
01/05/2024
Idan Kaga Mutum Yana Duba Laifin Wani Ko Yana Fadin Laifin Wani Ko Yanayiwa Wani Hassada Akan Mulki Ko Ilmi Ko Dukiya Ko Daukakan Da ALLAH Yayiwa Mutumin, To Wannan Mutum Har Yanzu Yana Nan a Muqamin ISLAM Ne,
Amma Indai Mutum Ya Kai Matsayin Muqamin IMAAN (Mumini) To Wannan Ba Damuwarsa Ba Ne Shi Dai Damuwarsa a Lokacin Ya Kula Da Ibadunsa Kawai,
Idan Kuma Mutum Ya Kai Matsayin Muqamin IHSAN To Wannan Ya Zo Qarshe Kenan Shi Duk Tunaninsa Da Komai Na Shi Akan Lamarin ALLAH Da ANNABI (S.A.W) Kawai Yake,
Indai Mutum Ya Zo Matsayin Muqamin IHSAN To Komai Kayi Masa Zai Dauka Daga ALLAH Ne, Haka Kuma Komai Ya Faru Dashi Ko Ya Same Shi Ko Ya Samu Ko Ya Rasa To Duk Zai Dauka Daga ALLAH Ne Kawai, To Wadannan Su Ne Bayin ALLAH Wadanda Ake Kiransu Waliyai"
To Fa Jama'a Lalle Akwai Jan Aiki a Gabanmu Wallahi Jama'a Mu Gyara Halayenmu,
ALLAH KASA MU KAI WANNAN MUQAMIN ALBARKAR ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMAA