30/03/2026
ALLAH SARKI, SARKI....
Daga Sheikh Kabir Asgar
Al-Imam Ibnu Hibban ya ruwaito a cikin (المجروحين) da Khateebul Baghdady a cikin (الفقيه والمتفقه) cewa wai Annabi (SAW) wai ya ce: "Ku tausaya wa mutane uku; mai daraja da ya ƙasƙanta da mawadacin da kuɗinsa s**a ƙare da kuma malami a tsakankanin jahilai".
Wannan hadisi yana da rauni ƙwarai da gaske. Amma dai, in muka ɗauke shi a matsayin zance na hikima ko azanci, za mu ga cewa da gaske ne, waɗannan mutane uku abin tausayi ne.
In ba haka ba, ta yaya za ka fassara abin da mutane ke ta yamaɗiɗi da shi akan ƙoƙarin Sheikh Pantami wajen sulhunta tsakanin abokai biyu waɗanda rikicin siyasa ya yi ƙamari a tsakaninsu. Shi dai Malam Pantami ya yi aiki ne da nassoshin dake umarni da a yi sulhu, sulhu alheri ne, a daina gaba, da sauransu.
Ku kuma kuna ta cewa don me zai yi hakan a maƙabarta? Ai ba haka ake yi ba. Gaskiya an cuci wane. Ba a yi ma wane adalci ba. Tsakaninku da Allah kuna da nassoshin da s**a sahhale muku waɗannan zantuttukan? Ko kuwa molanka ce kawai daga aljuhunku?
Ku ɗin dai ne fa masu zuga malamai cewa su shiga siyasa saboda su kawo gyara, sun shiga za su fara kawo gyaran kenan kun hayayyaƙo musu da cewa ba su iya ba, ba haka ake yi ba. Yenyenyen. Ba a iya muku kamar dangin miji.
Wannan ya tuna min da wata almara cewa, wai wani yaro ne ya ga ɗauko gawar sarkin garinsu shine ne ya ce: "Allah sarki, sarki".