Al—Ilaaj Herbal Clinic

Al—Ilaaj Herbal Clinic Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Al—Ilaaj Herbal Clinic, Medical and health, Behind Science Village Bypass Gombe, Gombe.

22/09/2024
CIWON CIKI MAI K**A DA SIHIRI Akoi wani nau'in CIWON CIKI MAI tsanani mai suna QULUNUL AJWAF,. Wanda tsanani sa ya kan t...
12/09/2024

CIWON CIKI MAI K**A DA SIHIRI
Akoi wani nau'in CIWON CIKI MAI tsanani mai suna QULUNUL AJWAF,. Wanda tsanani sa ya kan tayar da hankali sosai saboda da wassu dalilai k**ar haka;

1. Mutum yakan fita hayyacin sa saboda zafin ciwon cikin
2. Mutum ya kan yi birgima a kasa da dungure saboda WAHALAR CIWON cikin

CIWON CIKIN YA NA DA ALAMU K**AR HAKA;

1. Yawan tusa
2. A mafi yawan lokuta yana rike bangaren Ciki daya, Dama ko hagu.
3. Yawan shan Ruwa
4. zafin jikin
Irin tashin hankalin dake cikin JINYAR da yawa daga cikin mutane suke ganin cewa SIHIRI NE. Amma in an yi JINYAR SIHIRI Babu alama, lallai a goda jinyatar wannan mas'alar (QULUN AL AJWAF)

SANADIN CUTAR

Iskace take maqalewa a hanji na biyar na cikin mutum, a sanadiyyar toshewa ko murdewar hanjin. Alokacin da dabi'a tayi yunkurin fidda iskar sai ya haifar da MATSANANCIN CIWON CIKI saboda jijiyoyin sako dake sarkafe a hanji da sauran gabbai wadanda suke da alaqa da hanjin.

JINYAR CUTAR

1 kasan cewar iskace ta makale a hanji, don haka za a yi amfani da magunguna masu dabi'ar karya iska. k**ar su;
1. Citta mai yatsa
2. Aloe vera
3. kanamfari

A samu gari na daya daga cikin abubuwannan cikin karamin cokali sai a tafasa shi a zuba Zuma babban cokali 5 a dinga sha za a samu sauki da ikon Allahu.

Amma ga wadanda suke sana'ar magani za su iya amfani da JAWARISHU KAMUN ko dukkan jawarish mai dauke da sinadaran da muka ambata

ABIN LURA MAI AMFANI

Ga masu sana'ar jinya, wassu lokuta akan banban ce na sanyi ko zafin saboda alamu. MISALI; Wassu masana suna cewa in CIWON yafi yawa ta Dama masalar Harara ce. Amma ta hagu buruda ce. sai ayi qiyasi.
Allah muke roko ya bamu lafiya. Ameen.

SHEIKH BARR IBRAHIM TUKULMA
(IMAM MASALLACIN ABU HURAIRA BY PASS GOMBE)

RASHIN AURE NA HAIFAR DA CUTA MAI K**AR FARFADIYAMANIYYI a wassu lokuta ya kan canza ya koma guba a cikin jikin  mutum, ...
04/09/2024

RASHIN AURE NA HAIFAR DA CUTA MAI K**AR FARFADIYA
MANIYYI a wassu lokuta ya kan canza ya koma guba a cikin jikin mutum, musamman yan mata a lokacin da s**a bukaci aure kuma ba su samu ba.

Rikicewar maniyyin sai ya haifar da wata jinya mai suna 'IKHTINAQURRAHIM'. Hakan zai faru ne a sanadiyyar wani tiriri wanda zai taso daga mahaifa zuwa kwakwalwa da zuciya sai ya rikita ayyukan su. Hakan sai ya haifar da abu mai k**ada rikicewar tunani ko farfadiya.

Wannan rashin lafiyan ta na samuwa ne a sanadiyyar chanzawar ruwar maniyyi ko a wassu lokuta makewar jinin haila sai su koma sifa irinta guba a jikin mutane, sai ta haifar da wata jinya mai k**ar FARFADIYA. wannan cutar tana da alamu k**ar haka;

1. Nauyin nunfashi
2. faduwar zuciya da bugun zuciya
3. ciwon kai
4. Rashin barci
5. Tasowar wani abu daga mara zuwa Saman jiki
6. Raunin kobri
7. Canzawar launi
8. Damshi mai yawa a cikin ido
9. Rikicewar tunani.

BANBANCIN WANNAN JINYA DA FARFADIYA

1. Mai wannan JINYA za ta iya faduwar amma hankalinta baya bacewa, ba k**ar mai farfadiya ba.
2. Mai wannan jinya ba ya zubar da yawu lokacin faduwar. Duk da ke akoi nauo'i na farfadiya da yawun baya zuba.

