02/09/2025
Wasu Daga Cikin Alamomin Shafar Junnu / Sihiri
Daga Littafin Assarimul-Battar
1. Rashin son karatun Alkur’ani ko saurarensa.
2. Rashin sha’awar yin ibada (kamar sallah) ko yin ta cikin bacin rai da kasala.
3. Yawan ciwon kai, jiri ko ɗaukar zafi a kai.
4. Ciwon mara, baya, ƙwankwaso ko ciki wanda ba a gano musabbabinsa ba.
5. Jin kamar wani abu na tafiya a jiki (kiyashi, tsutsa, ƙwarkwata) amma ba a gani.
6. Mafarki masu ban tsoro, firgici ko jin an shake wuya a bacci.
7. Yawan tsoro ko faduwar gaba, jin ana kiran sunanka ba tare da wanda ya kira ba.
8. Jin sanyi, zafi ko rikewar sassan jiki ba tare da dalili ba.
9. Rashin bacci da daddare ko jin motsi/surutai.
10. Rashin son aski ko kitso, ko rashin juriya idan aka taɓa kai.
11. Yawan bacin rai da haushin mutane ba tare da dalili ba.
12. Rashin son shiga cikin jama’a, zargi ko rigima da mutane.
13. Kuka, dariya ko murmushi ba tare da dalili ba.
14. Jin kamar ana rada a kunne ko raya zuciya da mugayen tunani (kisan kai, zina, sata).
15. Rashin sha’awar aure ko korar samari / budurwa.
16. Daukewar sha’awa ko rashin jin daɗin saduwa da aure.
17. Yawan kallon madubi ko sha’awar kallon tsiraici.
18. Yawan son kiɗa da rawa.
19. Son dare, zama a duhu ko shuru.
20. Rikicewar jinin al’ada ko na nifasi ga mata.
21. Rashin haihuwa, yawan zubar ciki, haihuwar jariri mara rai ko matsalolin haihuwa.
22. Aikata abu ba tare da hankali ba, sai daga baya a yi nadama.
23. Faduwa kasa cikin rashin hayyaci, ihu ko gudu ba tare da sanin inda ake zuwa ba.
24. Yawan wasuwasi da mantuwa musamman a ibada.
25. Tabuwar kwakwalwa ko kasa fahimtar abubuwa.
26. Rashin tsafta da son zama cikin kazanta.
27. Yawan fita waje ba tare da dalili ba, kamar zama karkashin bishiya, bakin bola, bandaki, jeji, bakin ruwa da sauransu.
28. Rashin lafiya da ba a gane asalin cutar ba.
29. Rashin son wa’azi ko zama da mutanen kirki.
30. Jin tsoro ko rashin jurewa ruqya (karatun waraka).
Allahu Ta’ala A’alam.
---
📍 Daru-Shifa Prophetic and Herbal Medicine Store
Kawo – Kaduna
📞 WhatsApp: 08037624598