28/08/2025
menene ciwo sciatica? Ga bayani game irin wannan ciwon👇
Sciatica (ko sciatic nerve pain) wata irin matsalar ciwo ce da ke farawa daga ƙasan baya (lower back) zuwa ƙugu, mazaunin baya (buttocks), sannan ta bi hanya a kafa ɗaya (wani lokaci biyu, amma yawanci ɗaya). Ana samun wannan ciwo ne idan aka matsa wa sciatic nerve, wanda shi ne babbar jijiyar da ke tafiya daga ƙasan kashin baya har zuwa yatsun kafa.
Abubuwan da ke jawo Sciatica
Herniation ko prolapse na disc (faifan kashin baya ya zame ya matsa wa jijiyar)
Bone spur (tsiro a kashin baya)
Stenosis (kunkuntar hanya ta jijiyoyin kashin baya)
Rauni ko matsawa daga tsoka
Ciwo ko kumburi a yankin ƙugu ko kashin baya
Alamomin Sciatica
Ciwo mai kaifin gaske ko ƙaiƙayi daga ƙasan baya zuwa kafa.
Jin tingling (ƙaiƙayi kamar ana tsokanar jijiya).
Rauni ko sanyi a kafa É—aya.
Matsalar tafiya ko tsayuwa na dogon lokaci.
Matsayin Ciwo
Zai iya zama mai laushi ko mai tsanani. Wasu s**an ji shi kawai idan sun zauna ko s**a yi tsaye na dogon lokaci.
Magani
Hutu amma ba kwanciya dogon lokaci ba.
Magungunan rage zafi da kumburi (NSAIDs).
Fisiotherapy (stretching, exercises).
In ciwon ya tsananta ko ya daɗe ba tare da sauƙi ba, ana iya yin tiyata.