JINYAR WANNAN RASHIN LAFIYA

Mai bada magani zai lura da alamu kafin bada magani.
1. Za'a shafa mayin Yasmeen a bakin mahaifa.
2. Za'a samu Hilteet, Mur da Jundibadistaar ko wanne cikin cokali, sai a nike su a kasa garin gida goma sha biyu kullum a sha Kashi daya.

SHEIKH BARR. IBRAHIM TUKULMA

IMAM MASALLACIN ABU HURAIRA OPPOSITE HIGH COURT BY PASS GOMBE
(08060441137)

CUTAR HAUKA WACCE BA BU ALJANU KO SIHIRIAkoi wani nau'i na hauka wanda sanadinsa ba aljanu bane kuma ba sihiri bane. Amm...
25/08/2024

CUTAR HAUKA WACCE BA BU ALJANU KO SIHIRI

Akoi wani nau'i na hauka wanda sanadinsa ba aljanu bane kuma ba sihiri bane. Amma a wassu lokuta masu bada magani suna kuskuren yin ruqiya da tunanin cewa sihiri ne ko Shaidanu ne.

Wannan nau'in hauka malamai suna Qiran sa da suna 'MALIKULIYYA'
Na yi wannan rubutunne saboda da yadda mutane da yawa suke SHAN WAHALAR JINYAR tare da KASHE KUDI MASU YAWA
Wannan cutar tana da alamu k**ar haka:-

1. Son kadaita: Marar lafiyan yana son zama shi kadai.
2. Karancin magana: Maras lafiyan ba safai yake son yin magana ba.
3. Ganin abubuwa a wassu siffofi na daban: Maras lafiyan a wassu lokuta ya kan ga mutane da sauran abubuwa sun canza zuwa wassu siffofi daban. Misali:- Zai iya ganin Mutum ya zamo kwalba ko wuka ko wani abu daban.
4. Suranta munanan abubuwa a cikin ransa:- Maras lafiyan kullum yana da zargi kullum yana zargin cewa an hada baki don a cutar da shi ko ma a kashe shi.
5. Dukkan mutumin da ya samu sabani da shi to ya zamo abokin gaban sa kuma ko da mahaifiyar sa ce.
6. A wassu lokuta maras lafiyan baya karban abinci a hanun kowa saboda zargi don gani ya ke an hada baki za'a kashe shi

JINYAR WANNAN CUTA

Malamai s**a ce ana jinyatar wannan cutarne k**ar haka:-

1. Dole a samu mutum wanda shi maras lafiyan ya yarda dashi don ya dinga bashi magani cikin dabara. Saboda tsananin zargi da yake fama dashi. .
2. A samu ganyen Hanzal (Guna) da sanamakki da sibar (Aloe vera) Zuma da ma'ul wardi a hada su madaidaita. A dinga dabaran bawa maras lafiyan cokali Uku sau Uku a rana.
3. Amma ga wadanda suke sana'ar bada magani za su iya hada sanannen hadin magani da ake kira

MA'AJUN AN-NAJAH

Mun gwada da ikon Allah an samu lafiyan. A gwada wadannan insha Allahu za a samu nasara.

Allah ya bamu lafiya.

Ameen

Sheikh Barrister Ibrahim Tukulma

AL-ILAAJ HERBAL CLINIC GOMBE
08060441137

01/07/2024

KUHTBA JUMA'A

📍 Masjidu Abi-Hurairah Opposite High Court of Justice Gombe state, Nigeria

28 JUNE, 2024 22 ZHUL-HIJJA, 1445

Sheikh Barrister Ibrahim Tukulma

Mai Taken: IKHLASI

1. Kyawun niya ke sa aiki kadan ya samu sak**akon mai yawa a wurin Allahu.
2. Niya ke bambamta ayyuka masu k**a
3. Magabata suna lura da niyyoyin su fiye da abimcin da suke ci
4. Duk wanda ke son rayuwa mai kyau gobe Qiyama bai gyara niyyar sa ba, ya fiskanci abinda ba zaiyiwu ba.

28/05/2024

January 26, 2024. Rajab 14, 1445AH

NASIHA

Daga bakin: Sheikh Barrister Ibrahim Tukulma

DA MUTANE ZASU DOGARA DA ALLAH SU TAKAITA KAN CIN HALAL, DA ALLAH YA AZURTA SU K**AR YADDA YA KE AZURTA TSUNTSU YANA SAMMAKO BASHIDA KOMAI AMMA YA DAWO DA KOSHI. AMMA MAFIYAWAN MUTANE SUNA FITA DAGA GIDAJEN SU DA NIYAR CUTAN MUTANE A MA'AIKATA KO KASUWA KO WURIN SANA'A. KOWA YANA GANIN DABARAR SA CE ZA TA AZURTA SHI. ALLAH SAI YA BARMU DA HALIN MU. KULLUM RAYUWA WAHALA TAKEYI SABODA HALAYEN MU. MU NA CUTAR JUNAN MU, MUNA WAHALA DUKANMU.

