Golden Tree Medicare and physio clinic

Golden Tree Medicare and physio clinic For students and researchers

08/01/2026

Rechargeable EMS/TENS

Knee Support
25/08/2024

Knee Support

Ko me ke kawo shanyewar ƙafa ga uwa bayan haihuwa?Daga cikin matsalolin da iyaye mata ke fuskanta yayin naƙuda wadda ke ...
21/06/2022

Ko me ke kawo shanyewar ƙafa ga uwa bayan haihuwa?

Daga cikin matsalolin da iyaye mata ke fuskanta yayin naƙuda wadda ke hana su tafiya bayan haihuwa saboda rauni ko shanyewar ƙafafu akwai matsalar nan da ake kira da "Maternal Obstetric Palsy" a turancin likita. Wannan matsala na faruwa ne yayin naƙuda a lokacin da kan jariri ya sakko zuwa ƙugun uwa. Tsawaitar naƙuda ko kuma tangarɗar naƙudar kan sa kan jariri ya danne gungun jijiyoyin laka da s**a sakko zuwa ƙugu da ƙafafu da ake cewa "lumbosacral plexus" a yaren likita.

Duk da cewa wannan matsala tana iya shafar ƙafafu biyu a lokaci guda, amma ta fi shafar ƙafa ɗaya.

Iyaye mata da suke da haɗarin samun wannan matsala sun haɗa da:

1] Gajeru; saboda ƙuncin ƙugu.

2] Naƙuda / haihuwar jaririn da kansa ya wuce matsakaicin girma, wato girman kan jaririn ya fi faɗin mafitar ƙugun.

3] Nawa ko tsawaitar naƙuda fiye da yadda aka saba gani.

4] Uwayen da s**a gaza haihuwa da kansu har sai da aka taimaka musu da maƙatar ungozoma domin zaƙulo kan jaririn, wato "forcep delivery" a turance.

5] Juyewa ko karkacewar jariri yayin naƙuda da sauransu.

Alamun larurar sun haɗa da:

Waɗansu alamun suna bayyana tun a lokacin naƙuda, a yayin da wasu kuma kan bayyana bayan haihuwa.

1] Ciwo daga cinya zuwa tafin sawu.

2] Rashin jin daɗi a fatar ƙafar; k**ar jin tafiyar kiyashi, jin dindiris, jin k**ar ana tsira allura, ko kuma jin k**ar jan wutar lantarki.

3] Shanyewar ko raunin kafafu da tafin sawu.

4] Ƙwacewar fitsari da/ko bahaya.

5] Matsalar saduwa da iyali, da dai sauransu.

Sai dai, sau da yawa a kan bar iyaye matan da s**a haihu a kwance saboda sun kasa tashi sak**akon rashin ƙwarin ƙafafunsu ba tare da an ɗauki matakan da s**a k**ata ba.



A yayin da mace ta haihu, sannan aka lura ta kasa taka ƙafafunta a tuntuɓi likitan fisiyo domin ɗaukar matakan da s**a k**ata.

Ƙwacewar Fitsari Ga MataƘwacewar fitsari matsala ce ruwan dare da ba a cika neman maganinta ba saboda kunya, tsoron tsan...
18/06/2022

Ƙwacewar Fitsari Ga Mata

Ƙwacewar fitsari matsala ce ruwan dare da ba a cika neman maganinta ba saboda kunya, tsoron tsangwama ko kuma zaton cewa ƙwacewar fitsarin wata sananniyar al'ada ce musamman ga mata yayin rainon ciki da bayan haihuwa.

Ƙwacewar fitsari matsala ce da ke barazana ga ibada, walwala, tsabtar jiki da kuma ingancin rayuwar masu fama da ita.

Matsalar ƙwacewar fitsari na shafar maza da mata sai dai ta fi shafar manyan mutane. Haka nan, matsalar ta fi shafar mata manya, inda take shafar kimanin mata kaso hamsin cikin ɗari (50%) da kuma maza kaso goma sha ɗaya cikin ɗari (11%). Sai dai kaso ashirin da biyar zuwa sittin da ɗaya cikin ɗari (25–61%) ne kawai na matan ke iya samun kulawa.

