13/10/2025
YAYE SABBIN ‘YAN AGAJI (FIRST AID GROUP, JIBWIS JALINGO) NA KARAMAR HUKUMAR JALINGO
An gudanar da babban bikin yaye sabbin ‘yan agaji (First Aid Group) na ƙungiyar JIBWIS Jalingo Local Government a yau, wanda ya gudana cikin natsuwa da farin ciki a Harabar Babban Masallacin Juma'a na Masjid Uthman Bin Fodiyo Jalingo (Masallacin Juma'a na Dr. JALO), tare da halartar manyan baki daga ɓangarori daban-daban na addini da tsaro.
A yayin taron, Kwamandan First Aid Group na Jihar Taraba, Ustaz Muhammad Muhammad Usman, ya bayyana cewa sabbin jami’an da aka yaye sun samu horo na tsawon makonni a fannoni da dama, ciki har da horo kan taimakon gaggawa (first aid), tsare tsaro, da hidimar al’umma, bisa jagorancin ƙwararrun malamai da jami’an tsaro.
Ya ƙara da cewa:
“Wannan horo ya biyo bayan ƙudurin JIBWIS na tabbatar da cewa matasanmu suna da ilimi da ƙwarewa wajen bayar da taimako a lokutan gaggawa da kuma kare mutunci da tsaron jama’a a wuraren ibada da al’umma baki ɗaya.”
Shi ma Shugaban Majalisar AGAJI na JIBWIS Jalingo LGA, Malam Bashir Isa, ya yi kira ga sabbin yan Agajin da su kasance masu tawali’u, biyayya, da aiki don Allah kawai, yana mai jaddada cewa:
“First Aid Group ginshiƙi ne na tsari da tsaro a cikin JIBWIS.
Aikin ku na hidima ne, ba na neman suna ba. Ku kasance wakilan ƙungiyar a zahiri da aiki.”
An kuma samu jawaban ƙarfafa gwiwa daga daya daga cikin wakilan iayayen inda s**a yaba wa JIBWIS saboda yadda take tarbiyya da horar da matasa cikin ladabi da kwarewa.
A karshe, an rufe bikin da addu’ar neman nasara ga sabbin jami’an agaji, tare da raba takardun shaida (certificate) ga waɗanda s**a kammala horon cikin nasara.
Bikin ya kasance ɗaya daga cikin manyan al’amura da suke nuna jajircewar JIBWIS Jalingo wajen ci gaba da gina matasa masu tarbiyya, hidima, da kishin al’umma.
Usama Muhammad Bello
Deputy Secretary FAG Of
JIBWIS JALINGO Division