Whatsapp: https://chat.whatsapp.com/CBFeOnvy2yfDodU45nRYhJ

13/03/2024

RAMADAN TAFSEER DAY 01

Tare da: Sheikh Barrister Ibrahim Tukulma

SEMINAR LACCA MUHIMMANCIN AIKIN AGAJI Tare da: Sheikh Barrister Ibrahim TukulmaWanda za'a gabatar k**ar haka:Date: 06/01...
05/01/2024

SEMINAR

LACCA

MUHIMMANCIN AIKIN AGAJI

Tare da: Sheikh Barrister Ibrahim Tukulma

Wanda za'a gabatar k**ar haka:

Date: 06/01/2024
Time: 4:00pm
Venue: Masallacin Jumma'a na Malam Inna bayan GSU

Today's lecture after Magrib Prayer In sha Allah at Bolari Central Masjid JIBWIS Gombe State.
28/12/2023

Today's lecture after Magrib Prayer In sha Allah at Bolari Central Masjid JIBWIS Gombe State.

SAKON KHUTBAR JUMA'A TA RANAR 22/12/2023 Jumada Al-Akhirah 09, 1445. MASJID ABI HURAIRA OPPOSITE HIGH COURT OF JUSTICE B...
26/12/2023

SAKON KHUTBAR JUMA'A TA

RANAR 22/12/2023 Jumada Al-Akhirah 09, 1445.

MASJID ABI HURAIRA OPPOSITE HIGH COURT OF JUSTICE BYPASS GOMBE

Tare da: Sheikh Barrister Ibrahim Tukulma

MAKWAPCI

1.Makawabci shine Wanda ka ke tare da shi a gida ko wurin Sana'a har ma a mota lokacin yin tafiya
2. Kyautatawa makwabci na daga cikar imani da cikar mutunci.
3. Makwabci a wassu lokuta ya fi da'uwa na jini amfani.
4. Wajibi ne mutum ya lura da duk abinda ya ke yi don kaucewa cutar da makwabcinsa.
5. Annabi (SAW) ya yi tsammanin Allah zai yi umurnin gado tsakanin makwabta.

SAKON KHUTBAR JUMA'A TA RANAR 15/12/2023 Jumada Al-Akhirah 02, 1445. MASJID ABI HURAIRA OPPOSITE HIGH COURT OF JUSTICE B...
15/12/2023

SAKON KHUTBAR JUMA'A TA

RANAR 15/12/2023 Jumada Al-Akhirah 02, 1445.

MASJID ABI HURAIRA OPPOSITE HIGH COURT OF JUSTICE BYPASS GOMBE

Tare da: Sheikh Barrister Ibrahim Tukulma

ALLAH YA TSINEWA WASSU K**AR HAKA:

1. Wanda ke sa a zagi iyayensa
2. Wanda ya yanka dabba ba don Allah ba.
3. Wanda ya taimaki mai sabon Allah
4. Wanda ya ke mallake filin da ba nasaba (ko taku daya ne)
5. Wanda ke cin riba
6. Na miji mai k**anceceniya da mace ko mace mai k**anceceniya da maza

SAKON KHUTBAR JUMA'A TARANAR 08/12/2023 Jumada Al-ula 24, 1445. MASJID ABI HURAIRA OPPOSITE HIGH COURT OF JUSTICE BYPASS...
10/12/2023

SAKON KHUTBAR JUMA'A TA

RANAR 08/12/2023 Jumada Al-ula 24, 1445.

MASJID ABI HURAIRA OPPOSITE HIGH COURT OF JUSTICE BYPASS GOMBE

Tare da: Sheikh Barrister Ibrahim Tukulma

ALAMOMIN TASHIN QIYAMAH

1. Rashin nitsuwa da kankan da kai (khushu'i) a cikin sallah
2. Shuwagabani masu daukar mummunan abu tamkar mai kyau
3. Amintuwa da maha'inta da kuma ha'intar mutane masu amana
4. Mutane za su yi burin mutuwa saboda rikicewar rayuwa
5. Shekaru za su zanto suna gudu kuma albarkarsu ta zanto kadan
6. Alfahsha za ta yawaita.

06/12/2023

Darasin mu na yau In sha Allah

Address

Behind Science Village Bypass Gombe
Gombe

Telephone

+2348060441137

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al—Ilaaj Herbal Clinic posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Al—Ilaaj Herbal Clinic:

Videos

Share