda kana son wanda zuciyarka ta zaɓa.

Ba laifi ba ne, don ka so wani, shi kuma ya ƙi ka. Ba laifi ba ne, don wani ya so ka, kai kuma ka ƙi shi. Haka rayuwa take, wani lokacin akan yi dace, sashe ya so sashe da gaske, wani lokacin kuma ɗaya sashe ya ƙi ɗayan sashe (one sided love), takan iya kasance wa ga kowaye, ba mace, ba namiji; jahili ko mai ilimi, talaka ko mai dukiya da mulki.

Kuskure shi ne, ka san ba a sonka, amma ka nace (kai dole sai an so ka, an yi maka yadda kake so), za ka sa zuciyarka cikin rashin hutu. Laifin shi ne, ka san ba ka son mutum, ka rataye shi da igiyar zato, cikin aminci da girmamawa ka sallami zuciyar da ke son ka da gaske idan ba ka ra'ayi.

Kada ka cuci kowa,
Kada ka yarda a cuce ka,
Kuma kada ka cutar da kanka.

Don wani ba ya son ka, ba ya nufin ba ka kai a so ka ba ne, ko ba ka da ilimin da za a so ka, ko dukiya, ko kyau, ko nasaba, a'a; shi son gaske ba ruwansa da wannan. Wataƙila wanda bai kai ka 'qualities' ba, a so shi, kai kuma a ƙi ka. Ko kai kuma ka so mai 'qualities' ɗin da ba kai rabin na wanda kake ƙi ba.

Soyayya jarrabawa ce!
Idan an dace, ka ji daɗi, ka more,
Idan ba a dace ba, ka rasa hutun zuciya.

Ka yi da wanda yake yi da kai,
Ka bar wanda ba ya yi da kai, ka tsira da mutunci.

Ka bar wa Allah zaɓi, matuƙar addu'ar da kake yi da gaske neman zaɓin Allah kake yi, ba wai neman zaɓin son ranka ba. Hutun zuciya ya tabbata ga wanda ya fahimci wannan saƙon.

Imam Ash Shafi'i na cewa:

فما كل من تهواه يهواك قلبه
ولا كل من صافيته لك قد صفا

إذا لم يكن صفو الوداد طبيعة
فلا خير في ود يجيء تكلف

14/02/2024

Mata da yawa na kallon zawarci yanci ne, amma ba yanci ba ne, fitina da yake tattare shi yafi alkhairin sa.

Sannu da zuwa wannan shafi.
16/11/2023

Sannu da zuwa wannan shafi.

Address

Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Makarantar kula al'amuran yanmata da zaurawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share