Daga cikin abubuwan da ke ƙara haɗarin gamuwa da ƙwacewar fitsari akwai:

1. Jinsi: jinsin mata sun fi maza samun matsalar.

2. Rainon / goyon jiki da haihuwa.

3. Doguwar / tangarɗar naƙuda.

4. Ƙiba

5. Matsanancin tari tsawon lokaci.

6. Raunata jijiyoyin laka na baya.

7. Shan taba sigari.

8. Tiyatar ƙugu / mafitsara, da sauransu.

Ƙwacewar fitsari yayin ayyukan yunƙuri k**ar ɗaga nauyi, dariya, tari, atishawa ko motsa jiki matsala ce da ke faruwa sak**akon raunin / rashin ƙwarin tsokokin da ke shimfiɗe a ƙasan ƙugu. Waɗannan tsokoki sune ke riƙe da maɗaurin jakar mafitsara. Saboda haka, raunin tsokokin zai riƙa haifar da ƙwacewar fitsari ba tare da sanin mutum ba. Irin wannan ƙwacewar fitsari ana kiran sa da 'Stress Urinary Incontinence' a turance.

Saboda haka, idan kina da ƙorafin ƙwacewar fitsari ba tare da saninki ba, musamman yayin da kika yunƙura domin zama, miƙewa, ɗaga kayan nauyi, dariya, tari ko atishawa to alama ce ta wannan matsala.

Kada ki bari kunya ko tsoron tsangwama su hana ki bayyana damuwarki. Tuntuɓi likitan fisiyo a yau don ɗora ki kan hanyar da za ki yi bankwana da matsalar ƙwacewar fitsari.

Motsa jiki na matukar kyautata rayuwarmu.Na ji wani likita na cewa, da akwai yadda zai yi ya dunkule alherin da ke cikin...
12/06/2022

Motsa jiki na matukar kyautata rayuwarmu.

Na ji wani likita na cewa, da akwai yadda zai yi ya dunkule alherin da ke cikin motsa jiki ya zama tablet wanda zai rike bayar da prescription ga kowa, da yayi.

Saboda ba karamin taimakawa lafiyarmu ta ke yi ba musamman lafiyar zuciya.

Sannin kowane, zuciya tsoka ce mai matukar muhimmanci; ita ke fara aiki kafin sauran gabobi kuma da ta tsaya, komai ya tsaya cak kenan.

Saboda ita ke samar da mak**ashin da duk kwayoyin halittar Dan Adam ke amfani da shi domin gudanar da muhimman ayyukan gabobin jiki.

Allah mai iko, Jikin dan’adam tattare ya ke da triliyoyin kwayoyin halitta a jikin dan’Adam wadanda duk sun dogara da zuciya domin samun mak**ashin aiki. Kuma cikin ikon Allah take samar da abin da suke bukata, a daidai lokacin da suke bukata.

Hakan na faruwa ne saboda wani tsari mai k**a da road network wato k**ar hanyoyin zirga-zirga da s**a hada garuruwan da ke nesa da na kusa. To haka jijiyoyin dan Adam suke kuma zuciya ce hedikwatan da ke aika masinjoji su je su dawo akan wadannan hanyoyi zuwa duka sassan jiki. Su kai mak**ashin aiki, su kuma dauko abubuwan da za a mayar wa zuciya domin ta tace daga jini.

To k**ar yanda ake son maintaining wato kula da hanyoyi domin dorewa, haka ake son yi wa wadannan hanyoyin. Kuma motsa jiki na taimakawa wajen karfafa wadannan jijjiyoyin, akasin haka kuma ke lalata su. Wasa-wasa har abubuwa su shigo su toshe hanyoyin har a samu jinkirin isar da mak**ashin aiki. Daga nan sai heart attack. Allah Ya tsare

Sau da yawa ba mu fara tunanin motsa jiki sai don rage kiba. Idan kuma baka da kibar, baka da bukatar yinsa. Big mistake.

