01/05/2019
BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA KUNGIYOYIN KARE HAKKIN MUSULMIN NIGERIA
Daga Datti Assalafiy
Za muyi amfani da wannan damar wajen ankarar da dukkan kungiyoyin da suke kare hakkin musulmin Nigeria game da abinda yake faruwa a jami'ar Jos, musamman a asibitin koyarwa na jami'ar (Jos University Teaching Hospital) bisa yadda mahukuntan jami'ar suke tauyewa mata musulmai hakkinsu na saka hijabi
Da farko, hukumar kula da aikin renon jinya da unguwar zoma ta Kasar Nigeria (The Nursing and Midwifery Council of Nigeria) ta amincewa dukkan matan musulmai da kiristocin Nigeria su saka Hijabi gajere wanda zai sauka iya kan kafadunsu a bakin aikinsu, amma har zuwa yanzu mahukuntan asibitin koyarwa na jami'ar Jos bangaren kula da jinya da unguwar zoma (Nursing and Midwifery) suna cigaba da tabbatar da haramcin saka gajeren Hijabin
Mata musulmai ma'aikatan asibitin koyarwa na Jos ana tilasta musu cewa su zabi saka hijabi ko aikinsu, wasu dole s**a hakura da saka hijabin suna fitowa haka tsirara kamar matan arna, wasu kuma ala tilas sun hakura da aikin domin ba zasu iya cire Hijabi ba
Dalibai mata musulmai da suke koyon aikin kula da jinya da unguwar zoma suma ana tilasta musu dole sai sun cire Hijabi, ance sai dai suyi amfani da gashin doki ko gashin kansu su rufe kafadu da kirjinsu, amma ba wai su saka Hijabi ba an haramta musu, sati guda kenan da fara wannan haramci
Wannan hukunci da aka zartarwa mata musulmai a asibitin koyarwa na Jos tsagwaron nuna banbancin addini ne, kuma cin zarafin musulunci da musulmai ne, uwa uba asibitin ba mallakin jihar Pilato bane, mallakin gwamnatin tarayya ne, tsarin dokar Kasar Nigeria ya bawa duk wani 'dan kasa dama da 'yanci yayi addininsa ba tare da tsangwama ba, saka hijabi a gurin matan musulmai addini ne kuma ibada wanda yake wajib
Muna kira ga dukkan wanda abin ya shafa a Nigeria suji halin da mata musulmai suke ciki a jami'ar koyarwa na Jos, lallai a bawa mata musulmai hakkinsu, sannan ayi gaggawan hukunta shugaban jami'ar bisa cin zarafi da tauye hakkin mata musulmai
Don Allah jama'ar musulmi duk wanda yaga wannan sanarwa ya daure ya yada sakon ya isa inda muke fata
Muna rokon Allah Ya kwata mata musulmai 'yancin su a jami'ar koyarwa na Jos Amin