30/11/2023
ABUBUWAN DA SUKE SANYA HAIHUWAR JARIRI TAYI WUYA A LOKACIN DA MACE TAKEYIN NAKUDA (CAUSE OF OBSTRUCTED LABOUR AT CHILDBIRTH)
Idan mace tana nakuda, kuma bakin mahaifarta ya gama budewa (10cm cervical dilation), sa'annan kwanciyar jariri a cikin mahaifa tayi daidai yadda ake bukata (normal cephalic fetal presentation), kuma tanayin yunkuri sosai (effective pushing), amma jariri yaki fitowa daga mahaifa zuwa cikin ramin farjinta, wannan shine ake kira "arrest of descent" ko "failure to descend" ko "obstructed labour" a likitance.
Abubuwan da zasu iya haddasa hakan sune:
1. Rashin daidaiton girman kan jariri da kugun uwa (cephalopelvic disproportion): matsakaicin girman kan jariri a lokacin haihuwa wanda ba'a tsammanin samun wannan matsalar shine daga 32cm zuwa 38cm, watau 12.6 inches zuwa 15 inches. Idan akayi rashin sa'a kan jariri yafi hakan girma, sa'annan kugun uwa bashida fadi sosai, to, za'a sami rashin daidaitonsu. Daga nan sai fitowar jariri tayi wahala. Mai yiwuwa ne sai an kara mace (episiotomy) sa'annan ta iya haihuwa.
2. Rashin juyawar fuskar jariri ta kalli gadon bayan uwa (fetal face malposition): abinda ake bukata idan jariri zai fito daga farji shine fuskarsa ta kalli gadon bayan uwa (occiput anterior). Amma idan akayi rashin sa'a fuskarsa ta kalli saman cikinta (occiput posterior), ma'ana keyarsa tana kallon kashin bayan uwa, to, zaiyi wahalar fitowa. Za'a iya gyara wannan yanayin ne ta hanyar sanya mai nakuda ta danyi tafiya, ko ta zauna a cikin ruwan dumi, ko ta gurfana akan hannunta da gwuiwarta, ko jami'an amsar haihuwar su rika mammatsa bayanta.
3. Rashin takurewar mahaifa yadda ya kamata (inadequate uterine contractions): akwai bukatar haduwar yunkurin da uwa takeyi da kuma takurewar mahaifa yadda ya kamata a lokaci guda, domin samun saukin haihuwa. Idan daya kawai aka samu, amma ba'a sami dayan ba, to, fitar jariri daga farji zatayi wahala. Idan aka sami wannan yanayin, to, hanyoyin da za'a iya yin amfani dasu domin zaburar da takurewar mahaifar (uterine contractions) sune sanyawa mace ruwan nakuda (oxytocin infusion), ko sanya mace ta danyi tafiya (walking), ko bata isasshen ruwa ta rika sha (adequate hydration), ko sanyawa mace na'urar da zata fitar da fitsari daga cikin mararta (catheterization), ko mulmula mata kan nononta (ni***es stimulation).
Matakin karshe wanda za'a iya dauka idan dukkan hanyoyin magance matsalolin da na fada basuyi amfani ba, shine ayiwa mace tiyatar CS ta gaugawa.
Allah SwT ya sauki matanmu masu juna biyu lafiya, amin.
WalLahu A'lam.