Saboda haka idan kana son tsawaita rayuwarka (of course ba ka iya tsallake hukuncin Ubangiji), to ka rungumi motsa jiki ko ya ya ne.

Mafita Daga Ciwon Ƙugu Bayan Haihuwa.Daga cikin matsalolin da kan biyo bayan haihuwa akwai matsalar "buɗewar mahaɗar ƙug...
10/06/2022

Mafita Daga Ciwon Ƙugu Bayan Haihuwa.

Daga cikin matsalolin da kan biyo bayan haihuwa akwai matsalar "buɗewar mahaɗar ƙugu" wanda kan faru sak**akon buɗewar(yagewar) tantanai da ke riƙe da ƙasusuwan ƙugu yayin naƙuda wanda a ke cewa "Obstetric Diastasis P***c Symphysis" a turancin likita.

Ana tabbatar da samun matsalar "buɗewar mahaɗar ƙugu" yayin da aka sami buɗewar ɓangarori biyu na ƙasusuwan ƙugu a mahaɗarsu fiye da ƙima (=/>1cm), haɗi da ɓallewa ko tsinkewar tantanai da ke riƙe da mahaɗar ƙasusuwan.

Duk da cewa wannan matsala na ci wa matan da s**a haihu tuwo a ƙwarya, al'ada ta gudana cewa ciwon ƙugu ko kwankwaso wani abu ne da aka saba da shi, ko kuma al'adar masu haihuwa ce daman. Sai dai abin ba haka yake ba, domin akwai buƙatar duba wannan ƙorafi da waɗanda s**a haihu kan zo da shi. Domin bincike ya nuna cewa a duk haihuwa 385 akwai mace guda da kan sami wannan matsala. Sai dai kuma saboda ɓoye ƙorafin ciwon da mata kan yi, ana fargabar cewa adadin matan da kan gamu da matsalar suna da tarin yawa fiye da yadda binciken ya nuna.

Bugu da ƙari, kaso 45 cikin ɗari na masu juna biyu, da kuma kaso 25 cikin ɗari na matan da s**a haihu na da ƙorafin ɗaya daga cikin nau'o'in ciwon ƙugu.

Waɗanda ke da haɗarin samun buɗewar mahaɗar ƙugu yayin haihuwa sun haɗa da:

1. Haihuwar tagwaye ko fiye.

2. Juyewar ko kaikaicewar jariri yayin naƙuda.

3. Rashin daidaito tsakanin faɗin kan jariri da faɗin ƙugun uwa.

4. Matan da aka temaka wa da maƙatar ungozoma (obstetrical forceps) yayin haihuwa.

5. Matan da ke da larurar talewar tantanai fiye da ƙima.

6. Matan da s**a faɗa hannun ungozomomin da basu ƙware ba, da sauransu.

Alamomin "buɗewar mahaɗar ƙugu" sun haɗa da:

1. Ciwo a matsematsin cinyoyi, saman gaba, cinya, bayan ƙugu/baya,

2. Ciwo a ƙugu yayin da aka matse cinyoyi,

3. Ciwo da wahala yayin mirginawa/juyawa a gado,

4. Ciwo a ƙugu yayin tsaiwa, tafiya ko hawa bene,

5. Bauɗewar sawaye yayin tafiya, jan ƙafa, da dai sauransu.

Likitoci fisiyo na amfani da na'urorin rage raɗaɗin ciwo don magance matsanancin ciwon da masu wannan larura ke fama da shi, koya musu dabaru cikin ayyukan yau da gobe domin kauce wa jin ciwo ko ta'azzararsa, da kuma ɗora su kan keɓantaccen atisayen da zai ƙarfafa tsokokin ƙugu da ƙafafu.

Har ila yau, idan buɗewar mahaɗar ƙugun ta wuce ƙima ko kuma dukkan tantanai da ke riƙe da mahaɗar ƙugun sun raunata, wannan zai kai ga yin tiyata domin ɗinki ko haɗe mahaɗar.

