08/01/2026
MACE TAGARI!
Gidan miji masarauta ce ga mace, shi yasa mace tagari ke sarrafa dukkan abin da ta mallaka na ilmi, hankali, wayewa da ƙwarewar rayuwa, domin ganin ta mayar da masarautarta aljannar duniya, wajen kwanciyar hankali, more rayuwa da cikakkiyar nutsuwa ga uban ‘ya’yanta.
1. Mace tagari ita ce, wacce ta yi fice da ƙwarewa tare da yauƙaƙa soyayyarta wajen inganta bangorori 13 kamar haka: iya kwalliya, girki, tarba, murmushi, magana, kallo, rakiya, kwanciya, hira, tafiya, raha, rarrashi da kwantar da hankali.
2. Mace tagari a matakin farko tana kusantar mijinta ne, domin ta fahimci dabi’u, halaye da bukatunsa domin ta san yadda za ta zauna da abinta.
3. Mace tagari babban burinta, cika siffofin da Manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallam ya siffanta mace tagari da su. “Khairu nisaa’ikum allatiy izaa nazara ilaiha zaujaha sarrathu, wa in amaraha adaa’athu, wa izaa ghaaba anha hafizathu fi nafsiha wa maalihi’’4
4. Mace tagari tana zaman aure ne, domin samun yardar Allah Jalla wa Alaa, lazimtar addu’o’i da kyautata ladubban tarbiyya ta addinin musulunci a gidanta da ‘ya’yanta, tana kiyaye ibadu da kamanta tsoron Allah Jalla wa Alaa a dukkan al’amuranta.
5. Mace tagari tana fifita ilimi fiye da komai na rayuwarta, tana maida hankali a kan kyakkyawar rayuwar ilimi a cikin gidanta da yaranta domin samun albarka da hasken rayuwa.
Doctor Mata