
18/06/2022
SHAIKUL ISLAM IBNU TAIMIYYA YAYI BABBAN KUSKURE DA TA TUHUMI SAYYIDUNA ABDULLAHI DAN UMAR (RA) DA NUNA CEWA DAN BIDI'A NE (CIGABA)
To amma kuma duk da haka, ]aya daga cikin wa]ansu magabatan malamai, wanda duniya ta yi masa shaida a kan }o}arin bincike ta fuskar ilimi, a fannona da dama, babban malami Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya, wanda ya rubuta tarin littattafan da shafukan littattafan su ka haura dubu arba’in (40,000) a fannona da dama, to, shi kam a irin na shi hange da kuma irin fahimtarsa, Abdullahi [an Umar, bai wuce ]an bidi’a ba. Sannan kuma a bayyane ne yayi k**a da aikin Annabi to, sai dai a manufarsa, ya fi k**a da Yahudawa ne. Wannan maganar, tana da matu}ar ha]ari ga daliban ilimi irin mu. Saboda haka, idan da so samu ne, da k**ata yayi manyan malamai su ri}a barin irin wa]annan matsalolin can a tsakaninsu, ta yadda ba ma za su iya isowa zuwa gare mu ba, b***e har su iya saka mu a cikin ru]ani da kuma fitina, wanda ni ke ganin cewa, k**ar yin hakan bai dace ba.
Idan shehin malami Ibnu Taimiyya ya mayar da martani a kan wani malmamin da s**a yi zamani tare da shi, ya kuma jingina wata maganar s**a zuwa gare shi a kan kowace irin mas’ala ce, to muna iya fahimtar wani abu a nan, ba tare da lura da wanda ke bisa daidai ko kuma wanda ya dare a kan hanyar kuskure a tsakaninsu ba. A’a, abin lura a nan kawai shi ne, malamai ne kuma tsarakun juna, wanda faruwar hakan a tsakaninsu, ba wani abin mamaki ba ne.
Za mu cigaba In Sha Allah.
📝 SHEIKH MUNTAKA MUHAMMAD USMAN BILBIS