
22/07/2025
Aikin Likitan Fisiyo Bayan Yanke Sashin Jiki
Yanke sashin jiki, musamman hannu ko ƙafa ƙalubale ne da ke sauya rayuwa kacokan. Domin abu ne da ke da tasiri ga ingancin rayuwa da tattalin arziƙi. Yanke sashin jiki na zama wajibi idan sashin jiki ya samu mummunan lahanin da, a likitance, ba za a iya ceto shi ba, ko ya lalace, ko ya riga ya ruɓe, ko kuma domin daƙile bazuwar ƙwayoyin cuta ko ciwon daji zuwa sauran sassan jiki.
Yanke sashin jiki na afkuwa daga sabuba da yawa, musamman daga haɗura, iftila'o'i da cutuka.
Daga cikin sabuban yanke sashin jiki akwai:
1. Haɗuran ababen hawa
2. Haɗuran injinan masana'antu kamar yanka daga injin yanka, injin niƙa/markaɗe da sauransu.
3. Raunukan yaƙe-yaƙe ko ta'addanci kamar fashewar bom, harbi, yanka ko sara.
4. Iftila'o'i kamar gobara, ruftawa/faɗowar gini da dai sauransu.
5. Cutukan jijiyoyin jini
6. Ciwon siga
7. Ciwon daji/kansa
8. Matsalolin ɗorin gida/gargajiya, da dai sauransu.
Sassan jiki da aka fi yankewa su ne hannu da ƙafa. Kuma yankan na iya kasancewa a kowane sashi na hannu ko ƙafar.
Likitan fisiyo na aiki tare da sauran likitoci kafin, yayin da kuma bayan yanke sashin jiki.
Musamman bayan yanke sashin jiki kamar hannu ko ƙafa, aikin likitan fisiyo ne rage ciwo, rage kumburi da ƙarfafa tsokokin dungulmi. Daga ƙarshe, muradin likitan fisiyo shi ne tabbatar da ingancin lafiyar dungulmi domin ya dace da sanya hannu ko ƙafar roba.
© Physiotherapy Hausa