08/07/2025
KARIN MAHAIFAH (FIBRIOD)
Dr Umar herbal ๐ฟ and holistic medicine ๐ฟ
MINENE FIBROID?
Kafin bayanin alamomin, mu fara da minene "fibroid"? Fibroid wata matsalace a mahaifar mace, wato wani yanayi ne da wani curin nama yake fitowa kuma yana girma a mahaifar mace. ฦkululun naman mai cutar da lafiya yana ษanfare da wani sashen mahaifar (uterus) da wasu igiyoyinsa matakam. " Fibroid" kalmar turanci ce, domin sauฦin furuci da Hausa, zamu cigaba da amfani da lafazin FAIBIROD a cikin bayanin mu anan . Anyi ฦiyasi cewa cikin mata 100, kashi 20 zuwa 50 na matan suna da fibroid, musamman a shekarunsu na samun haihuwa - wato daga shekara 16 zuwa 50. Wani ฦkiyasin kuma ya nuna cewa mata 30 zuwa 77 suna samun matsalar fibroid a lokacin shekarunsu na samun haihuwa, wato lokacin ฦkuruciyar balaga zuwa lokacin tsayawar al'adar mace saboda manyanta ko tsufanta (menopause). Mafi yawan nau'in faibirod da ake samu bayada alaka da ciwon-daji / kansa (not cancer). ฦkululun ko ฦkwallon irin wanda baya da nasaba da ciwon-daji ne (benign/non-cancerous). Yana iya fitiwo fiye da ษaya a mahaifa, k**ar guda uku, huษu koma fiye da haka a wurare daban-daban cikin mahifa.
ALAMOMIN MATSALAR FAIBIROD
DR UMAR HERBAL ๐ฟ AND HOLISTIC MEDICINE
Wasu daga cikin alamomin sun haษa da:
1. Zubar jinin al'adah mai yawa, ko na tsawon lokaci
2. Zubar jini baaฦin lokutta ko tsakanin lokuttan haila
3. Ciwon ฦkugu, saboda ฦkululun yana danne wani sashen jiki cikin mahaifa
4. Yawan fitsari
5. Ciwon baya daga ฦkasan baya
6. Jin zafi /ciwo lokacin yin jima'i
7. Rashin jini a jika saboda yawan zubar jini
8. Rashin jin dadi a mara, musamman saboda girman ฦkululun a ciki
9. Basur maisa tsugunni a bayi saboda rashin fitar bahaya
10. Ciwon kafa
11. Girman ciki k**ar mace tana da juna biyu amma ba juna biyu bane, musamman idan faibirod din ya girma
12. Koma rashin ganin wasu ko daya daga cikin alamamomin da muka yi bayani
WASU DAGA CIKIN MATSALOLIN DA FAIBIROD ZAI IYA HADDASAWA:
- Matsala wajen haihuwa/lokacin nakuda
- Matsala yayin fama da juna biyu
- Matsalar rashin samun juna biyu / rashin ษaukar ciki ga mace saboda ฦkululun ya toshe/taushe ko danne wani bangaren mahaifa
- Yawan bari/zubewar ciki
Yana da matukar muhimmanci mai jin daya ko fiye daga cikin wadannan matsalolin yaje asibiti domin binciki ko tana da matsalar faibirod ko akasin haka. Idan kuma kin riga kin sani to sai a nemi magani.
MINENE KE KAWO MATSALAR FAIBIROD?
DR UMAR HERBAL AND HOLISTIC MEDICINE
Har yanzu dai masana ilimi a fannin lafiya na ฦoฦarin fahimtar cikakken dalilin daya sa ake samun fibroid. Saidai an gano cewa yawan sinadarin ESTROGEN (estarojin) a lokacin shekarun da mace ke iya samun haihuwa yana da nasaba da lokacin da mata ke samun matsalar faibirod. Daga shekara 16 zuwa 50 shine lokacin da sinadarin yafi yawa a cikin jinin mace. ESTROGEN daya ne daga cikin manyan sinadaran jikin mace, wato ESTROGEN sinadari ne na jinsin mace dake tafiyar da girman jikin mace, rayuwar mahaifarta da yanayin halittarta daya shafi jima'i . A lokacin balaga sinadarin na taimakawa yasa nonuwa da gashin mara da hammata su fito, kuma shine ke saka sha'awa ko yawan sha'awa ga mace idan yayi yawa. A lokacin balaga ฦkwayayan mahaifa (ovaries) zasu fara samar da sinadarin. Za'a iya kiran ESTROGEN da suna MAฦkERIN ฦณAN MATA , domin kuwa shine ke taimakawa wajen sauye-sauyen halittar jikin mace yayinda take girma. A takaice, ESTROGEN shine sinadarin da faibirod s**a dogara dashi domin samun daษa girma a mahaifa, wato mak**asin faibirod. Faibirod zai cigaba da girma har sai lokacinda mace ta bar yin al'ada saboda girma (menopause), daga nan sai ya fara ฦkanฦkancewa.
WASU DALILAI DA KA IYA SA YIWUWAR MACE TA SAMU FAIBIROD:
DR UMAR HERBAL AND HOLISTIC MEDICINE
- Gado : Idan mahaifiyarki ko ฦดyar uwarki ta taba samun fibroid zai iya yiwuwa ki samu saboda gadon jini.
- Jinsin bakar fata: Mutanen Africa ko ฦkasashen bakar fata, wato jinsin bakar fata su s**a fi kowanne jinsin mata a duniya samun matsalar faibirod. Kuma matasa mata bakar fata sune s**a fi samun matsalar a shekarunsu na matasa. A ฦkasashen turawa, Indiya da Chaina da sauran wasu ฦkasashen, ba kaso ake samun matansu da matsalar ba.
- Amfani da hanyoyin tsaida haihuwa (ฦkwayoyin tsaida haihuwa wani lokacin zasu iya sa faibirod ya girma), kiba ฦkarancin sindarin vitamin D, yawan cin jan-nama, rashin cin abincin ganye da yayan itatuwa, shangiya da sauransu.
Hanyoyin asibiti na magance matsalar asibiti ya ฦkunshi: aikin tiyata (surgery) domin cire ฦkululun tare da cire wani bangaren mahaifa "uterus" [Hysterectomy] wanda zai hana samun haihuwa, sa'annan wani nau'in aiki tiyatar [Myomectomy]wanda baya hana haihuwa a gaba, ฦwayoyin magani da wasu hanyoyin. Musamman idan ya girma aikin tiyata ne akafi yi domin rabuwa da matsalar.Girman faibirod na iya zama kwatankwacin girman dutse karami ko ฦkasa da haka , ko girman lemun tsami ko na zaki, ko girman ฦkwallo, girman jariri koma fiye da girman jariri, musamman idan ba'a cire shiba ko magance saba. Wasu likitocin naganin idan faibirod yakai girman inci 4 (4 inches/9-10 cm) to akwai bukatar ayi aikin tiyata domin a cire shi. Idan Kuma bai kai hakan ba insha Allahu akwai maganin da zai narkar da shi.
MUSUNEMAN KARIN BAYANI SAI KU TUNTUBEMU A WHATSAPP KO KIRA INSHA ALLAH DON ALLAH KARKUMANTA DA SHARING DA LIKE DOMIN WOSU SU ANFANA NAGUDE DAGA NAKU DR UMAR HERBAL AND HOLISTIC MEDICINE