Wannan ciwo ana warkewa sarai, musamman idan aka sami cikakkiyar kulawar likitocin fisiyo da sauran likitoci.

Daga ƙarshe, sau da yawa mata kan ɓoye wannan ciwo da zaton cewa wannan ciwon al'ada ne da kan zo duk bayan haihuwa. Sai dai ɓoye wannan ciwo da kuma barin sa ba tare da an magance shi ba na iya tsawaita ko kuma ya sake dawowa lokacin renon ciki na gaba.

Saboda haka sanar da likitocin da ke kula da ke irin ciwon ƙugu, ƙafafu, ko wahalar tafiya da k**e ciki bayan haihuwa domin neman ɗaukin likitan fisiyo.



***cSymphysis




Abubuwa Biyar Da Ka Iya Janyo Fashewar Faifan Ƙashin Gadon Baya.Da farko, ya k**ata a fahimci mene ne faifan ƙashin gado...
08/06/2022

Abubuwa Biyar Da Ka Iya Janyo Fashewar Faifan Ƙashin Gadon Baya.

Da farko, ya k**ata a fahimci mene ne faifan ƙashin gadon baya, sannan kuma mene ne aikinsa. Ƙashin gadon baya jigida ce da ta ƙunshi jerin ƙasusuwa har guda 33, tun daga ƙasan ƙoƙon kai har zuwa jelar jigidar inda ta ƙare a cikin ƙugu. A tsakanin kowane ƙashi da ƙashi akwai wannan faifai. Waɗanan fayafayai suna da ɗabi'ar roba ko ɗanko ne, wato suna iya lotsewa idan s**a ji nauyi sannan su miƙe idan nauyin ya gushe. Saboda haka ne ƙasusuwan gadon baya ke lanƙwashewa sannan su miƙe ba tare da wata tirjiya ba.

A duk lokacin da wani faifai ya fashe ko kuma ya yi bulli, zai danne laka ko kuma jijiyoyin laka. Hakan yana iya faruwa a wuya ko kuma a baya. A yanzu, za mu mai da hankali kan fashewa ko bullin faifai a ƙasan gadon baya. Saboda a nan ne matsalar ta fi faruwa.

Alamomin fashewa / bullin faifai sun haɗa da:

1. Ciwon ƙafafu: Idan faifai ya samu matsala a baya, bayan ciwon baya sannan kuma ciwon zai riƙa sauka zuwa tsokokin ɗuwawu, cinya, sangalali har zuwa tafin sawu.

2. Idan bullin faifai ya danne laka ko jijiyar laka za a ɗinga jin zogi, raɗaɗi, zafi, dindiris, k**ar shokin ɗin lantarki, k**ar tafiyar kiyashi ko kuma k**ar ana tsitstsira allura a ƙafar.

3. Rauni ko rashin ƙwari: Zuwa wani lokaci, ƙafafu za su fara samun rauni sannan kuma tafiya da sauran ayyukan yau da kullum su fara yin wahala.

Duk da cewa ingancin fayafayan yana raguwa da miƙawar shekaru. Akwai abubuwa biyar da ke ƙara haɗarin fashewa ko bullin fayafayan k**ar haka:

1. Ƙiba / teɓa: Ƙarin nauyin jiki na ƙara wa faifai nauyi da wahala.

2. Aiki / sana'a: Ayyukan sana'o'i da ke buƙatar aikin gangan jiki tuƙuru na iya janyo matsalar faifai. Maimaituwar ɗaga kayan nauyi, turawa ko janyo kayan nauyi duka na ƙara haɗarin samun matsalar faifai. Idan kana sha'awar motsa jiki ko atisaye domin gina ƙwanji, kasance ƙarƙashin kulawar likitan fisiyo domin kauce wa samun ciwon baya.

