
29/06/2020
Kungiyar Nisau Sunnah Na Neman Taimako Saboda Gina Makarantar Islamiya
A shekarar da ta gabata Kungiyar Nisau Sunnah a jihar Adamawa ta sanar da samun filaye har guda bakwai a wurare mabanbanta a jihar Adamawa inda kungiyar ta sanar zata gina makarantun Islamiya don karfafa ilimi a kauyukan da filayen suke.
Zuwa yanzu, kungiyar ta samu nasar fara gini a daya daga cikin filayen kamar yanda kuke gani a hoto, a unguwar Badirisa dake karamar hukumar Girei a jihar Adamawa.
Ameera H. Dan Umma ta bayyana cewa kungiyar su na neman tallafi daga hannun al'umma na kudi ko kayan aiki don samun karasa wannan gagarumin aiki, wanda duk wanda ya taimaka zai zama sadakatul jariya.
Ana iya aikawa da taimako ta asusun kungiyar ko kuma a tuntubi daya daga cikin wadannan malaman
1. Malam Malami Garba
08060509073
2. Malam Mamman Nasir
+234 803 812 6777
3. Ameera Habiba Dan Umma
0803 770 1504
Banki: Zenith Bank
Sunan Asusu: Jibwis Woemen Da’awa Committee
Lambar Asusu: 1013563272
Allah ya albarkaci abunda zaku bayar.