19/06/2025
[6/19, 7:42 AM] LAKURAWA;
Mayakan kungiyar nan ta Lakurawa sun gargadi al'ummomin garuruwa fiye da goma na yankin karamar hukumar Augie ta jihar Kebbi, a kan su yi watsi da dabarar sayar da shanun huda suna sayen wasu na'urorin zamani na huda da ke amfani da man fetur.
Mayakan sun ce za su halaka duk wanda ya ki jin gargadin nasu.
Manoman dai kan sayar da shanun su sayi na'urorin huda saboda tsoron da suke yi, cewa 'yan bindigar suna sace musu dabbobi.
Kashedin da ake zargin 'yan kungiyar ta Lakurawa sun yi wa jama'ar garuruwan, ya jefa fargaba da zaman dar-dar ga mutanen yankin.
[6/19, 7:48 AM]
ISRRAL;
Ayayin da yaki ke cigaba da zafafa kasar israel tace : Daga cikin mak**an da za a iya harbawa su keta ƙarƙashin ƙasa har su iso wurin da rumbunan ajiyar sinadaran nukiliyar Iran suke, daya ne kawai ba a yi amfani da shi ba zuwa yanzu, kuma Isra'ila ba ta da shi a yanzu.
Makamin shi ne GBU-57A/B - wanda ya kasance bom marar nukiliya mafi ƙarfi a duniya - da zai iya lalata rumbunan ajiyar sinadaran ƙera makamin nukiliya, kuma Amurka ce kadai ta mallake shi a duniya.
Wannan tsararren makami mai nauyin kilogiram 13,600 zai iya ketawa ƙarƙashin ƙasa domin wargaza rumbunan sinadaran ƙera nukiliyar Iran da ke binne can ƙarƙashin duwatsu.
Zuwa yanzu Amurka ba ta bai wa Isra'ila mak**ain ba.