09/02/2025
SU WAYE CUTAR HIV BATA YIMA ILLA?
Dazu nayi Wani rubutu inda nake bayanin cewar akwae mutanen da cutar HIV bata yimusu illa duk da kasancewar tana cikin jininsu, inda wadansu suke tambayar Karin bayani akan hakan. Ga bayanin k**ar haka👇
Acikin jikin mutum akwae wadansu sojoji wadanda aikinsu shine bayar da kariya ga mutum yayin da Wani abin zargi ko Kuma Mai cutarwa ya shiga cikin jiki, wadannan sojoji Kuma acikinsu akwae wadanda Ake cema CD4 cells Wanda sune ainahin wadanda kwayar cutar HIV take yima illa da zarar ta shiga jikin mutum, Wanda yake sanya mutum ya zama ya galabaita sanadiyyar kasheshu.
A jikin kowanne kwayar sojan CD4 cells akwae abinda Ake cema CCR5 Wanda shi k**ar wata alamace ko Kuma tuta wacce kwayar HIV take nema da zarar ta shiga jikin mutum. Saboda haka idan har ajikin CD4 Babu wannan alamar ta CCR5 toh babu yadda zaayi ta iya k**a jikinsa har ta kashe su, sai dai take yawo acikin jiki tana garari batare da yin wata illaba.
Akwae mutanen da suke da nakasar da Ake kira CCR5-delta 32, wanda sune wadanda basuda CCR5 kenan acikin jikinsu. Toh idan kwayar cutar HIV ta shiga jiki, zatake yawone kawae ba tareda ta gane CD4 din ba saboda rashin CCR5 din. Wanda cutar zatake yawone kawae a haka ba tareda tayi illa ga mutum ba.
Shiyasa Daya daga cikin hanyoyin da yanzu Ake amfani dashi wajen kokarin kare mutum daga cutar HIV shine, kokarin bunkasa nakasar CCR5 acikin jikin mutane, ta yadda cutar ba zatayi tasiri ba kenan.
Sannan mutanen da suke da wannan matsalar wato CCR5- delta 32 mutation, suna dauke da cutar ba tare da tayimusu illaba, amman zasu iya gogawa mutane dayawa Kuma tayimusu illa.
Karin bayani:
Hoto na farko, shine mutane wadanda cutar HIV take yimusu illa, kasancewar sunada CCR5, Wanda shine wata jar alama ajiki.
Hoto na biyu Kuma shine wadanda cutar bata yimusu illa saboda rashin CCR5 ajikin kwayar CD4 dinsu, maana basu da wannan jar alamar ajikinsu.