
18/03/2025
SANARWAR GAYYATA ZUWA WAJEN KADDAMARDA TALLAFI ZUWA GA MARAYU!
Shugaban Kwamitin Marayu na Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah na Garin Gwandu Sheikh (Imam) Muhammad Yabani Yana farin cikin gayyatar Yan uwa musulmi zuwa wajen kaddamar da rabon tallafin abinci da kayan sallah ga marayu da Cibiyar taimakon marayu ta Garin Gwandu ke gabatarwa a duk Shekara
Insha Allahu wannan shekarar za'a kaddamarda rabon tallafin ranar Lahadi 23 Ramadan, 1446 wanda yayi daidai da 23 March, 2025 a Masallacin Juma'a na Jibwis dake shiyar Yar Gada a Garin Gwandu
Kuma har yanzu kofa a bude ta ke ga duk wanda zai bada gudummuwar abinci ko sutura wadda za'a iya kai wa kai tsaye a Masallacin Juma'a na Jibwis na Garin Gwandu Ko kuma sanya gudummuwa ta wannan asusu kaman haka:
Banki: First Bank
Lambar Asusu: 2029657649
Sunan Asusu: kwamitin tallafawa marayu na Jibwis Gwandu
Domin karin bayani za'a iya kiran wadannan lambobi kamar haka 07035314017 08146475378 08069045101
Allah yabada ikon halarta yasa a gabartarda taro lafiya akare lafiya Allah ta'ala yasaka kowa da mafificin alhairinsa
JIBWIS GWANDU
18 Ramadan, 1446
18 March, 2025