29/04/2026
NAU’IKAN CIWON SUGA
(Types of Diabetes أنواع أمراض السكري)
Ciwon suga cuta ce da ke shafar yadda jiki ke sarrafa sikari (glucose) a cikin jini. Yana faruwa idan jiki ba ya iya samar da insulin ko amfani da shi yadda ya kamata.
Masana sun tabbatar cewa ciwon suga yana da nau’o’i daban-daban, amma manyan da aka fi sani su ne:
1. Ciwon Suga na Fitsari (Diabetes Insipidus)
Wannan nau’i ba shi da alaƙa da sikari kai tsaye.
Yana faruwa ne saboda matsalar sinadarin ADH a jiki
Yana sa:
Yawan fitsari sosai
Yawan jin ƙishirwa
Rashin riƙe ruwa a jiki
2. Ciwon Suga na Sikari (Diabetes Mellitus)
Wannan shi ne mafi shahara.
Yana faruwa ne saboda matsalar insulin
Insulin yana fitowa daga Pancreas (saifa mai sarrafa insulin)
Rassan sa sun haɗa da:
Type 1 Diabetes
Jiki baya samar da insulin
Yawanci yana farawa tun ƙuruciya
Ana amfani da insulin allura
Type 2 Diabetes
Jiki yana samar da insulin amma baya aiki yadda ya kamata
Yana da alaƙa da kiba da rashin motsa jiki
Shi ne mafi yawan mutane ke fama da shi
Gestational Diabetes
Yana faruwa ga mata masu ciki
Yana iya ɓacewa bayan haihuwa
Ciwon suga cuta ce mai haɗari idan ba a kula da ita ba. Amma da kulawa, abinci mai kyau da motsa jiki, ana iya sarrafa ta
Ayi kokarin share na wannan bayanin domin wayar da kan mutane
Allah ya kare mu daga cututtukan Zamani