3. Shan taba sigari: Shan taba sigari na rage ingancin aikin faifan.

4. Tuƙi akai-akai: Tuƙi akai-akai tare jijjiga daga abin-hawan na iya yin lahani ga faifai.

5. Rashin motsa jiki: Rashin motsa jiki na iya rage ingancin aikin faifai.

Likitan fisiyo na amfani da ƙwarewa domin rage ciwon da kuma shawo kan matsalar daga tushe. Ci gaba da shan ƙwayoyin rage ciwo ba tare tuntubar likitan fisiyo ba na iya ta'azzara matsalar wanda hakan kuma na iya tilasta yin tiyatar baya daga ƙarshe.



Yanke Shakku Kan Sababin Karkacewar Baki KwatsamShanyewar ɓarin fuska larura ce da ke faruwa sak**akon sanyi ko shanyewa...
08/06/2022

Yanke Shakku Kan Sababin Karkacewar Baki Kwatsam

Shanyewar ɓarin fuska larura ce da ke faruwa sak**akon sanyi ko shanyewar jijiyar laka ta bakwai (7) da ta fito daga ƙwaƙwalwa zuwa tsokokin fuska.

Wannan jijiyar laka na iya samun matsala k**ar shaƙewa, dannewa, lahani daga harbin ƙwayoyin cuta ko kuma bugu daga waje a kan hanyarta daga ƙwaƙwalwa zuwa fuska domin kai saƙonni zuwa tsokokin ɓarin fuska, jakar yawu, jakar hawaye, tsinin harshe, da wata tsoka da ke dai-daita sauti da ke can cikin kunne, da dai sauransu. Idan ɗaya daga cikin waɗannan matsaloli ya faru, aikin jijiyar lakar zai yi sanyi ko rauni sai kuma ɓarin fuska ya shanye.

Yadda za a gane ɓarin da fuska ta shanye:

1) Karkacewar baki: wanda hakan zai sa wahalar rikewa ko zirarewar abinci ko abinsha daga baki.

2) Zubowar yawu ta ɓarin da bakin ya shanye.

3) Sakkowar gira da kuma yawan zubar hawaye.

4) Gaza ko wahalar rufe ido.

5) Gaza ko wahalar bayyana labarin zuciya a fuska, k**ar murmushi, fushi da sauransu.

6) Matsalar kasa ɗaga gira ko tattare fatar goshi.

7) Ƙaruwar ƙara ko sauti a kunnen ta ɓarin da fuskar ta shanye.

8) Rashin jin ɗanɗano a tsinin harshe, da sauransu.

Abubuwan da ka iya janyo shanyewar ɓarin fuska:

1) Shanyewar ɓarin jiki, wasu masu shanyewar ɓarin jiki kan zo da shanyewar ɓarin fuska.

2) Ciwon siga.

3) Fashewar jijiyar jini a cikin kai.

4) Ciwon kunne.

5) Matsananciyar mura.

6) Bugu/rauni a kai ko fuska.

7) Doguwar tafiya a kan abin hawa tare da iska mai karfi na bugun ɓarin fuska tsawon lokaci.

Wannan matsala ta shanyewar ɓarin fuska na ci wa masu fama da ita tuwo a ƙwarya, k**a daga wahalhalu wajen cin abinci ko shan abinsha, zubar hawaye ko yawu wanda ke sa su jin kunyar bayyana fuskarsu a cikin jama'a, wanda hakan kan sa su ƙaurace wa jama'a, ko kuma tilasta musu rufe fuskarsu domin gudun tsangwama.

Wannan jinya ta shanyewar ɓarin fuska ana warkewa sarai k**ar ba a yi ba. Don haka, idan kina / kana fama da wannan matsala tuntuɓi likitan fisiyo a asibiti mafi kusa da kai.

Likitan fisiyo na amfani da hanyoyin ƙwarewa domin yi wa jijiya laka da tsokokin ɓarin fuskar ƙaimi domin farfaɗo da aikinsu.




Address

Zaria Road Funtua
Funtua

Telephone

+2348137645792

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Golden Tree Medicare and physio clinic posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Golden Tree Medicare and physio clinic:

Share